Bikin wankan sarautar Sarkin Bugaje Ahmad Aghali ya kayatar

A ranakun 15 da 16 ga watan Maris 2014, an yi bikin wankan sarautar Sarkin Bugaje, Ahmad Aghali Ibba, inda manyan sarakunan Nijar da mahukunta suka taru a garin Teni-iya da ke karkashin birnin Tanout a Jamhuriyar Nijar, don tabbatar wa al’umma karfin ikon shugabansu, wanda aka nada bara, bayan rasuwar mahaifinsa.Manyan mutanen da suka […]

Bikin wankan sarautar Sarkin Bugaje Ahmad Aghali ya kayatar

A ranakun 15 da 16 ga watan Maris 2014, an yi bikin wankan sarautar Sarkin Bugaje, Ahmad Aghali Ibba, inda manyan sarakunan Nijar da mahukunta suka taru a garin Teni-iya da ke karkashin birnin Tanout a Jamhuriyar Nijar, don tabbatar wa al’umma karfin ikon shugabansu, wanda aka nada bara, bayan rasuwar mahaifinsa.
Manyan mutanen da suka halarci wannan biki, sun hada da Sarki Abubakar na Damagaran da Gwamnan Jihar Zinder da wakilan kungiyoyin taimakon al’umma na duniya, irin su Odfam da sauran jami’an hukumar kasar Nijar. Mafi yawan manya da shugabanin al’umma da suka taru a wajen wannan biki, sun roki al’umma da su zauna lafiya tare da sabon sarkinsu, su kuma kasance masu biyayya ga hukuma.
Makada da mawaka su ma ba a bar su a baya ba, domin Alin Maliki da Buda Ali Zakin waka da mawakan matan Bugaje sun cashe iya son ransu. Sannan an gudanar da tseren rakuma  da dawakai. Mata mahayan rakuma su ma sun halarci bikin.
’Yan matan Abzinawa sun yi waka a cikin yarensu, a wajen wannan bikin sarauta. An rubuto sunayen mutane da suka ba dimbin kyaututtuka, wadanda aka rika fadi a yarensu, wato Maraugim da Sigisgim da Egim. Don haka Aminiya ta tuntubi wani Ba’auzine ya fassara mata, inda ya bayyana cewa: “Maraugim na nufin jika 50; Sigisgim jika 30 sai Egim jika dubu ko Sefa (CFA) miliyan daya.”
A jawabin godiya da Sarki Ahmad Aghali Ibba, ya yi wa dimbin jama’ar da suka halarci wankn sarautarsa, ya gabatar da kukan al’umma Tenhya, inda ya bukaci Gwamnan Zinder da ya gabatar da matsalolinsu ga Shugaban kasa Mammadu Issufu.
“Kukan Tenhya uku ne, wato satar bisashe ta yi mana yawa; mun san ba ta karewa, amma muna so a rage. Sannan ba mu da razo, wato hanyoyin sadarwar wayar salula. Kuma Tenhya mutane sun yi yawa, amma babu asibiti; idan mace za t ahaihu sai an sha wuya.” Inji shi.
Ana cikin hada-hadar biki, sai hukumar tallafa wa al’umma da agaji ta duniya wato Odfam, ta bukaci a ba ta dama, don ta gabatar da shirinta na jan hankalin al’ummomin kauyuka da su rika sanya ’ya’yansu makarantun zamani. A nan suka gabatar da jawabai, tare da raba takardu dauke da hotunan uwa tana rike da jaririnta. Kuma hukumar raya ilimi ta Jihar Zinder, a karkashin jagorancin Baru Shekarau, wanda ya tashi ya yi jawabi a madadin Gwamnatin kasar Nijar.
“A karkashin shirin gwamnati  na shekara uku, na sanya yara makaranta, an sanya akalla yara dubu a kauyukan da ke Jihar nan,” inji shi.
Wakilan kungiyar Odfam, sun yi godiya ga gwamnatin Nijar da Malam Baru Shekarau da ya yi bayani kan shirin tallafa wa ilimin kananan yara na shekara uku da gwamnati kasar ta bullo da shi.
Su ma jami’an kula da lafiyar dabbobi, sun yi amfani da bikin wankan sarautar, inda suka tunatar da Bugaje da Fulani kan lallai su rika bayar da rakuma da shanu ana yi yi musu allura.
Wanan bikin wankan sarauta ya yi armashi, domin ya samu halartar manyn mutane daga ko’ina a fadin Nijar da kuma kungiyoyin bayar da agaji na duniya.