Bikin Ranar Rubutattun Wakoki ta Duniya

A shekaranjiya Laraba, 21 ga watan Maris aka gudanar da Bikin Ranar Rubutattun Wakoki a duk fadin duniya. Wannan rana ce da Majalisar dinkin Duniya ta ware domin jaddada muihimmancin rubutacciyar waka ga al’ummar duniya gaba daya dangane da ilimantarwa da fadakarwa da kuma samar da nishadi. Rubutacciyar wakar, kamar yadda majalisar ta ce, hanya […]

Bikin Ranar Rubutattun Wakoki ta Duniya


A shekaranjiya Laraba, 21 ga watan Maris aka gudanar da Bikin Ranar Rubutattun Wakoki a duk fadin duniya.

Wannan rana ce da Majalisar dinkin Duniya ta ware domin jaddada muihimmancin rubutacciyar waka ga al’ummar duniya gaba daya dangane da ilimantarwa da fadakarwa da kuma samar da nishadi. Rubutacciyar wakar, kamar yadda majalisar ta ce, hanya ce da ke bayyana halayen al’umma da al’adunsu da fasaharsu. Haka kuma wani tsari ne na samar da kaifafa tunani da natsuwar ruhin dan Adam, don haka ne ma majalisar ta ware rana ta musamman domin tunawa da ita.

An tabbatar da ranar 21 ga Maris ce a matsayin ranar Bikin Rubutattun Wakoki ta Duniya a yayin taron kungiyar Bunkasa Ilimi ta Majalisar dinkin Duniya (UNESCO), karo na 30 da ya gudana a birnin Paris, kasar Faransa, a 1999.

A taken bikin na bana, an nemi marubuta wakoki su ci gajiyar ranar wajen rubuta wakoki cikin harsunan gida, domin karfafa harsunan da fito da fasahohinsa. Hakan a cewar majalisar, zai taimaka wajen karfafa harsunan, domin kada su bace. Ga kadan daga cikin wasu rubutattaun wakokin da sha’irai suka samar: