Bikin Takutaha ya dauki sabon salo a Kano

Bikin Takutaha da ake yi a ranar 19 ga watan Rabiul Auwal don murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammd (SAW) ya gudana birnin Kano a ranar Asabar inda aka yi zagayen Takutaha a cikin birnin. A lokutan baya akan fara gudanar da bikin mauludi ne ta hanyar gudanar da zaman karatuttuka a majalisai daban-daban, inda […]

Bikin Takutaha ya dauki sabon salo a Kano
Bikin Takutaha ya dauki sabon salo a Kano

Bikin Takutaha da ake yi a ranar 19 ga watan Rabiul Auwal don murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammd (SAW) ya gudana birnin Kano a ranar Asabar inda aka yi zagayen Takutaha a cikin birnin.

A lokutan baya akan fara gudanar da bikin mauludi ne ta hanyar gudanar da zaman karatuttuka a majalisai daban-daban, inda ake kwana ana karatun tarihin Manzon Allah da bayani game da kyawawan halayensa (SAW).
Idan gari ya waye kuma wato ranar Takutaha jama’a da suka hada da maza da mata, manya da yara kan yi ado cikin sababbin tufafi a kuma yi abinci mai kyau inda ake raraba wa gidajen ’yan uwa da abokan arziki. A gefe guda kuma yara kan je su hau Dutsen Dala don nuna murnarsu da zagayowar wannan rana.
Kuma jama’a kan je gidan Babban Malami na Madabo don neman samun albarka da addu’o’i. A gidan babban malamin ne bayan an kammala karatu malaman da ke gudanar da karatu kan gudanar da addu’o’i na mussaman ga jama’ar da suka taru. Almajiransu kuma kan yi amfani da wannan lokaci wajen raba wa mutane addu’o’in tsari da na neman biyan bukatu. Kuma akan ajiye wata kwatanniya cike da rubutun sha inda jama’a kan rika sha.
Har ila yau almajirai kan gwamgwaje a wannan rana inda suke samun sadaka daga jama’a, don neman biyan bukata a wurin Allah.
Sai dai kuma a ’yan shekarun nan bikin na Takutaha ya dauki sabon salo inda jama’a kan gudanar da zagaye na musamman da suke kira da zagayen Takutaha. A wanann zagaye wasu jama’a kan yi hawan dawaki ko jakuna ko rakuma yayin da wasu kuma a kafa.
A lokacin zagayen, jama’a daga unguwanni daban-daban cikin sababbi ko kyawawan tufafi kan gudanar da zagayen a cikin unguwanninsu suna tafe suna salati da sauran zikirori.
Shaikh Sharif Sani Janbulo wanda shi ne Shugaban kungiyar Ahbabun Nabiyyi (Masoya Manzon Allah) kuma shugaban wannan zagaye, ya bayyana wa Aminiya cewa sun fara gudanar da wannan zagaye ne shekara shida da suka gabata. “Mun fara gudanar da wannan zagaye ne
a shekarar 2009, tun a ranar 16 ga watan Rabi’ul Auwal muke fara gudanar da karatuttuka a nan gidana (Janbulo) tare da jama’a masoya Manzon Allah (SAW) har zuwa ranar 19 ga wata. A safiyar wannan ranar ta Takutaha ne muke dunguma gaba daya mu tafi Unguwar Madabo inda muke tafe muna yi wa Annabi salati tare da sauran yabo gare shi irin su Ishiriniya da sauransu. A Madabo ne muke tsayawa mu gudanar da addu’o’i daga nan kuma sai kowa ya tafi harkarsa,” inji shi.
Aminiya ta nemi sanin dalilinsu na gudanar da wannan biki na Takutaha, inda ya bayyana cewa suna yi ne don nuna kauna ga Manzon Allah (SAW). “Kamar yadda aka sani jama’a na gudanar da bukukuwa daban-daban da suka hada da bikin aure da na haihuwa da na murnar samun wani abu ko bikin murnar dawowar wani daga tafiya da sauransu. To idan har za a yi biki don nuna murna ga faruwar wasu abubuwa ashe ba laifi ba ne don mu ma mun gudanar da biki don nuna murnarmu ga zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW). Allah ne kawai Ya san yawan salatin da ake yi wa Annabi (SAW) a wannan lokaci,” inji shi.
Sheikh Sharif Sani ya kara da cewa a yanzu haka wannan zagaye da suke gudanarwa a lokacin bikin Takutaha ya sami karbuwa ba ma kawai a Jihar Kano ko Najeriya ba har ma a sauran kasasshen da ke makwabtaka da kasar nan. “Duk wanda ya fito a wannan rana ya ga irin yadda mutane suka halarci wannan biki, don haka wannan zai ba wa mutum damar gane yadda wannan biki ya samu karbuwa a wajen masoya Manzon Allah (SAW). Baya ga jama’ar da ke jihar, mun samu baki da suka halarta daga jihohi 29 a fadin kasar nan. Kuma mun sami baki daga Nijar da Kamaru da Benin da Ghana da Sudan da Chadi wadnda suka zo tare da matansu. Babban abin da yake hada kanmu shi ne yadda muka jingine bangaren akida a cikin harkar gudanar da wannan zagaye. Abin da muke yi shi ne muna gayyatar dukkan Masoya Manzon Allah (SAW) kawai, hakan ya ba wa jama’a damar halartar bikin,” inji shi.