Bikin karrama ’yan fim a Indiya ya tuna da batattun ’yan wasa 1

boyayyun bayanai 3 game da wakar ‘Thriller’ ta Michael Jackson Kamar yadda bincike ya tabbatar, wakar ‘Thriller’ wadda marigayi Michael Jackson ya rera kuma ya tsara ta a faifan bidiyo, tana daya daga cikin fitattun wakokin da suka sama masa martaba da kauna daga masoyansa a duk fadin duniya. An fitar da faifan wakar a […]

Bikin karrama ’yan fim a Indiya ya tuna da batattun ’yan wasa 1

boyayyun bayanai 3 game da wakar ‘Thriller’ ta Michael Jackson
Kamar yadda bincike ya tabbatar, wakar ‘Thriller’ wadda marigayi Michael Jackson ya rera kuma ya tsara ta a faifan bidiyo, tana daya daga cikin fitattun wakokin da suka sama masa martaba da kauna daga masoyansa a duk fadin duniya. An fitar da faifan wakar a ranar 2 ga Disamba, 1983. Mutane miliyan 149 ne suka kalli wakar a ‘YouTube’ na intanet. Ga wasu boyayyun bayanai uku game da wakar:
1-An kashe Dala rabin miliyan daya wajen shirya bidiyon wakar kadai kuma bincike ya nuna cewa, faifan bidiyonta, shi ne ya fi kowane kashe kudi wajen shirya shi.
2-Marubucin wakoki Rod Temperton ne ya rada wa wakar suna ‘Thriller’ amma tun farko shi Michael Jackson ya kudurci sanya wa faifan nasa sunan ‘Starlight.’
3-Akwai sanarwa ta musamman da Michael ya yi a karshen wakar, inda ya barranta kansa da kungiyar matsafa. Bayani ya gabata cewa, ya yi haka ne saboda shi Kirista ne, mabiyin darikar ‘Jehobah Witness.’ Duk da wannan sanarwa, wasu sun rika tsegumin cewa lallai shi dan kungiyar asiri ne.