Bin doka da oda ne zai yi maganin gobarar tanka a Legas – Shugaban kungiyar RTEAN
Shugaban kungiyar Masu Motocin Haya reshen Jihar Legas (RTEAN), Alhaji Muhammad Musa Maitakobi ya ce dole sai direbobi sun bi dokar tuki sannan za a iya shawo kan matsalar gobarar da tankokin mai ke haddasawa a jihar. Shugaban ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a makon nan. “Ai muddin direbobi ba […]
Shugaban kungiyar Masu Motocin Haya reshen Jihar Legas (RTEAN), Alhaji Muhammad Musa Maitakobi ya ce dole sai direbobi sun bi dokar tuki sannan za a iya shawo kan matsalar gobarar da tankokin mai ke haddasawa a jihar.
Shugaban ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a makon nan. “Ai muddin direbobi ba su daina tukin ganganci ba kuma muddin masu motocin haya ba su daina ba direbobin da ba su kware ba motocinsu, to babu yadda za a yi a iya maganin gobarar da tankokin mai ke haddasawa a jihar. Za ka ga direba bai kware ba an ba shi tukin tanka, ya dauko ta makare da mai babu abin kashe wuta a cikin motar. Idan ma an sanya abin kashe wutar to za ka guda daya ne tak kuma sannan direban bai kware ba saboda haka da ya zo kwana sai ka ga ya kada motar, gobara ta tashi.” Inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Ya kamata masu motocin tanka su gane cewa ba kowane direba ba ne yake iya tukin tanka, sai kwararre mai lalasi na matakin ‘E’ sannan kuma sai ya samu horo sosai; idan ba haka to zai rika haddasa hadurra. Da yawa direbobin da ke tukin tanka ba su san idan sun zo kwana su buda sosai ba sai ka ga sun shiga kwana a haka sun kayar da motar. Shi kuwa fetur abu ne da idan ya gangara kwatami to fa duk inda ya hadu da wuta zai tashi. Shi ya sa kake ganin gobarar da aka yi kwanakin baya ta janyo mummunar asara.”
Ya bayyana cewa saboda haka ne kungiyarsu ta RTEAN ta dauki matakai don ganin cewa kwararrun direbobi ne ke tuka motocin membobin kungiyar a jihar.
“Mun sha bamban da kowace kungiya. Mu ba kara zube muke ba, muna da tsari da ka’idoji. Ba kowane diraba muke yarda mu ba motocinmu ba sai wanda muka tabbatar ya kware kuma ya san tukin amma da yawa za ka ga direba ba shi da cikakkun takardu, bai iya tuki ba amma an dauki mota an ba shi. Mu ba mu yarda da haka.” Inji shi.
Ya yaba wa matakin da gwamnan jihar ya dauka na daukar matakan da suka dace don maganin matsalar.