Bikin Sallah ba bikin nuna tsiraici ba ne!

A yayin da muke taya al’umma Barka Da Sallah, mun samu wannan muhimmiyar tunasarwa daga Aminu dankaduna Amanawa, Sakkwato 07065654787, wanda ya ja hankalin al’umma game da bukukuwan Sallah. Ga abin da yake ambatawa:Haka Allah Yake ikonSa. Komai ya yi farko tabbas yana da karshe. Haka abin yake ga kowane irin lamari na rayuwa. Bayan […]

Bikin Sallah ba bikin nuna tsiraici ba ne!

Bagizage Ibrahim Hamisu, yana jawabi, a yayin taron Gizago da aka gudanar a Sakkwato a 2012A yayin da muke taya al’umma Barka Da Sallah, mun samu wannan muhimmiyar tunasarwa daga Aminu dankaduna Amanawa, Sakkwato 07065654787, wanda ya ja hankalin al’umma game da bukukuwan Sallah. Ga abin da yake ambatawa:
Haka Allah Yake ikonSa. Komai ya yi farko tabbas yana da karshe. Haka abin yake ga kowane irin lamari na rayuwa. Bayan kammala azumin watan Ramadan mai dimbin falala da tarin albarka sai kuma shiga shagulgulan bikin karamar Sallah.
Hakika lokacin Sallah, lokaci ne na farin ciki da ciye-ciye da lashe-lashe tare da ziyarar dangi da sada zumunci tsakanin ’yan uwa da abokan arziki. Haka kuma lokaci ne da ya halatta a sanya sabbin tufafi da fesa turare mai kanshi da sabbin takalma da dukkan wasu al’amura da za su nuna walwala da jin dadi tare da iyalai amma fa bisa koyarwar shari’a.
Abin mamaki, wani yanayi da muke ciki yanzu ko kuma zamani na nuna wayewa da kaiwa matuka wajen nuna burgewa da ci gaba, galibi lokacin bikin Sallah samari da ’yan mata kan fita ko zaga dangi da ziyarar ’yan uwa ko kuma zuwa wuraren shakatawa da gwangwajewa ko kuma zuwa wajen wasu bukukuwa na gargajiya, kamar hawan da masu martaba sarakuna kan yi a fadojinsu ko ma wani abin da ba wannan ba; cikin shiga ta fitina da tashin hankali.
Abin da kan faru yayin bikin Sallah shi ne, galibi da yawa yara ko kuma samari da ’yan mata kan soma lalacewa ne a ranar Sallah; domin kuwa a lokacin bikin Sallah ne za ka ga mata da dinkuna na tashin hankali, duk wai domin nuna burgewa. Abin takaici shi ne, iyaye kan sakar wa ’ya’yansu mara a lokacin bikin Sallah, su yi duk abin da suka ga dama babu kwaba, ba tankawa.
Galibi abin ya fi kazanta a cikin birane, inda za ka ga ana baje kolin fitsara da rashin kunya a fili. A nan ina nufin ’yan mata kan fita cikin ado da kwalliya masu dauke da jan hankalin duk wani baligi, ta yadda wani lokacin sai ka kasa bambance tsakanin budurwa da matar aure. Da yawan ’yan mata kan fake da zuwa gun samari da sunan karbar ‘Goron Sallah,’ inda za ka iske budurwa ta je dakin saurayi cikin shiga mai motsa sha’awa; wanda shi kuma idan aka yi rashin sa’a marar tsoron Allah ne, ya fito da kudi ya nuna mata amma ya ja hankalinta sosai kafin ya ba ta. Daga nan Allah Ya kiyaye ka ji labarai marasa dadi.
Da yawa daga cikin ’yan mata kan yi dafe-dafe ga samarinsu da sunan ‘Barka Da Shan Ruwa,’ inda za ka ga dukkansu sun sha ado da kwalliya, inda galibi akan yi amfani da wannan lokaci wajen aikata badala. Wata budurwar idan ta yi maka wata shigar, za ka ga ba ta da maraba da tsirara kuma ta fita gaban iyayanta duk da sunan murnar Sallah. Haka kuma abin bai tsaya ga samari da ’yan mata ba, har da kananan yara, inda za ka ga an caba musu ado da kayayyaki masu ban sha’awa da kayatarwa; wanda a nan ma ana samun bata gari masu fakewa da daukar yarinya da sunan za su ba ta ‘Goron Sallah,’ su kai ta dakinsu. Daga karshe ka ji labarin an aikata badala da ita.
Lallai Manzon Allah ya yi gaskiya, inda ya ce a karshen lokaci mata za su rika yawo da kaya amma a tsirara suke. Ya ce ‘kasiyatun ariyatun.’
Kamar yadda na ce, yara da yawa na fara lalacewa ne a lokutan da ake bukukuwan Sallah, domin a nan ne kananan yara kan koyi zukar taba sigari, samari kuma da suke dan busa tabar kan ci gaba zuwa busa tabar wiwi; ’yan wiwi da sholisho kuma kan kurba ruwan khamru uwar laifi. Haka kuma, a wannan lokacin akan motsa sha’awa tsakanin samari da ’yan mata, wai da sunan ‘Happy Sallah,’ wanda daga nan ne yara kan zarce da fitsara da rashin kunya, domin kuwa galibi samari da ’yan mata kowa da ’yan kudi a kugunsa. Su kuma mata ga kwadayi da son abin duniya. Za ka ga yarinya ba ta iskanci amma a rude ta da cewa yau ne kawai. A karshe ka ga Shaidan ya rinjaye yarinya ta ba da kanta.
Haka abin yake idan ka je gidajen shakatawa, inda za ka ga abin ma ya fi muni, domin wuri ne inda kowa ba shi da mafadi. Galibi abubuwa marasa dadin ji kan faru a irin wadannan wurare na shakatawa, musamman ma idan a kace akwai dan karamin kududdufi da za ka shiga ka yi ninkaya, inda za ka iske katti mata da maza cikin ruwa, wai suna wasa ko kuma yana koya mata ruwa. Allah Ya kiyaye!
Haka kuma lokaci ne da ake fitowa kallon sarki. Akan fito cikin ado da kasaita da nuna bajinta da iya kwalliya da yawan iyaye kan bar ’ya’yansu zuwa kallon sarki amma
Ba su san irin illar da hakan kan haifar ba; domin wuri ne da ake cika, mata da maza babu wani wuri da aka ware na maza daban ko na mata daban. A gwamatse ake tsayuwa, yadda irin munanan abubuwan da suke faruwa a yayin ‘Hawan Sallah’ kunne ba zai so jin su ba.
A nan nake son na yi amfani da wannan dama na yi kira, na farko ga samari da ’yan mata da su ji tsoran Allah, su daina shiga mai bayyana tsiraici da surar jiki. Ku sani mutuncinku shi ne ku sanya sutura tagari, wadda za ta suturce jiki gaba daya kuma wallahi ki sani ko dan iska burinsa shi ne ya auri tagari. Ba sai kin nuna albarkar jikinki zai sa samari su so ki ba. Duk wani saurayi da ya rude ki da cewa shigarki ta yi kyau, ki sani wallahi yaudararki yake yi. Don Allah a yi shiga da ta dace da addininmu da kuma al’adarmu. Ki sani koma bayan tunani ne ki rika kwaikwayon Turawa da Indiyawa.
Haka kuma, ina kira ga teloli da su ji tsoron Allah a duk al’amuransu kuma su sani cewa za su kasance ababen tuhuma ranar gobe kiyama a wajen Allah, domin su ne su ke ba da wannan damar ga ’yan mata ta nuna albarkar jiki, ta hanyar yi musu dinkuna na tashin hankali.
Abu na uku shi ne, iyaye ya kamata su sani, ’ya’ya fa amana ne Allah Ya ba ku kuma zai muku tambaya a kan yadda suka gudanar da harkarsu. Lallai ne a sanya ido sosai a kan yara, a ga ina suke zuwa kuma wace irin suturace ke jikinsu kuma su wane suke yawo tare da su? Idan har suka yi haka, wallahi sun yi abin da ya dace kuma za su kubuta har gaban Allah. Da fatan za a kiyaye da wadannan ’yan shawarwari nawa, kuma Allah Ya sa a yi Bikin Sallah lafiya, a gama lafiya. Allah kuma Ya sa ibadun da muka yi a watan Ramadan karbabbu ne.