Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya: kungiyoyin marubuta sun fara shiri
Ya zuwa yanzu dai kungiyoyin marubutan Hausa daban-daban sun dukufa haikan wajen shirya gagarumin Bikin Ranar Marubuta ta Duniya, wanda ake shirin gudanarwa a watan Oktoban bana a Kano. Hakan kuwa ya biyo bayan wani taro da aka gudanar kwanakin baya da ya samu halartar wakilan kungiyoyin da aka gudanar a ofishin kamfanin wallafa littattafai […]
Ya zuwa yanzu dai kungiyoyin marubutan Hausa daban-daban sun dukufa haikan wajen shirya gagarumin Bikin Ranar Marubuta ta Duniya, wanda ake shirin gudanarwa a watan Oktoban bana a Kano. Hakan kuwa ya biyo bayan wani taro da aka gudanar kwanakin baya da ya samu halartar wakilan kungiyoyin da aka gudanar a ofishin kamfanin wallafa littattafai na Gidan Dabino International da ke Unguwar Sabon Titi Mandawari, Kano.
Taron wanda ya gudana bisa shugabancin fitaccen marubucin Hausa, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), an fara shi ne da misalin karfe 12 na rana, inda Malam Faruk Lawan Da’u ya bude da addu’a.
A jawabinsa na gabatar da taron, Ado Gidan Dabino ya bayyana makasudin kiran taron kungiyoyin marubutan, inda ya ce: “Ganin irin muhimmancin da ke tattare da harkar rubutu da marubuta, an dora mani nauyin shirya yadda za a gudanar da gagarumin Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya. Wannan biki, tun baya can da dadewa ya kamata a gudanar da shi amma saboda wasu matsaloli da suka sha gaban marubuta, ba a samu gudanar da shi ba sai yanzu.”
Ya nemi hadin kan daukacin marubuta da sauran al’umma ta yadda za a samu nasarar bikin, musamman ganin cewa rana ce da za ta kasance abar alfahari ga duk wani marubucin Hausa a duniya.
A yayin gudanar da taron, an tattauna yadda za a samu hada kan marubutan Hausa, inda mahalarta taron suka bayar da shawarwari masu muhimmanci. Malam Bashir Yahuza Malumfashi, a matsayinsa na dan jarida kuma marubuci da ya halarci taron, ya ba da shawarar cewa ya kamata a tuntubi wasu dattijai kuma maganata a harkar Adabin Hausa, wadanda za su kirawo shugabannin kungiyoyin marubutan Hausa domin jan hankalinsu su hada kai domin a gudu tare kuma a tsira tare, musamman wajen bunkasa harkar Adabin Hausa. “A nan, ina ganin a tuntubi Farfesa dandatti Abdulkadir ko Dokta Bukar Usman, domin kuwa ana daraja su a wannan harka kuma za su taimaka wajen ganin an samu hadin kai a tsakanin marubuta, domin gudanar da wannan gagarumin biki.” Inji Bashir.
Shi kuwa Sakataren Taron, Malam Zaharaddeen Ibrahim Kallah, jawo hankalin mahalarta taron ya yi, inda ya ce duk wani abu a aje shi gefe guda, a mayar da hankali kacokan wajen neman hanyoyin da za a gudanar da wannan biki cikin nasara.
Ita kuwa marubuciya, Hajiya Sa’adatu Saminu Kankiya, da take bayar da tata shawarar, ta nemi daukacin marubuta da su bayar da iyaka gudunmowarsu, su nuna kishi domin ganin an samu nasarar aiwatar da bikin. “Kowa ya kamata ya nuna kishi, ya ba da gudunmowarsa ganin yadda za a ciyar da harkar rubutu da marubutan Hausa gaba, ba wai yadda mutum zai gina kansa ko biyan bukatar kashin kansa ba.” Inji ta.
Da ake tsayyana irin abubuwan da za a gabatar a bikin kuwa, an gabatar da abubuwa kamar haka: Baje kolin littattafai, gabatar da kasidu da jawabai, karanta kirkirarrun labarai da wakoki, gudanar da taron bita da sanin makamar aiki ga marubuta da kuma shirya gasa ta musamman ga sababbin marubta.
Kafin a tashi daga wannan kwarya-kwaryan taro, an kafa kwamitoci daban-daban, wadanda za su ci gaba da tsara bikin. Kwamitocin sun hada da na Kudi, bisa shugabancin Dokta Garba Kawu. Sai kuma membobin kwamitin da suka hada da Sa’adatu Saminu Kankiya da Fadila H. Aliyu Kurfi da Umma Sulaiman ’Yan Awaki da Fatima Ibrahim da Iliyasu Umar Maikudi da Rabi’u Na’auwa da Jamila Umar Tanko da Mami Yusuf Yakasai da Zaharaddeen Ibrahim Kallah.
Kwamitin Watsa Labarai kuwa ya kunshi mutane kamar Malam Ibrahim Sheme a matsayin shugaba, a yayin da membobi suka kasance: Bashir Yahuza Malumfashi da Kabir Assada da Al’amin Chiroma da danladi Z. Haruna da Abu Hidaya da Fauziyya D. Sulaiman da danjuma Katsina da Almustapha Musa Ilyas.
A kwamitin Jin Dadi da Walwala kuwa, akwai Umma Sulaiman ’Yan Awaki da Sadiya Garba Yakasai da Hasana Abdullahi Hunkuyi da Maryam Tarau da Jamila Umar Tanko da Bushira Nakura da Kabir Yusuf Anka da Habibu Hudu Darazo da Mukhtar Isa kwalisa da kuma Nura Nasimat da Khadija Mahuta da kuma Halima Abdullahi K/Mashi.
A kwamitin tsaro kuwa, akwai Faruk Lawan Da’u da Auwal G. danbarno.
Ya zuwa yanzu dai kwamitocin tuni suka ci gaba da gudanar da ayyukansu na ganin an cin ma nasarar gudanar da gagarumin bikin na Ranar Marubutan Hausa ta Duniya a watan Oktoba mai zuwa, inda ake sa ran halartar marubutan Hausa daga sassa daban-daban na duniya, musamman ma makwabta, kamar Nijar da Ghana da sauransu.