Bikin murnar cika shekara 50 da fara zuwa duniyar wata (I)
Ga wadanda suke bibiyar labaru musamman kan fannin kimiyyar sararin samaniya a ranar Talata 16 ga Yulin bana ne aka fara bikin murnar cika shekara 50 da fara zuwa duniyar wata daga wannan duniya tamu. Sanadiyyar haka ne sashen Hausa na DW da ke Jamus suka tattauna da ni na tsawon minti wajen 10, don […]
Ga wadanda suke bibiyar labaru musamman kan fannin kimiyyar sararin samaniya a ranar Talata 16 ga Yulin bana ne aka fara bikin murnar cika shekara 50 da fara zuwa duniyar wata daga wannan duniya tamu. Sanadiyyar haka ne sashen Hausa na DW da ke Jamus suka tattauna da ni na tsawon minti wajen 10, don yin sharhi a kan muhimmancin wannan rana ko shekara, da irin ci gaban da aka samu tun sannan da kuma darasin da kasashe masu tasowa musamman kasarmu Najeriya za ta iya dauka. Idan masu karatu ba su mance ba dai, ranar 16 ga Yulin 1969 ne Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, (NASA), ta harba kumbo dauke da motocin ziyara a sararin samaniya (Lunar Robers) guda uku, don aika kwararru su gano abin da Allah Ya tanada a duniyar wata, wato tauraron wannan duniyar tamu ke nan. Wannan ayari na mahaya dai ya dauki tsawon kwana hudu ne daga tashinsa daga cibiyar da aka harba shi, ya kuma isa duniyar wata a ranar 20 ga watan Yulin 1969. Wannan ke nuna muna cikin shekara 50 ke nan da faruwar wannan lamari.
Tun daga wancan lokaci kasashe suka fara musabaka da juna wajen zuwa duniyar wata da shuka taurarin dan Adam don manufofi daban-daban. Bayan kasar Rasha ta aika kumbonta dauke da Yuri Gagarin, mutum na farko da ya fara shiga sararin samaniyar wannan duniya tamu, a 1961, sai Amurka ta aika da tawagar farko dauke da su Neil Armstrong da Buzz Aldrin da kuma Michael Collins, zuwa duniyar wata a 1969. Daga nan aka samu kasashe da dama irin su Birtaniya su ma suka aika nasu. Abin da ya fara daga zuwa duniyar wata, wanda shi ne tauraron wannan duniyar tamu, zuwa yanzu an kai ziyara zuwa duniyoyi guda shida da kuma duniyar watanni guda uku.
Dangane da haka Hukumar NASA ta Amurka ta shirya bukukuwa da tarurruka da bitoci kan wannan al’amari, wanda ta fara tun cikin watan Afrilun bana, zai kuma zarce zuwa watan Janairun badi. Duk wannan don kara fadakar da jama’a ne muhimmancin da ke cikin wannan al’amari. Ba Hukumar NASA kadai ba, kafafen watsa labarai na gwamnatocin kasashe da masu zaman kansu da jaridu da mujallu musamman na kimiyya da sararin samaniya, duk sun rubuta makaloli da dama don nuna murna da zagayowar wannan rana. Daga cikin kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin da suka bai wa wannan rana da lokaci muhimmanci akwai BBC da ke Birtaniya da rediyon DW da ke kasar Jamus.
Daga wannan wata da muke ciki har zuwa karshen bana za a ci gaba da ta tattauna wannan al’amari a matsayin wata marhala mai matukar muhimmanci a fannin sararin samaniya, wanda hakan ya haifar da ci gaba mai girma a bangarorin tsaro da sadarwa da yanayi da kuma kimiyyar kere-kere.
A namu bangare kuma ga wadanda suka saba karanta wannan shafi shekara bakwai zuwa 10 da suka gabata, sun san mun gabatar da bayanai masu yawa kan wannan maudu’i. Don haka, daga wannan mako zuwa mako hudu da ke tafe in Allah Ya so, za mu yi waiwaye, abin da Bahaushe ke kira adon tafiya, kan wadancan bayanai da muka gabatar, don bai wa masu karatu musamman wadanda ba su samu damar karanta wadancan makaloli da suka gabata a baya, damar karantawa da samun karuwar ilimi da fahimta.
Bayanan da muka gabatar dai sun hada da amsar tambayoyi da wadansu cikin masu karatu suka aiko da kuma makaloli na musamman da na rubuta kan wannan maudu’i, musamman wadanda suka shafi tauraron dan Adam da kumbo-kumbon da kasashe ke harbawa zuwa sararin samaniya da halittar rana da wata da yadda wannan duniya ke gudanuwa a kimiyyance da dai sauran bayanai masu alaka da wannan ilimi mai matukar muhimmanci musamman a duniyar yau.
Da fatan masu karatu za su ci gaba da kasancewa tare da mu.