Bikin yaye daliban Islamiyya na tatsar iyaye
Makarantun Islamiyya wuri ne da ake karantar da ilimin addini da bayar da tarbiya ta Musulunci, domin tabbatar da al’umma sun ginu cikin tsarin Musulunci.
Makarantun Islamiyya wuri ne da ake karantar da ilimin addini da bayar da tarbiya ta Musulunci, domin tabbatar da al’umma sun ginu cikin tsarin Musulunci.
Ilimin Islamiyya sabon tsari ne da ya wanzu a kasar Hausa da ba zai gaza shekara 50 ba, inda aka zamanantar da karatun addinin Musulunci, domin tafiya daidai da zamani.
Makarantun Islamiyya dai ba a karkarshin hukumomin gwamnatin jihohi ko na tarayya suke ba, sai dai a wasu jihohi ana ba da tallafin gudanarwa ga makaratun, lamarin da ya sa suke cin gashin kansu, in da wadanda suka samar da suke kula da su, ta hanyar kudin makaratar yara da wasu tallafi na gefe da ake samu.
Shigowar sababbin dabi’u da al’adu a bikin yaye dalibai da bikin saukar karatu da makarantun Islamiyya ke yi na kara sa alamar tambaya kan shin wadannan bakin al’adu ko suna da tushe a karantarwa ta Sahabbai da magabata?
Wasu daga cikin wadannan al’adu sun hada da yi wa yara sabon dinki a yayin bikin saukar karatu ko yayin bikin Maulidi da dafa abinci da kai wa makarantar da kawata wuri da tanadin kyaututtuka da kai kaji masu rai da sanya irin rigunan da akan ga daliban makarantu, musamman jami’o’i da manayan makarantu na gaba da firamare kan sanya a yayin yaye dalibai, wadanda ake ganin tushensu ma kamar yana da alaka ta kut da kut da al’adun Turawa.
Sai kuma irin yadda makarantun Islamiyyar ke cajin iyayen yara kudi a yayin bukuwan don yin abubuwa da suka hada da dauko hayar kujerun zama da rumfar da za a zauna da kuma irin abinci da abin sha da za a sha a wurin taron da dai sauran bukatu.
An samu ra’ayoyi sun bambanta tsakanin iyaye da masu ruwa da tsaki kan yadda ake gudanar da bukukuwan yaye dalibai a makarantu a fadin kasar nan, inda wasu ke ganin al’ada ce mai amfani, yayin da wasu ke kallon ta a matsayin dora nauyi ga iyaye masu karamin karfi, musamman duba ga yadda jama’a ke cikin matsin tattalin arzikin da kuncin rayuwa a wannnan lokaci.
Ba daidai ba ne kwaikwayon dabi’un Nasara a wajen bukukuwan sauka-Malam Usman Abdullahi
A tattaunawarsa da Aminiya, Na’ibin Masallacin Juma’a na Nana Oil da ke kusa da Dutsen Zuma Rock a Birnin Tarayya Abuja, Malam Usman Abdullahi ya bayyana cewa, taruwa don taya wanda ya samu haddace wani sashe ko kuwa dukkannin Alkur’ani murna abu ne mai kyau kuma mai asali.
Ya bayyana cewa, “an samu lokacin da Sayyadina Umar amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya haddace wani sashe na Alkur’ani Mai girma, ya tara wasu sahabbai suka yi walima kan murnar wannan falala da Alla (SWA) Ya yi masa. Don haka ba laifi ba ne yin taro don taya wanda ya haddace wasu ayoyi ko ma gaba dayan Alkur’ani,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa,” a wannan zamanin kuma ina ganin yadda jama’a suke baya-baya da karatun addini ne ya sa ake irin wadannan taruka na bikin sauka a makarantun Islamiyya. Wannan na daya daga cikin dabarun jawo hankalin iyaye da dailbai tare da kwadaita masu son karatun.
“Sai dai ba daidai ba ne a rika kwaikwayon wasu bakin al’adu na Nasara a wajen bukukuwan, wato ina maganar bai kamata a rika sanya irin riga da hular nan da masu saukar karatu a makarantun Boko ke amfani da su ba. Dalili kuwa shi ne maganar asalinsu. Kowa ya san daga Nasara suke, kuma suna da wani asali da tasiri a gare su, wanda mu ba mu sani ba. Don haka koyi da su ba daidai ba ne.”
Malam Usman ya kara da cewa, “haka kuma yin liki ko watsa kudi a yayin wadannan bukukuwa shi ma ka iya kai mutum ga fadawa cikin riya ko kuma almubazzaranci. Domin a Musulunci ya dace a girmama duk wani abu da za a yi. Idan za ka ba wa dalibi kyauta ce, to kamata ya yi ka sanya a ambulan ko leda ka mika masa cikin mutunci. Haka kuma idan makarantar za ba wa kyauta ai tana da akawun, sai ka tura masu a ciki.”
Da ya juya kan batun irin kudin da makarantu ke cajin iyayen yara a yayin gudanar da bukukuwan, sai ya ce, “ba daidai ba ne makaranta ta dora wa iyayen yara wani haraji don za a yi saukar karatun dalibai. Amma abu ne da ya kamata a ce, an zauna da shugabannin makarantun da kuma iyayen yara don a samu daidaito da kowane uba ya amince zai iya biya daidai karfinsa.
“Domin da yawa akan sanya iyaye da dalibai cikin kunci, saboda fafitikar kokari kawo kudin ko kuma saboda kasa biyan kudin.”
A Zariya iyaye sun koka kan kudaden da ake karba a bukukuwan
Wasu iyaye sun bayyana damuwarsu ga tsadar wasu bukukuwan yaye dalibai, wadanda kan jefa iyalai cikin wahala, musamman wadanda ba su da halin biyan kudaden da ake bukata.
Sun ce, hakan na iya sanya wasu dalibai jin kunya ko kuma daina zuwa makaranta, saboda tsoron a bambanta su da takwarorinsu.
Malam Musa Dauda, wani mahaifi, ya ce, ba ya adawa da bikin yaye dalibai, matukar ba a matsa wa iyaye wajen biyan kudi ko sayen kayan da ba za su iya ba.
“Ana samun gasa da farin ciki tsakanin dalibai, ta hanyar irin wadannan bukukuwa. Amma ya kamata a gudanar da su cikin sauki ba tare da sanya iyaye cikin kunci ba,” in ji shi.
A nasu bangaren, wasu malamai sun bayyana cewa, manufar bikin yaye dalibai ita ce, karfafa gwiwa da zaburar da dalibai, musamman masu tasowa, tare da karrama wadanda suka kammala karatunsu da kuma wadanda suka yi fice a fannoni daban-daban.
Sun kara da cewa, mafi yawan makarantu ba sa tilasta wa iyaye biyan wasu kudade, domin suna la’akari da halin tattalin arzikin iyalai, tare da amfani da hanyoyin da ba za su zama nauyi ba wajen gudanar da bukukuwan.
Bikin yaye dalibai na karfafa alaka tsakanin makaranta da iyaye-Dakta Nura
Shugaban Makarantar NANA Tarbiyya School da ke Zariya, Dakta Nura Abdullahi ya ce, bikin yaye dalibai na taka muhimmiyar rawa wajen karfafa alaka tsakanin makaranta da iyaye, tare da kara wa dalibai kaimi.
“Ana karrama wadanda suka yi kwazo, domin su zama abin koyi ga sauran dalibai. Wannan na karfafa su, su ma su dage wajen karatu.
Don haka, bikin yaye dalibai ba shi da wani laifi idan an gudanar da shi cikin tsari da adalci,” in ji shi.
Wasu daga cikin daliban kuwa sun ce, suna daukar ranar yayen a matsayin rana ta musamman da suke daukin jira tun kafin karshen zangon karatu.
Sun bayyana cewa, idan aka soke bikin, hakan zai rage musu farin ciki, domin suna kallon ranar tamkar ranar biki da ke ba su damar yin murna tare da iyaye da malamai da abokan karatu, bayan kammala karatunsu.
A Sakkwato iyaye sun nemi gwamnati ta rika biyan albashin malaman Islamiyya
Iyayen yara sun koka kan yadda tallafin kula da yara, domin su samu ilimin addini ke nema sauya salo, ya bar asalin da aka san shi, waton hidimta wa addini zuwa tilasta wa kai.
Malam Maniru Bala mahaifi ne da yake da yara a islamiyya ya ce, “harkar walimar Islamiyya a yau ta koma wahala ce gaskiya, a yanzu a kalla yaro daya in za a yi bikin walimarsa sai ka biya Naira 15,000 zuwa Naira 25,000 har sama, wannan sabon abu ne ga Bahaushe da yake neman zama alakakai.
Buki ake yi gagarumi, iyayen yara na wahala kan lamarin, wanda kowa ya sani ba a boyewa. Ya kamata Fadar Sarkin Musulmi ta shigo, ta yi kira ga al’umma a koma baya, kamar yadda lamarin ya kasance na ci-gaba a da, inda yin walimar yaro ba za ta kasance ta zo wa iyaye da shan wuya kamar yadda ake tatsar mu yanzu ba’’ .
Maniru ya ci gaba da cewa, “bayan ka biya kudi sai ka yi wa yaro sababbin kaya ka dafa abinci, wata makarantar ma sai su nemi ka kawo kaji masu rai, wadanda ba a yanka ba, saboda son rai kawai, in ka duba kasuwa ce suka bude don samun kudi.
Sai ka ji malaman makaranta sun ce, a kawo masu kaji masu rai, wane abu ne haka, ina ganin ya kamata sanya malaman a tsarin albashin gwamnatin jiha don toshe wannan kofa. In yaro bai yi dinki ko biyan kudin biki ba, za ka samu shi da mahaifansa suna cikin damuwa ga kuma gori.”
Ya kara da cewa, “kur’ani ba sayar da shi ake yi ba, don haka bai kamata a samu takurawa ba a cikin lamarin karatun, abu ne da ya kamata a sauya salonsa.”
Na taba samun matsala da matana kan kasa biyan kudin bikin saukar karatu– Malam Aminu
Muhammad Mai Agogo, tsohon malamin Islamiyya kuma uba ya ce, “a makarantar da yarana suke karatu za a yi masu walimar sauka kowane yaro zai ba da Naira 30,000 sannan a dinka masa sabon tufafi. Wannan takura ce, don na taba samun matsala da matana biyu kan na kasa biya wa yarana biyar da suka yi sauka, inda suka ga laifina.”
Da ya juya kan bikin, Malam Aminu ya ce, “malamai sun koma burin tara yawan yara a wurin walima, don haka sai ka ga in lokaci ya karato, ana zuba wa yaro karatu ba ka’ida don ya shiga cikin masu sauka ba tare da la’akari da ingacin karatun da ake koyar da shi ba. Wani abu ma shi ne, da zarar an gama walimar za ka ga yara sun daina karatu, suna ganin sun sauke, alhali ba su san karatun bai nuna ba.”
Ya ci gaba da cewa, “ya kamata iyaye su sani cewa, idan yaro ya sauka, to su dauka daga nan ne yaro ya soma karatu, wato sai a tabbatar da ya fara harda mai inganci da karatun littafai. Don mafi yawa ba hardacewa suke yi ba. Da harda ce da za a ce karatun na cikin kansa.”
“Mata na sayar da kadarorinsu don su biya kudin bukukuwan saukar”
Daga karshe ya yi kira da cewa, “ya kamata iyaye su kashe wannan bidi’a ta saukar kur’ani, don da yawa mata nasayar da kayansu, su biya kudin da ake cajin ’ya’yansu don kar su ji kunya. Na san wadda ta sayar da akuyarta kan bukin. Haka kuma akwai wadda na gani a cikin dare tana neman sayen jaka 100 don yin abin bukin, don haka dai bikin yana kawo fitina tsakanin ma’aurata.”
Komai aka yi a kan kur’ani daidai ne-Alhaji Altine
Shi kuwa wani uba a Sakkwato, Alhaji Altine cewa ya yi, “komai aka a yi kan kur’ani daidai ne, domin malamai suna wahala ga kula da yaranmu har su samu nasarar sauke Alkur’ani. Don haka, duk abin da aka ce a kawo bai yi yawa ba, tsarin samun ilimin ne ya zo haka.”
Iyaye ne ke da sha’awar a yi walimar sauka-Shugaban Makarantar Bin Baaz Islamiyya
Malam Murtala Bello, Shugaban Makarantar Bin Baaz Islamiyya da ke karanatar da yara a Sakkwato da Kebbi a tsokacinsa ya ce, “abin da na sani iyaye ne ke bukatar a yi walima bisa ga sha’awar yaransu, sun kai wani mataki na karatun Alkur’ani, sun samu ci-gaba. Domin in za a yi bikin, ana kiran taro ne da iyaye da ’yan uwan yara za su zo, su halarci walima.
Tabbas yana cin kudi kama daga abin da ya shafi kawata wuri da kyaututtukan da za a raba wa yara. Za a yanke yaro ya bayar da kamar Naira 15,000 ko 20,000 don su ba da damar abubuwan da za a yi. Yanzu haka makaranta da ke Birnin Kebbi mun yi matsaya cewa, ranar 9 Agusta za mu yi walima, kuma kowane yaro da ya sauke zai bayar da Naira 30,000. Wadanda suka hardace kur’ani za su biya Naira 50,000,” in ji shi.
Ya kara da cewa, ”mun yi haka ne duba da halin da iyayen yara ciki, mun san za su iya biya, ba mu takura wa iyaye ba, za ka samu iyaye mata su ne ke taka muhimmiyar rawa a wurin walima. Za ka samu ana rage kudi ga wadanda ba su da hali, wasu ma ana yafe masu baki daya.”
Malam Murtala Bello ya kara da cewa, “a shekara 19 da na kafa makarantar, a sanina ba a cilasta wa iyaye su kawo abinci sai dai a al’ada kowa yakan aiko daidai karfinsa.”
Game da maganar yiyuwar sanya Islmiyya a cikin tsarin albashin gwamnati sai malamin ya ce, “ban aminta da wannan ba ko kadan. Iita gwamnati tana da abubuwan da ta sanya a gaba na bukatun mutane, wanda ko rabi ba ta yi ba har yanzu kama da ilimin boko da lafiya da hanyoyi, ballantana ta shiga abin da ba nata ba. In ta fara ba da albashi za ta yi karambanin juya makarantun sai ka ga sun dauki wani bangare na siyasa. Hakan ba zai haifar da alheri ba ga malaman Isalmiyya.”
A Yobe iyaye sun ce ana tatsarsu a bukukuwan
Duk da yake harkokin karatun addinin Musulunci a tsakanin al’ummar Musulmi a Yobe kullum sai kara habaka yake yi, sakamakon yawaitar bube makarantun Islamiyya da a sannu a hankalin suke kan hanyar maye makarantun allo ko kuma rage tasirinsu a tsakanin al’umma.
Sai dai rahoton da Aminiya ta samu, ya gano yadda makarantun Islamiyya ke kirkiro wasu hanyoyin samun kudade daga iyayen daliban a-kai-a-kai da kuma yadda wannan sabon salo ke addabar iyayen daliban, ta yadda a kullum suke kokawa kan yawaitar karbar kudade daga gare su.
Allah ne kadai zai biya malaman Islamiyya-Malam Tijjani
A kan hakan ne Aminiya ta samu jin ta bakin wani mahaifi, Malam Ahmad Tijjani a kan ko ya gamsu da yadda makarantun Islamiyya ke gudanar da harkokin karantar da yaransu da kuma yadda suke kirkiro wasu bukuwan da ke sa daliban ke zuwa suna damun iyayen a kan karbar kudade a-kai-a-kai?
Sai malamin ya bayyana cewa, “lallai da farko na gamsu da yadda makarantun ke koyar da yaranmu ilimin addinin Musulunci kamar yadda ake so.”
Ya ci gaba da cewa, “to sai dai a kan batun yawaitar kudade da makarantun ke karbar wannan yana damun mu, wadda har a wani lokaci mukan ce, shin me ke sa hukumomin makarantun na Islamiyya ke yawaita karbar kudade daga hannunmu? Mafi yawan lokaci za ka tarar da yaro ya zo, yana ta sharbar kuka a kan wai an ce musu sai sun kawo wasu kudade kaza da kaz,a don yin wasu hidimomin da ba wajibi ba ne a addini.
Don haka a nawa ganin yawaitar karbar kudade barkatai daga hannunmu yana damun mu sosai, kuma muna son shugabannin makarantun su sani cewa, wasu ladaddakin fa Allah SWT ne zai biya su.”
Mukan sauya wa yaranmu makaranta kan kudin sauka-Malam Sani Wali
Shi kuwa Malam Muhammad Sani Wali da Aminiya ke tambayar sa a kan wannan lamari na makarantun Islamiyya sai ya ce, shi kam a gaskiya akwai lokutan da makarantun na Islamiyya ke kokarin gudanar da abubuwan da ba bisa dacewa ba, tare da tilasta wa daliban da sai sun kawo kudaden gudanar da wadannan irin bukuwa, tare da matsa musu lamba a kan sai sun dinka kayayyaki na musamman duk da kayayyakin makaranta da aka dinka musu, ba tare da la’akari da irin halin matsin tattalin arzikin da ake ciki, musamman a irin wasu bukukuwan kamar mauludi da bikin yaye daliban da sauransu.
A cewarsa “a mafi yawan lokuta, irin wannan halayya na matukar damun mu, ta yadda wani lokaci har mukan yanke shawarar cire yaran daga wannan makaranta ta Islamiyya, don canza su, zuwa wata makarantar da ke da saukin lamari.
Babu wani bikin da muke gudanarwa da ba ya kan ka’ida-Shugaban Islamiyya
Aminiya ta tuntubi wani shugaban makarantar Islamiyya Malam Abubakar Ahmad kan ko me ke sawa, suke kirkiro wasu bukukuwan da ke sa iyayen yara ke gajiyawa da irin kudaden da ake karba daga gare su, da ke sa iyayen daliban ke kosawa a kan hakan?
A nan sai malamin ya amsa da cewa, shi a ganin sa babu wani bikin da suke gudanarwa da baya kan ka’ida kuma kowane biki ba ya yiwuwa sai da kudi, wanda ala tilas sai sun nemi dalibansu da su tara kudaden gudanar da bukuwan, wanda za su karbo daga iyayensu.
Don haka yake jaddada cewa, akwai bukatar iyayen yara su rika daurewa da kuma hakuri a kan wannan lamari, wanda ba duk lokaci ake yi ba, sai dai in lokacin yin abin ya zo, musamman kan abin da ya shafi bukuwa irin su saukar karatu da bikin yaye dalibai, wanda suna kan kowane dalibi da sauran bukuwa.