Bin diddigi: Shin da gaske an bude bodar Legas don shigo da motoci?

Shin da gaske ne Tinubu ya ce a bude bodar a shigo da motoci?

Bin diddigi: Shin da gaske an bude bodar Legas don shigo da motoci?

Bodar Seme da ke Legas

Gabatarwa

Labarai da ke yawo a kafafen sada zumunta a Najeriya suna ta bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin a bude bodar kasar.

Tun a ranar Laraba aka fara yada labaran, amma daga Alhamis sai labarin ya fara canjawa, inda aka ware cewa wai bodar Seme ta Jihar Legas kawai aka bude domin a rika shigo da motoci.

Shafin “Gawuna kawai forever” da ke dandalin Facebook ya ruwaito cewa: “Labari da dumi-duminsa. Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce za su bude boda domin a ci gaba da shigo da motoci da abinci. Ka ga jagoran talakawa mai kishin talakawa. Muna rokon Allah Ya yi riko da hanayyen ka amin.”

Shi kuma wani mai suna Comrd Abubakar Hamisu Tijjani rubutawa ya yi cewa, “Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin bude boda amma iya motoci ne za a rika shigo da su.”

Shi kuma wani mai suna M Inuwa MH, wanda dan jarida ne ya rubuta cewa, “bodar ma da za a bude ta iya Jihar Legas. To ai [s]hi ke nan.”

Bin diddigin labarin

Aminiya ta bi diddigin labarin domin gano ainihin inda aka samo rahoton, amma hakar ta bai cim ma ruwa ba domin babu wata babbar kafar watsa labarai da ta rawaito labarin.

Sai dai a wani labarin da Jaridar Punch ta ruwaito, ta rawaito Daraktan Sufuri na Kasa na Ma’aikatar Sufuri, Ibrahim Musa yana cewa a zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari masu fito suka rubuta wasika zuwa ga Ministar Sufuri inda suka bukaci a bude bodar.

A cewar shi, “Mun taba zuwa nan (Bodar Seme) da tsohon Minista a Ma’aikatar Sufuri inda masu fito suka bukaci a bude bodar domin cigaba da shigo da motoci. Da kuma koma ministan ya umarce mu da mu shirya takardar da zai gabatar a gaban Majalisar Zartarwa, wanda kuma hakan aka yi. Sannan bayan ya gabatar an amince da bukatar,” in ji shi, sannan ya kara da cewa bayan an amince da bukatar, sai majalisar ta amince a bar batun a gadar da shi zuwa ga sabuwar gwamnati domin ta yanke hukunci.

Da wannan bayanin ne Jaridar Punch ta kafa hujja, inda ta rawaito cewa an kusa bude bodar, amma a cikin labarin baki daya, babu inda ta ce Gwamnatin Tarayya ta ce a bude bodar ta Seme.

Aminiya ta tuntunci wani jami’in Hukumar Kwastam, inda ya tabbatar da cewa labarin na kanzon kurege ne.

Kammalawa

Bisa dalilan binciken Aminiya, wannan labarin na bude bodar Seme domin shigo da motoci ba gaskiya ba ne. Amma ta yiwu a waiwayi lamarin kasancewar daraktan ya ce sun gabatar da shi a baya duk da cewa hakan yana ta’allaka ne da tsarin sabuwar gwamnatin da sabon minista da za a tura Ma’aikatar Sufuri.