Bikin Kalankuwar Legas ya kare da rikici
Ga dukkan alamu bikin kalankuwar da Gwamnatin Jihar Legas ta shirya ya koma fada, inda wasu matasa da ba sa ga miciji da juna suka far wa juna, inda mutum takwas suka jikkata wasu kuwa suka samu munanan raunuka a lokacin da suke yi jerin gwano a kan hanyar Awolowo da ke yankin Ikoyi a […]
Ga dukkan alamu bikin kalankuwar da Gwamnatin Jihar Legas ta shirya ya koma fada, inda wasu matasa da ba sa ga miciji da juna suka far wa juna, inda mutum takwas suka jikkata wasu kuwa suka samu munanan raunuka a lokacin da suke yi jerin gwano a kan hanyar Awolowo da ke yankin Ikoyi a Jihar Legas.
’Yan tawagar da suke kiran kansu da Oko-Faaji su ne suka yi zargin wasu matasa da ke yankin Ikoyi sun afka musu inda suka yi wa membobinsu rauni.
Wani ganau ya bayyana cewa fadan ya dauki lokaci ana yin sa ba tare da jami’an tsaro sun kawo dauki ba.
Ganau din wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda wasu dalilai ya bayyana cewa: “Da idona na ga an kai wa ’yan tawagar Oko-Faaji hari da misalin karfe biyar na yamma a kan titin Awolowo a daidai unguwar Ikoyi kusa da barikin gandurebobi na unguwar Ikoyi a lokacin da suka yi jerin gwano suna kada-kade da raye-raye. Har aka ji wani daga cikinsu rauni a kai wasu kuma da dama daga cikinsu sun jikkata. Su ma ’yan tawagar Oko-faaji sun yi ta maza don sun kare kansu amma da illar da za a yi musu ta fi haka yawa.”
Da take jawabi don tabbatar da abin da ya auku, shugabar tawagar Oko-faaji Misis Tola Williams ta shaida wa manema labarai cewa wasu matasa sun kai musu hari yayin da suke dawowa daga filin da aka gudanar da kalankuwar a filin wasa na Tabawa balewa da ke tsakiyar birnin Legas.
Ta ce: “Mutum takwas aka jikkata mana kuma wadanda suka ji rauni an kwantar da su a asibitin gwamnati da ke titin Broad da ke birnin Legas. Wadanda kuka gani a nan wadanda ba su ji mummunan rauni ba ne.”
Wani jami’i a hukumar agajin gaggawa na Jihar Legas ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce: “babu shakka wasu ’yan iska sun far ma tawagar Oko-faaji hari yayin da suka yi jerin gwano suna raye-raye.” Amma ya musanta cewa mutum takwas ne suka ji munanan raunuka yayin fadan.
Ya ce: “karya ne mutum biyar aka yi wa rauni kuma tuni aka yi musu magani cikin gaggawa.”
Bikin kalankuwar na bana, wanda shi ne na shida da Gwamnatin Fashola ta shirya, ya samu halartar tawaga-tawaga 35 daga sassa da dama na jihar.
Bikin wanda aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata a filin wasa na Tabawa balewa da ke tsakiyar birnin Legas ya samu halartar kungiyoyi da manyan baki da ’yan yawon bude ido daga kasashen Afirka da kuma Turai.
kungiyoyin da suka shiga bikin sun hada da kungiyar da ta wakilci unguwar Isolo da Ketu da Ifako Ijaiye da Ogba da Agege da Surulere da Ikoyi da Obalande da Ebute Metta da Isale Eko da kuma Lafiaji.
Sauran sun hada da kungiyoyin koroso da masu wasan kwaikwayo da masu kide-kide da wake-wake da kuma kungoyin wasannin gargajiya daban-daban.
Da yake jawabi a wurin bikin kalankuwar, Gwamna Babatunde Raji Fashola, ya bayanna cewa bikin ya zamo masa wata kafa da zai yi bankwana da al’ummar Jihar Legas.
Ya bayyana cewa gwamnati ta shirya bikin ne don hada kan mutanen jihar da bunkasa harkar yawon bude ido a jihar.