Bikin Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya: Masarautar Kano ta albarkaci shirin

A ranar Talatar da ta gabata ce Masarautar Kano ta yi na’am kuma ta sha alwashin tallafa wa marubutan Hausa, musamman a shirye-shiryensu gabatar da gagarumin Bikin Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya da ake shirin gudanarwa a bana, inda mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya alkawarta dauki nauyin bayar da kyaututtuka ga […]

Bikin Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya: Masarautar Kano ta albarkaci shirin
Bikin Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya: Masarautar Kano ta albarkaci shirin

A ranar Talatar da ta gabata ce Masarautar Kano ta yi na’am kuma ta sha alwashin tallafa wa marubutan Hausa, musamman a shirye-shiryensu gabatar da gagarumin Bikin Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya da ake shirin gudanarwa a bana, inda mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya alkawarta dauki nauyin bayar da kyaututtuka ga gwarazan marubutan da suka yi nasara a gasar rubutun gajerun labarun kirkira da za a gabatar a yayin bikin.
Damar hakan ta samu ne, a yayin da ’ya’yan kwamitin shirya bikin na ranar marubuta suka kai ziyarar musamman ga sarkin, a fadarsa. Sarkin ya bayyana harshe a matsayin ginshikin karfafa sha’anin siyasa da tattalin arzikin kasa.
A takaitaccen jawabinsa a yayin ziyarar, shugaban kwamitin, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, ya bayyana makasudin shirya bikin ranar marubutan Hausa ta duniya. Ya ce an yi la’akari da yadda darasin Hausa ke samun nakasu ta fuskar koyarwa a wasu jami’o’i da ke koyar da harshen a wasu kasashen duniya, shi ya sanya marubutan Hausa suka kuduri aniyar bunkasa darajar harshen ta hanyar shirya irin wannan biki. Ya ba da misali da cewa: “Jami’ar SOAS da ke Landan a shekarar 2010 tana da dalibai masu nazartar Hausa guda goma, a shekarar 2015 kuwa suna da dalibai guda hudu rak. Haka kuma manyan malaman da ke koyar da darasin Hausa a wannan jami’a duk sun yi ritaya, yanzu saura guda daya ya rage.” Inji Ado.
Daga cikin irin matsalolin da rubutun Hausa ke fuskanta, ya ce har da yadda wasu ke sauya lamirin namiji zuwa mace. “Wani abin takaicin shi ne yadda ake rubuta kalmar mace a matsayin namiji, ko kuma yadda masu gabatar da shirye-shirye a rediyo da talbijin suke yin gurbatacciyar Hausa. Sai ka ji an ce ‘motana, wayana, matana’ da sauransu; maimakon ‘motata, wayata, matata.” Inji shugaban.
A ci gaba da jawabin nasa ga sarki, shugaban kwamitin ya ce bikin na marubutan Hausa ya kunshi gamayyar kungiyoyin marubuta goma sha biyar tare da wasu Hausawan marubuta da malamai daga kasashen Nijar da Ghana da Kamaru da suka yunkuro domin kawo hadin kai da inganta harkar rubutun Hausa da kuma dada cusa kishin rubutu da karatu cikin harshen Hausa.
Shugaban kwamitin ya bayyana irin shirin da kwamitin nasa ke yi, domin ganin an samu nasarar gudanar da bikin na ranar marubutan Hausa ta duniya. “Akwai mukalu da masana daga jami’o’i za su gabatar, masu take kamar haka: 1-Rubutun Adabi Jiya Da Yau: kalubale Da Madosa Ka’idojin Rubutu Da Daidaitacciyar Hausa. 2-Mahimmancin Bincike A CikinRubutu. 3-Hanyoyin Tallata Ayyukan Marubuta A Kafar Intanet. 4-Dabarun Rubuta kagaggun Labarai.”
Bayan haka kuma, duk dai a yayin bikin mai zuwa, Ado Gidan Dabino ya ce  za a yi wa marubutan Hausa da suka riga mu gidan gaskiya ta’aziyya da karramawa ta mussamman. Sannan akwai gasar rubutun gajerun labaru da kwamitin ya shirya ga sababbin marubuta, wadanda ba su taba wallafa littafi ba.
“Yanzu haka an samu wadanda suka shiga wannan gasar, kimanin mutane hamsin, wadanda suka tsara labarai a fannonin rayuwa daban-daban.” Inji shi.
 A cewar shugaban kwamitin, a cikin tsare-tsaren wannan kwamitin su hada da rarraba kyaututtuka ga wadanda suka samu nasara, daga na daya zuwa na uku. Sannan za a bai wa mutane goma kyauta ta bai-daya saboda yabawa da kokarin da suka yi a wannan gasa ta rubutu da suka fafata.
“Wannan dalili ne ya sa muka kawo wa mai martaba Sarki ziyara ta musamman, domin sanin matsayinsa na marubuci dama da hauni da kuma neman tubarraki, yadda wannan taro zai yi albarka.” Inji shugaban.
Ya kuma kara da cewa, akwai tsammanin wannan bikin zai ci gaba da gudana a duk shekara, inda za a rika gudanar da shi a jihohin kasar nan daban-daban da kuma makwabtan kasar nan.  
A nasa bangaren, wanda aka kai wa ziyarar ta ban girma, mai martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya nuna farin cikinsa da hobbasan marubutan Hausa, domin ceto harshen daga irin barazanar da take fuskantar rubutu da furuci.
Sarkin, wanda shi ma kwararren marubuci ne, ya kara da cewa: “Rubutu na karfafa alaka tsakanin masu amfani da harsuna a fadin duniya. Don haka Masarautar Kano na goyon bayan wannan kwamiti da irin ayyukan da ya sa a gaba, kuma za a tsara yadda wannan masarauta za ta dauki nauyin rarraba kyaututtuka ga zakarun da suka samu nasara a gasar da aka sanya ta wannan shekara.”
Bisa ga haka ne ma sarkin ya amince da cewa kyaututtukan da za a mika wa zakarun gasar na bana, a yayin bikin, za a kira su da taken: ‘Kyautar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.’
Daga karshe, mai martaba Sarkin Kano ya karbi kyauta ta musamman daga hannun shugaban kwamitin. Kyautar dai ta littattafai da mujallun da marubutan na Hausa suke wallafawa ne.
Wannan ce ziyara ta farko da kwamitin ya soma gabatarwa, a kokarinsa na shirya bikin ranar marubutan Hausa ta duniya a karon farko. Ana sa ran halartar masana harshen Hausa da dalibai da sauran masu sha’awar rubutu da karatun Hausa daga ko’ina suke a duniya.
Bikin dai zai iya zama zakaran gwajin dafi, bias yunkurin da marubutan Hausa suka yi na ceto harshen da irin yadda ake rubuta shi yadda aka ga dama. Har’ila yau, bikin zai zaburar da sababbin marubuta yadda za su inganta rubutunsu da yadda ake bincike wajen gina labari da kuma yadda ake kasuwancin littatafai ta hanyar zamani,wato intanet.
Tun farkod ai an shirya cewa za a gudanar da wannan biki a bara, saboda wasu matsaloli da kwamitin shirye-shiryen ya fuskanta, sai aka dage shi zuwa bana.
Sai dai a cewar Ado Ahmad, an zabi a gudanar da bikin ne a ranar 3 ga watan gobe, domin ta dace da Ranar Marubuta Ta Duniya da Babbar kungiyar Marubuta Ta Duniya (PEN) da ke da rassa a kasashe daban-daban na duniya ta ware domin karrama marubuta.
A jawabinsa, Sakataren Kwamitin, Malam Zaharaddin Ibrahim Kalla, ya bayyana cewa, kwamitin zai ci gaba da kai irin wannan ziyarar ban girma ga masu martaba sarakunan kasar Hausa, domin neman albarkacinsu a wannan. taron. “Nan gaba kadan za mu kai makamanciyar wannan ziyara ga sarakunan Zazzau da Katsina da Daura da kuma wasu sarakunan da nan gaba za mu fade su.” Inji shi.
A tattaunawa da shugaban kwamitin ya yi da ’yan jarida, yayin wannan ziyara, ya yi kira ga hukumomin gwamnati da kamfanoni da su shigo a tallafa wa wannan kokarin da marubutan Hausa suke yi, domin a cin ma nasarar da aka sa gaba. Ya yi bayanin irin alfanun da za a samu, musamman ga kamfanonin da ke tallata hajarsu cikin harshen Hausa.
Duk dai a wannan rana, kwamitin na marubuta ya ziyarci gidan talabijin na Arewa 24 da ke yada shirye-shiryensa a tauraron dan Adam, inda Shugaban sashin shirye- shirye na gidan, Mista Michel ya tarbi ’yan kwamitin cikin farin ciki da annashuwa. Ya yi jawabi game da ayyukan wannan gidan talabijin da irin abubuwan da ya sa gaba, sannan ya nuna jin dadinsa game da ziyarar da wannan kwamitin ya kai masu.
Sakatare Malam Zaharaddin Ibrahim Kalla, ya bayyana makasudin wannan ziyara, inda ya ce domin neman hadin gwiwar gidan talbijin na Arewa 24 wajen yayata yadda ta wakana a wannan bikin na ranar marubutan Hausa.
Mista Michel ya yi na’am da shirin kungiyoyin marubutan, bias hobbasan da suke yi wajen inganta rubuce-rubucen Hausa da kuma harshen, wanda hakan ya yi daidai da manufar gidan talabijin din. Ya bayar da dama ga ’ya’yan kwamitin da su yi tambayar da suke so, inda wasu daga ciki suka yi tambayoyi kuma ya bayar da gamsassun amsoshi.
An zagaya da ’ya’yan kwamitin sassa daban-daban na gidan da yadda ake gudanar da ayyuka. A jawabansu daban-daban, ’yan kwamitin sun bayyana farin cikinsu da irin karbar da aka yi musu a fadar Sarkin Kano da gidan talabijin na Arewa 24.