Bikin musuluntar wani likita dan kabilar Ibo ya kayatar

Musuluntar wani likita kuma shugaban likitoci na babban Asibitin Gwarzo a Jihar Kano, mai suna Dokta Charles Onyia, ya kayatar.Likitan dan kabilar Ibo an gudanar da gagarumin taron karbarsa zuwa cikin addininMusulunci a garin Gwarzo.Taron da jama’ar garin Gwarzo suka dauki nauyin shirya shi kuma aka gudanar a Cibiyar Musulunci ta Gwarzo, ya samu halartar […]

Bikin musuluntar wani likita dan kabilar Ibo ya kayatar
Bikin musuluntar wani likita dan kabilar Ibo ya kayatar

Musuluntar wani likita kuma shugaban likitoci na babban Asibitin Gwarzo a Jihar Kano, mai suna Dokta Charles Onyia, ya kayatar.
Likitan dan kabilar Ibo an gudanar da gagarumin taron karbarsa zuwa cikin addinin
Musulunci a garin Gwarzo.
Taron da jama’ar garin Gwarzo suka dauki nauyin shirya shi kuma aka gudanar a Cibiyar Musulunci ta Gwarzo, ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da kwamishinoni da Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da shugaban karamar Hukumar Gwarzo da sauran manyan mutane.
Likita Charles Onyia wanda sunansa ya koma Abdurrazzak, ya karbi kalmar shahada ne tun wata uku da suka gabata. Kuma ya ce hasken Musulunci ya shiga zuciyarsa ne tun shekara 17 da suka gabata a lokacin da aka turo shi Kano daga Enugu don aikin neman
kwarewa a likitanci, inda daga bisani gwamnatin jihar ta dauke shi aiki saboda gamsuwa da kwazonsa a aiki.
Bayan tura shi Gwarzo, kwazonsa da kyakkyawan halinsa ya sa mutanen garin suka karbe shi hannu bibbiyu. Ya ce ganin rungumarsa da aka yi tare da gamsuwa da kyawawan dabi’un Musulunci ne ya sa ya karbi Musulunci a ranar 16 ga Mayun bana, kuma ya sauya sunansa zuwa Dokta Abdurrazzak Onyia.
A jawabin Dokta Abdullahi Ganduje ya ce suna cike da gamsuwa da halartar wannan gagarumin taron wanda aka shirya shi “Don musuluntarka Dokta Abdurrazzak kuma mun dauke ka a matsayin dan uwanmu,” inji shi. Ya yi alkawarin ba shi duk taimakon da yake bukata.
karamar Hukumar Gwarzo ta danka wa Dokta Abdurrazzak Onyia takardar zama dan asalin karamar hukumar, tare da daukar nauyinsa zuwa aikin Hajjin bana.
Dokta Abdurrazzak Onyia ya halarci taron karbarsa zuwa Musulunci tare da uwargidansa Misis Justina Onyia da kuma ’ya’yansa.