Bikin karrama ’yan fim a Indiya ya tuna da batattun ’yan wasa

Masu shirya bikin karrama ’yan fim na Indiya da aka yi wa lakabi da ‘Bollywoodlife Awards’ sun yi shirin karrama ’yan fim da fuskokinsu suka bace a yayin bikin na bana.Kamar yadda jami’an shirya bikin suka ce, sun yi la’akari da cewa a masana’antar fim ta Indiya, ana samun ’yan wasa da suka shahara kuma […]

Bikin karrama ’yan fim a Indiya ya tuna da batattun ’yan wasa

Aftab Shivdasani

Fardeen KhanHarman BawejaUday ChopraMasu shirya bikin karrama ’yan fim na Indiya da aka yi wa lakabi da ‘Bollywoodlife Awards’ sun yi shirin karrama ’yan fim da fuskokinsu suka bace a yayin bikin na bana.
Kamar yadda jami’an shirya bikin suka ce, sun yi la’akari da cewa a masana’antar fim ta Indiya, ana samun ’yan wasa da suka shahara kuma suka dusashe, don haka a wannan karon za su nemo su domin karrama su, a matsayin wata hanya da za a sake tunawa da su ko kuma a dawo musu da martabarsu ga al’umma. “Irin wadannan ’yan wasa da aka mance da su, sun cancanci a karrama su, musamman domin dusashewar da suka yi ma kawai, suka zabi su ci gaba da rayuwa ba tare da kyale-kyalen wasanni ba, shi ma kansa abin kokari ne. Don haka, a wannan karon, bikin karrama ’yan fim din ya ware kaso na musamman domin karrama su.
’Yan wasan da aka ambata sunayensu domin karramawa sun hada da Harman Baweja da Aftab Shibdasani da Uday Chopra da Fardeen Khan da Zayed Khan da Ameesha Patel da Shushmita Sen. Wadannan jerin ’yan wasa da suka yi tashe kuma suka bace kamar walkiya, shin me suke ciki a yanzu?
Harman Baweja: A can baya, ya yi tashe a fina-finan ‘Lobe Story 2050’ da ‘bictory’ da ‘What’s Your Rashee?’ A halin yanzu, an alakanta dusashewarsa a fim da dalilin kibar jiki da ya yi, duk da cewa an ji labarin yana kokarin dawowa ruwa. Ko zai samu nasara kuwa?
Aftab Shibdasani: Shi kuwa, ya samu nasara a kwanakin baya, kafin tauraruwarsa ta dushe. Ya yi fina-finai da suka kai guda arba’in amma mafi yawansu ba su yi tasiri ba.
Uday Chopra: da ne ga fitaccen daraktan fina-finan Indiya Aditya Chopra. Shi ma ya yi tashe na dan lokaci a baya amma tauraruwarsa ta dusashe. A yanzu haka shi ne ke rike da kamfanin Yash Raj Films, reshen Amurka.