Bikin Sallah: Fasto ya raba dafaffen abinci ga nakasassu da ’yan gudun hijira dubu
A kokarinsa na yada fahimta a tsakanin Musulmi da Kiristoci, Fasto Yohanna Buru ya ziyarci gidan nakasassu da ke a Titin Kano inda ya ciyar da nakasassu da ’yan gudun hijira dubu domin murnar bukukuwan Sallah karama, inda ya ce ya ciyar da mutanen ne domin su ji dadi kamar kowa a wannan rana ta […]
A kokarinsa na yada fahimta a tsakanin Musulmi da Kiristoci, Fasto Yohanna Buru ya ziyarci gidan nakasassu da ke a Titin Kano inda ya ciyar da nakasassu da ’yan gudun hijira dubu domin murnar bukukuwan Sallah karama, inda ya ce ya ciyar da mutanen ne domin su ji dadi kamar kowa a wannan rana ta Sallah bayan kammala azumin watan Ramadan.
Fasto Yohanna Buru wanda ya jagaronci Kiristoci ’yan uwansa wajen raba kayan abinci da abin sha ya taya Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan.
Fasto Buru ya ce Littafin Mai tsarki ya karantar da su kaunar makwabtansu kamar yadda suke kaunar kansu. Kuma duk abin da za su yi sai sun tabbatar ya yi daidai da karantarwar Baibul. “Wannan ne karo na biyar da muke ciyar da nakassasu Musulmi duk shekara a ranar Sallah. Marasa galihu da nakasassu da zaurawa da marayu da sauransu da ba sa iya ciyar da kansu ne ke amfana da abincin. A lokacin bikin Kiristimi da sabuwar shekarar Miladiya ’yan uwanmu Musulmi suna ziyartarmu domin kara dankon zumunci da fahimtar juna,” Fasto Buru ya ziyarci inda ’yan gudun hijira suke zaune a unguwannin Badarawa da Unguwar Dosa da Barakallahu da Rigasa domin taimaka masu.