Bikin murnar cika shekara 50 da fara zuwa duniyar wata (5)

A yau kuma ga mu dauke da takaitattun bayanai daga littafin Dokta Adnan Abdulhamid da ke Kano mai take: WHY ASTRONOMY? Mun fassara babi uku zuwa hudu na wannan littafi, muka buga ga masu karatu.   Allah bai kaddara na karasa aikin fassarar gaba daya ba.  Ga bayanin Dokta kan mahangar Musulunci dangane da ilimin sararin […]

Bikin murnar cika shekara 50 da fara zuwa duniyar wata (5)

A yau kuma ga mu dauke da takaitattun bayanai daga littafin Dokta Adnan Abdulhamid da ke Kano mai take: WHY ASTRONOMY? Mun fassara babi uku zuwa hudu na wannan littafi, muka buga ga masu karatu.   Allah bai kaddara na karasa aikin fassarar gaba daya ba.  Ga bayanin Dokta kan mahangar Musulunci dangane da ilimin sararin samaniya.  A sha karatu lafiya:

Ilimin Sararin Samaniya a Mahangar Musulmi

Sai daga baya na fahimci cewa ashe taurari halittun Allah ne. Na gane haka ne ta hanyar ilimi da kuma tarbiyyar Musulunci. Halittu ne su masu biyayya ga umarnin Allah. An kuma halicce su ne kamar yadda aka halicci sauran ’ya’yan Adam. Sai dai duk da haka, babu wani cikin taurari ko wata ko rana, da ke tasiri wajen sauya abin da Allah Ya kaddara kan mutane ko sauran dabbobin da ke doron kasa. Yin amfani da halittun da ke sama (rana ko wata ko taurari) wajen fassara abin da ke faruwa ga halittu, shi ake kira Ilimin Taurari (Ashraf, 2001:45).  A nasa bangaren, Hakue-Copilah (N.D) ya tabbatar da bambancin da ke tsakanin Ilimin Sararin Samaniya (Astronomy) da kuma Ilimin Taurari (Astrology), inda ya fito da abin fili, ya ce:

“Tabbatar da bambancin da ke tsakanin Ilimin Sararin Samaniya da Ilimin Taurari abu ne mai matukar muhimmanci, domin da yawa cikin mutane sun dauka ma’anarsu daya ce. Duk da yake ba nesa suke da juna ba. “Ilimin Sararin Samaniya” nau’i ne na ingantaccen ilimin kimiyya, kuma halal ne a koye shi, shi kuma Ilimin Taurari jabun ilimin kimiyya ne, kuma haram ne.  Ilimin Sararin Samaniya ya kunshi ilimin sammai ne da kuma fahimtar tsarin da ke tafiyar da dabi’un duniyoyin da ke cikinsu da gungun taurari da ma duniyar baki daya. A daya bangaren kuma, Ilimin Taurari na amfani ne da yanayi ko dabi’un halittun da ke sararin samaniya (taurari da wata da sauran duniyoyi) wai don gano tasirinsu a kan kaddarar da Allah Ya tsara wa mutane.  Har yanzu ba a taba samun wani cin karo tsakanin karantarwar Ilimin Sararin samaniya da karantarwar Kur’ani Mai girma ba.”

Duk da yake wasu lokuta faruwar abubuwa kan dace da wani yanayi. Kamar yadda tarihin Musulunci ya karantar da mu, lokacin da Ibrahim, dan Manzon Allah (SAW) ya rasu, kuma hakan ya dace da lokacin da rana ta yi husufi. Wannan ya sa mutane suka yi ta rade-radin cewa hakan ya faru ne don rasuwarsa. Nan take Annabi  (SAW) ya kawar da wannan mummunar fahimta, cewa wannan husufi bai da nasaba da rasuwar dansa ko kadan, inda ya rika cewa, “Hakika, rana da wata ba su yin husufi don mutuwar wani ko don rayuwarsa.” Don haka Ilimin Taurari ba ilimin kimiyya ba ne ko kadan; wani ilimi ne da ya samo asali daga miyagun akidu da al’adu. Alkur’ani Mai girma ya sanar da mu alakar da ke tsakanin masu ilimin taurari (bokaye) da kuma shaidanun da ke labarta musu dan tsakuren abin da suka fahimta daga wahayin da suke zuwa satar jinsa a cikin sammai, inda kuma a karshe ake jefo wadannan shaidanu da wasu taurari masu harshen wuta. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma hakika Mun kawata saman duniya da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga shaidanu. Kuma Mun tanada musu azabar Sa’ir…” (K:67:5). Haka a sura ta 37:6-11 da kuma 15:16-18).

Hanyoyin da suke bi wajen tara bayanansu galibi ba su wuce kintance da zaton karya mai dauke da yaudara ba. Don haka, addinin Musulunci ya yi na’am da Ilimin Sararin Samaniya, amma bai yarda da Ilimin Taurari ba.  Allah Ya ce: “Suna tambayarka dangane da jira-jiran wata, ka ce: ‘lokatai ne domin mutane da kuma Hajji…” (Sura 2: 189).

Alkur’ani Mai girma cike yake da tsarin nazari kan sammai. Ga ayoyi nan birjik masu kiran dan Adam zuwa yin dubi da izna da tunani cikin halittun sararin samaniya don ganin irin kawa da kuma kintsin da Allah Ya yi musu.  Bucaille (1976:135-151) ya gano ayoyi sama da 50 cikin Kur’ani masu magana kan halittun da ke sararin samaniya da duniyar ma gaba daya.  A karshe ya ce:

“A nan ma, ba karamin abin sha’awa ba ne, musamman idan aka gwama bayanan da Kur’ani ya yi da bayanan Kimiyyar Zamani a bangare daya, da kuma bayanan  da ko kadan ba a hada su da tunanin mutumin da ya yi rayuwa shekara 1,400 da suka gabata ba, a daya bangaren.”

Ba ma Ilimin Sararin Samaniya kadai ba, hatta Ilimin Duniya a dunkule (Cosmology) ma Musulunci ya san shi. Shi ne ilimin da ya kunshi halittar duniya gaba daya da duk abin da ke cikinta.  Shi ne dadadden nau’in kimiyyar da manyan littattafan sama guda uku suka karantar: Attaura da Linjila da kuma Kur’ani.

******

Halittar sammai da kasa gaba dayansu da abin da suke dauke da shi, duk sun samu ne cikin ikon Allah.  Kur’ani ya yi bayani kan taurari, da rana, da wata, da irin tsarin da  duniya ke gudanuwa a ciki, mai ban al’ajabi.  A zamanin yau, fannin Ilmin Duniya a Dunkule (Cosmology) ya zama wani bangare ne cikin fannin Ilmin Kimiyya, kuma shi ne ke lura da tarihin abubuwan da suka faru tun shekaru aru-aru da suka gabata.  Wannan kalma wadda a turance ake kira “Cosmology”, ta samo asali ne daga kalmomi guda biyu cikin harshen Girka; ‘Kosmos’ wadda ke nufin ‘tsari’, da ‘kintsuwa’, da ‘duniya,’ da kuma Kalmar ‘Logos’ mai nufin ‘bincike’ ko ‘tattaunawa’ (kan wani abu).  Don haka, a takaice dai abin da kalmar Cosmology ke nufi shi ne Ilmin duniya gaba dayanta.

A warware kuma, wannan fanni na bayani ne kan buruji ko masaukan taurari, da ranar karshe, da abin da zai faru ga dukkan taurari, da wannan duniyar tamu, da wata, da ma yadda duniyar gaba daya za ta kasance a karshe.  Dukkan wadannan halittu Allah ne Ya halicce su, kuma gaba dayansu duk za su gushe a karshe; kuma gare shi za a tayar da dukkan rayuka don Ya yi musu hisabi.  Sannan bayan haka, an umarci dukkan musulmi da su yi dubi zuwa ga sama, su zurfafa tunani kan tsarin halittarta don su dada fahimtarsu dangane da girman Ubangiji Mahalicci.  Akwai ayoyin Kur’ani masu yawa da suka zo kan haka.

Kur’ani mai girma ya sifata tsarin halittar duniya baki daya, kuma wajibi ne a ilmantar da kananan yara don su fahimci tsarin halittar Ubangiji mai ban mamaki da ke gewaye da su. A lokacin da mutum ke karami ba zai fahimci wadannan ayoyi ba, saboda an saukar da Kur’ani ne cikin harshen Larabci. Amma abu ne mai sauki idan aka saurari tafsirin malamai.  Kamar sauran kananan yara, na samu daman karanta Kur’ani tun ina dan karami, kuma na fahimci mahangar musulunci dangane da halittar duniya gaba dayanta.  A takaice ma dai, na iya cewa wannan na daga cikin abin da yayi tasiri matuka wajen sanya mini sha’awar fannin Ilmin Sararin Samaniya.  Na dada samun karfin gwiwa a lokacin da malamina mai suna Malam Zakariya ya sanar da ni cewa, “Idan kana son sanin Allah, to ka kalli sama, za ka ga abubuwan mamaki da al’ajabi.”  Kuma wannan shi ne abin da Allah Ya fada cikin Kur’ani.  A takaice na iya cewa addinin Musulunci ne ya kara mini kwarin gwiwa kan wannan fanni.