Bilinbituwar bobon bokokon babban Baushe (2)
Tundurkin tanderun tanda Tawayar tauye toye-toyen ta’ada Tande-tanden taraddadin gasar ganda Tuttule tulun ramin randa Tunkuyar tattala rabashen ragadada Musun maganganun magabata Murkusun mutunta magabta Marairecewar matalauta Makarkashiyar murkushe makusanta Miskilancin makamar mahukunta Nuku-nukun nukura Mashakon makoshin mai mura Tattakin takura Shirye-shiryen shegantakar shekara Kararen kambama kakarar karkara Haka ake wasan dara […]
Tundurkin tanderun tanda
Tawayar tauye toye-toyen ta’ada
Tande-tanden taraddadin gasar ganda
Tuttule tulun ramin randa
Tunkuyar tattala rabashen ragadada
Musun maganganun magabata
Murkusun mutunta magabta
Marairecewar matalauta
Makarkashiyar murkushe makusanta
Miskilancin makamar mahukunta
Nuku-nukun nukura
Mashakon makoshin mai mura
Tattakin takura
Shirye-shiryen shegantakar shekara
Kararen kambama kakarar karkara
Haka ake wasan dara
Ana sassafar safara
Nomau-na-manomi taki ya ci tura
Almajirai na ta bara
Jimirin juriyar shakara
Mutane sun gundura
Ana ta haifar da asara
Mun shantake muna jira
Kullum ai ta kiraye-kirayen kira
Rakashewa na kasura
Bukatu ba su da fifiko
Maufofi masu matukar mamako
Muku-mukun matsalolin mako
Turka-turkar taga-tagar ture tarko
Carin carar cakwaikwaiwa cirko-cirko
Balulluba
Ko bahallatsar gaba
Da bilinbituwar kwaba
Birgimar barin saba
Bagararwar bobon jibgin jiba
Bututun batutuwan bokoko
Basajan barkono a koko
Burgar burge bako
Bushe-bushen roko
Bukkokin dakon dako
A bar shaci-fadi
Don kar a shiga rudi
Manufa kowa ya samu budi
Talaka da mai kudi
Kowa na iya barin sudi
A assa asusun alkinta awalaja
Hada-hadar harhada haja
Banga-bagar basaja
Logar luggar laftun lahaja
Maje-hajin hanin hajijiyar manhaja
Balullubar bahallatsar bilinbituwar birgimar bagararwar bobon bokokon babban Baushe, bushashar bushe-bushen burgar bugun buguzum ce a fannonin faskaren fasko fasahar fannonin fahimtar fafutikar al’amuran rayuwa, inda a babbar bukkar bokoko a kan yi uwar watsi watsa-watsa da kinkimar kimiyyar kintsin kayayyaki da fasa fasahar kyallaro kyalkyalin kalkale kyale-kyalen kere-keren kirkirar kankantar karfin karafuna. Kuma a yi ta toye-toyen tanderun tandar tande-tanden tauye tumatirin tuganden tattasai, musamman a wajen koyi-ka-koyar da kwashe-kwashen kwanson kwasa-kwasai. Watakila ma shi ya sa aka samar da kwararan kwararrun zaratan zakakuran masana kimiyyar kintsa miya da karajin karfin karatan karfa-karfan kafafar kumbiya-kumbiyar kamuya-muya da ke ta bini-binin bankarewar botsare-botsare burgar burgewa.
Shin dakon dakon mangalar aura ake yi ko jiran gawon shanu? Wadansu dai na bushe-bushen rikon roko a burgar burge bako a bututun batutuwan bokoko don jin dadin kwankwadar koko. Don haka sai a yi ta tunkudo tundurkin tanderun tandar tawayar tauye toye-toyen ta’adar Tande-tanden taraddadin gasar gargadar gada-gadar gudun gadar gandar ta’anatin tuttule tulun ramin randar tunkuyar tattala romon rabashen ragadada. Irin wannan yanayi ke haifar da musun maganganun magabata a murkusun mutunta magabtan mutane da ke tabbatar da marairecewar matalauta, ta hanyar makarkashiyar murkushe makusanta a miskilancin makamar mahukunta
Babu abin da mummunar ta’ada ke haifarwa irin rashin bai wa bukatu muhimmai fifiko, tare da manufofi masu matukar mamako, har a samu kauce wa muku-mukun matsalolin mako da turka-turkar taga-tagar ture tarko, ballantana a karke da ce-ce-ku-cen carin carar cakwaikwaiwa cirko-cirko.
Dagar dogewar dambarwar dandatsar damatsan dumuiniyar dawurwrin firgicin fargabar faragar fagamniyar fangimar fagagen ilimantarwa ke haifar da koyi-ka-karkatar da doki ka dakatar ko ma a karke da dabarbarun doki-ka-dankwafar. Daukacin tsilli-tsillin tsauraran matsalolin da ke ci wa al’umma tuwo a akushi, sun yi kawanyar kwakumar kadandoniyar zautuwar zanzaron zawarawan zirga-zirgar ziryar zurarewar zamani. Sai dai da zarar an yi zabarin zaburar zungurar zirin zara zaro-zaron zanzaron zabgewar zazzage su, aikin kan ci tura cikin lamarin lamirin larurar lumanar lullumin lumana lullum!
Ganin haka ta sanya na ce, a dai yi watsi da sa-in-sa ko matsin lambar da aka tursasa wa masu gwanlangwaso da kwalisar kantakaryar kwarkwasa, abin yi kawai a dai dage a ci gasa. Kwalliya ce dai a dandasa, kuma gidan bikin ma fa a karasa, sannan baje-koli a karkasa, har ayyuka su kankama wasa-wasa, sai a jajirce wajen ganin garkamamun kofofi an kwankwasa.
Tun da akwai bukatar zumun zumuntar zaman zamanin zamunna, sai na bijiro da bukatar da a ba ni fura-mai-kyau in sha a yau, ko gobe na yi kyau-kyau da darandakau ga walwala sakayau, musamman in an yi mini sassaucin sarkakiyar sasarin sakanni-in-dire, saboda ai Ilimu ke hana a dare, kuma a samu daukacin faffadar hanya duk a share, a kara samun kimar matsayi a dare, har al’umma ta murmure, ta more, bayan duk wasu wahalhalu an jure.
Don cimma kyakkyawar manufa, lallai a kauce wa sare-sare da kwalisar kwanare a kai-kawon ’yan ta-more, wadanda suka samu wurin zama suka share, inda suke ta yi wa al’umma bare-bare
Jan janjamin juriyar Jajircewar jimirin jinkirin Jam’in jama’ar jami’o’i, wajen karade kowane zira’i don kauce wa balbalin bala’i, tun daga safe zuwa isha’i, ta yadda za a yi ta samun sa’a sai saisayen saye-sayen samamen sa’i. To sai a kinkimi kimiyya da fayyace fasahar kirar kere-kere, ta yadda kusan daukacin fanoni a tattare a watsattaken wangale wagage littattafai na baje koyi-ka-koyar a faifai da ake yi a tare, har mu samu kai wa ga gacin ganiya. Kuma mu kara kaimin karfafa sagaraftun sarrafa sinadarai da inganta Ilmin sanin tsirin tsiron tsirrai, tare da na halittu, inda za a rika dubin dubiyar bibiyar bin kadin duba birai, tunda a cikinsu akwai jarirai da manyan ja’irai. Daga nan sai daga likafar likitanci, yadda Bokan Turai zai tarairayi rai, tare da binciken ayyukan kwarai a daukacin ayyukan da suka sha bamban da kakarin karime-karimen kanikancin kacici-kacicin kutungwilar katutun katantanwar kangarewa.
Dangane da batun bisashe, sai a daina duk wani hasashe ko dabarbarun kwashe-kwashe, tunda tuni gari ya washe, shi ya sa ake da bukatar ganin mun killace su a kowane sashe. Al’amarin da ya shafi gayaunar garka don ribatar rabautar gararumar rani da kaka a hantsin hantsewar hatsin haskakawa, lallai kayan marmari a yi musu tufka, tamkar yadda al’amura ka iya kasancewa a bagiren zamanin jika da kaka.