Bikin Nuna Al’adu: Ali Nuhu ya wakilci Hausawa a Amurka
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu ya wakilci Hausawa yayin da aka gudanar da bikin nuna al’adun Najeriya a Amurka a ranar Litinin.An fara gudanar da bikin ne da misalin 8:00 na dare a Cibiyar John F Kennedy da ke Washington DC a kasar Amurka.Ma’aikatar Yawon Buda Ido da Al’adu da Wayar da Kan Jama’a […]
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu ya wakilci Hausawa yayin da aka gudanar da bikin nuna al’adun Najeriya a Amurka a ranar Litinin.
An fara gudanar da bikin ne da misalin 8:00 na dare a Cibiyar John F Kennedy da ke Washington DC a kasar Amurka.
Ma’aikatar Yawon Buda Ido da Al’adu da Wayar da Kan Jama’a ta Tarayya ce ta shirya bikin mai taken Our Cultural Heritage.
Makasudin shirya bikin shi ne don tallata kayayyakin da Najeriya take da su, wadanda suka hada da fina-finai da wake-wake da kade-kade da marubuta da rubutu da kasuwanci da wasan kwallo da sauransu.
Shugaba Goodluck Jonathan ne babban bako a wurin taron.
Mawaka da jaruman da suka halarci bikin sun hada da Don Jazzy da Rita Dominic da Ali Nuhu da Dabido da Flabour da Tiwa Sabage da Tee Billz da Masterkraft da Tola Odunsi da Leslie Kasumba da Di’Ja da Lola Ogunnaike da Obi Asika da Hakeem Kae-Kazim da Ubi Franklin da sauransu.