Bikin karrama ’yan fim a Kano: Nasarori da kura-kurai

A masana’antar shirya fina-finai a ko’ina a duniya ana bukukuwa. Irin wadannnan bukukuwa sun hada da bikin baje-kolin fina-finai inda ake baje-kolin basira da azanci da kuma fikira, sannan a bayar da kyaututtuka ga wadanda suka yi abin a-zo-a-gani, tare da karrama jarumai da dai sauransu.Irin wadannan bukukuwa a cibiyoyin shirya fina-fnai na Bollywood da […]

Bikin karrama ’yan fim a Kano: Nasarori da kura-kurai

????????????????????????????????????

A masana’antar shirya fina-finai a ko’ina a duniya ana bukukuwa. Irin wadannnan bukukuwa sun hada da bikin baje-kolin fina-finai inda ake baje-kolin basira da azanci da kuma fikira, sannan a bayar da kyaututtuka ga wadanda suka yi abin a-zo-a-gani, tare da karrama jarumai da dai sauransu.
Irin wadannan bukukuwa a cibiyoyin shirya fina-fnai na Bollywood da ke Indiya da Hollywood a Amurka da kuma Cannes a Faransa da sauransu ba sabon abu ba ne. A wadannan kasashe a kan gudanar da irin wadannan bukukuwa sau daya a shekara, wasu sau biyu, wasu kuma idan aka yi ba za a sake yi ba sai bayan wasu ’yan shekaru don ya yi armashi ya kuma kara daraja.
A nan arewacin Najeriya, a shekarun baya, an gudanar da irin wadannan bukukuwa a karkashin kungiyar shirya fina-finai ta MOPPAN, inda aka yi irin wannan biki a Kaduna har sau biyu da Kano da kuma Bauchi. Bayan gayyar ta watse, har an manta, sai gashi sabuwar kungiyar shirya fina-finai ta Arewa watau Arewa Film Makers Association ta yunkuro don ci gaba da wannan biki, inda bisa tallafin kamfanin sadarwa na MTN da suka yi niyyar sanya masan’antar shirya fina-finan Hausa a cikin jerin ‘yan uwanta na duniya, wajen shirya irin wannan bikin na karramawa, wanda aka gudanar makon jiya a Kano karo na farko. Sun kuma kuduri aniyar ci gaba da yi duk shekara.
Wannan rahoton ya zakulo nasarori da kuma kura-kuran da aka samu yayin gudanar da bikin, hade da ba da shawarwarin yadda za a magance kura-kuran nan gaba.
Daga dukkan alamu kwamitocin da aka kakkafa don gudanar da wannan biki sun yi aikinsu don ganin cewa kwalliya ta biya kudin sabulu, kuma dole a yaba musu, amma fa da sauran gyara duk da cewa wannan shi ne karo na farko.
An dai gudanar da bikin a wani zauren taro mai suna Afficient wanda ke unguwar Nassarawa. Cikin kwaryar zauren bikin, an yi shiri na kasaita; kamfanin da ya dauki nauyin bikin ya zuba kayan alatu da na kawa, kama daga wajen zama da dandamalin da aka  gabatar da shagalin bikin, komai na zamani ne. Sannan ga fitilu masu bayar da launi iri daban-daban, abin sai wanda ya gani. Kayan kidan da aka yi amfani da su kuwa ko dujjal sai haka. Domin, idan aka sa waka sai hantar cikinka ta motsa saboda da amon kidan. Sannan ga talabijin birjik a cikin zauren, an sa su a kowace kusurwa.
An sa kyamarori masu hasko duk abin da ke gudana a kan dandamalin bikin, ta yadda kana daga zaune, ba sai ka wahalar da kanka ba za ka ga komai a cikin akwatunan talabijin din.
 Gefe guda kuwa, kabaki-kabakin abinci ne da lemo da kuma ruwan sha na alfarma a cikin mazubinsu na robobi, abin tubarkallah. Shirin dai kamar a Turai.
Duk da wadannan shirye-shirye da tanadi na jin dadi, sai da mutane da yawa wadanda aka gayyata, kuma masu ruwa da tsaki a masana’antar shirin fim suka gwammace su hakura da shiga zauren bikin, duk da katin gayyatar da aka ba su mai dauke da bayanin cewa wannan na musamman ne. Da yawa dai komawa gida suka yi domin katin bai yi aiki ba.
Za mu ci gaba.