Bikin wasan gargajiya na Nguon a Kamaru

Muhamman Babalala, a kasar Kamaru A makon da ya gabata ne aka gudanar da bikin ‘Nguon’ na bana a kasar Kamaru, inda al’umma suka hallara kamar yadda aka saba.A duk bayan shekaru biyu, kabilar Bahunawa a yammacin Kamaru suna yin bikin zagayowar “Nguon” wanda shi ne kasaitaccen biki mafi girma da yake hada ’yan kabilar […]

Bikin wasan gargajiya na Nguon a Kamaru
Bikin wasan gargajiya na Nguon a Kamaru

Muhamman Babalala, a kasar Kamaru

A makon da ya gabata ne aka gudanar da bikin ‘Nguon’ na bana a kasar Kamaru, inda al’umma suka hallara kamar yadda aka saba.
A duk bayan shekaru biyu, kabilar Bahunawa a yammacin Kamaru suna yin bikin zagayowar “Nguon” wanda shi ne kasaitaccen biki mafi girma da yake hada ’yan kabilar na ciki da wajen kasa a lokaci guda.
Wannan bikin da ya gudana a zagaye na dari biyar da arba’in da biyar, an debi tsawon mako guda ana gudanar da shi. A duk tsawon wannan lokacin an yi abubuwa daban-daban da suka hada da raye-raye na gargajiya, wasu al’adun da suka shafi rayuwar kabilar ta Bahunawa, da tarurruka na kara wa juna ilimi, hadi da ire-iren abincin da matan Bahunawa suka shahara a kai wurin dafawa.
Hakan kuma bikin ya ba masu yawon bude ido damar dandana abincin gargajiya na wannan kabila ta yammacin Kamaru; wadanda sun rabu gida biyu a fannin addini. Akwai Kiristoci da kuma Musulmi a yankin, wadanda ke tafiyar da al’amuran rayuwa a tare. Wasu fannonin gargajiyarsu kuma suna da nasaba da na Arewacin Kamaru amma kuma inda suka bambanta shi ne, suna yawan yin amfani da gumaka a gargajiyar tasu.
Ya zuwa yau, ana iya cewa bikin wasan gargajiya na “Nguon” ya samu kafuwa sama da shekaru dari shida baya. A irin wannan lokaci ne kuma Basaraken gargajiya na al’ummar yake samu ya gana da mutanensa, ya kuma yi musu jawabi game da halin rayuwar da suke ciki. “Nguon” suna cewa na wasu ire-iren dangin ganyen miya saboda haka samun halartar akasarin jama’a wurin halartan bikin na da alamar cewa girbin hatsi kamar masara, gero da sauransu zai yawaita. Saboda haka bikin “Nguon” da ya dinga gudanawa a shekarun baya ya zame biki ne na karrama albarkatun noma. A dalilin haka ne kusan karni biyar baya aka dinga gudanar da bikin na bayan an yi girbi a tsakanin watannin Yuli da kuma Agusta.
Basaraken da ya kafa daular Bahunawa, wato Nchare, shi ne ya zabi wannan lokacin domin gudanar da bikin a duk bayan shekara biyu. A shekara ta 1394 ne aka fara gudanar da wannan bikin, inda aka dinga yi a kowace shekara. Sai dai kuma tun daga shekara ta 1992, lokacin da basarake na yanzu, wato Ibrahim Mbombo Njoya ya hau kujerar sarauta, ya maida ka’idar cewa bikin za rika gudanuwa duk bayan shekaru biyu.
A karshe dai “Nguon” biki ne da yake da tasiri, inda aka tanade shi domin yada al’adun gargajiya hadi da nuna tsarin sarautar gargajiyar kabilar da kuma wasu tsatsubai da ake kira “Nguri” da kuma “Mbansie.”
Tsatsubar da suke gudanawa na “Nguri” an kebantar da su ne kawai ga ’ya’yan sarki a lokacin da kuma “Mbansie” yake na jama’a baki daya a lokuta kuma daban-daban kamar na mutuwar sarki da wasu al’amura na farin ciki ko kuma bakin ciki da suka shafi dangin gidan sarauta.