Bin sunnar Annabi (SAW) ke tabbatar da sonsa a zukata (2)

Daga Hudubar Imam Mustapha Yusuf Shu’aib, Limamin Masallacin Wuse Zone 5, Abuja Ta haka Abdullahi ya kubuta daga yanka shi, Allah Ya kubutar da shi ne don me? Allah Madaukaki Ya kubutar da shi ne daga yanka, saboda a gadon bayansa yana dauke da mafi girman halitta da ya kasance yana bibiyar tsatso tsarkaka zuwa […]

Bin sunnar Annabi (SAW) ke tabbatar da sonsa a zukata (2)

Daga Hudubar Imam Mustapha Yusuf Shu’aib, Limamin Masallacin Wuse Zone 5, Abuja

Ta haka Abdullahi ya kubuta daga yanka shi, Allah Ya kubutar da shi ne don me? Allah Madaukaki Ya kubutar da shi ne daga yanka, saboda a gadon bayansa yana dauke da mafi girman halitta da ya kasance yana bibiyar tsatso tsarkaka zuwa mahaifu masu tsarki har ya iso zuwa ga Abdullahi.

An haifi Manzon Allah (SAW) a ranar Litinin a shekarar giwaye, don haka marhaban da haihuwar masoyi (SAW) a wannan rana.

Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da amincin mai yawa.

Huduba ta Biyu:

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Wanda Ya aiko ManzonSa da shiriya da addinin gaskiya domin Ya rinjayar da shi a kan addini dukansa koda mushirikai sun ki. Ina gode masa Matsarkaki a bisa abin da Ya bayar kuma Ya ni’imta, kuma ina yi maSa shukura a bisa abin da Ya daukaka kuma Ya girmama. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayy a gare Shi, ba Ya da tamka ko kini, Ya daukaka a cikin malakutinSa da rububiyyarSa, kuma Ya kadaita a cikin wahadaniyyarSa da uluhiyyarSa. Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu Annabi Muhammad bawanSa ne, masoyinSa ne, zababbenSa ne, kuma ManzonSa ne.

Allah Ya bude rufaffun zukata da shi, Ya sanya wa makantattun idanuwa suna gani da shi da kuma jiyarwa ga kurumtattun kunnuwa. Tsira da Aminicin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako da aminci mai yawa.

Bayan haka, ku ji bi Allah da takawa ya ku bayin Allah! Ku sani bin Allah da takawa ba ta tsaya a kan yin azumi da rana da kiyamul laili da dare ba ne kawai, sannan a yi sakaci a tsakaninsu. A’a bin Allah da takawa yana nufin jin tsoron Allah da tsayuwa wajen bin umarninSa da guje  wa zubar da jinin Musulmi da cin mutuncinsu ko dukiyarsu. Duk wanda ya yi da’a ga Allah da ManzonSa kuma ya ji tsoron Allah, ya yi maSa takawa, to wadannan su ne masu samun babban rabo.

Ya ku Musulmi! Lallai girmama janibobin Al-Mustapha (SAW) da Sunnarsa mai girma na daga cikin rukunan imani da ka’idojin addini. Allah Mai tsarki da Daukaka Ya ce a cikin abin saukarwarSa mai hikima: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku gabatar da wani aiki a gabanin Allah da ManzonSa….” har zuwa karshen aya. Kuma Ya ce: “Kada ku shiga gidajen Annabi face an yi muku izini zuwa ga cin abinci ba tare da kuna jiransa ba…” kuma Mai girman daraja Ya ce: “Lallai wadanda suke cutar da Allah da ManzonSa an la’ance su a duniya da Lahira…”

Wadannan hukunce-hukuncen shari’a ne da suka wajaba a kan Musulmi su hadu a kansu domin kare su daga hallaka da izinin Allah kuma su kasance da su sababi abin hana musu da sabani da rarrabuwa a tsakaninsu. Allah Madaukaki Ya ce: “Ka ce: “In kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku.” Kuma Matsarkaki Ya ce: “Wadanda suke saba wa umarninsa su ji tsoron wata fitina ta same su ko kuwa wata azaba mai radadi ta same su.”

Wannan domin lallai sura da halayen girmama Annabi (SAW) da Sunnarsa da sonsa suna da yawa da nau’o’i daban-daban. Kuma mafi girman dalilai da mafi girman shaidu a kan girmama matsayin Annabi (SAW) domin tabbatar da sonsa a zukata shi ne bin Sunnarsa mai girma, mai tsarki, a zahiri da badini da lizimtar yi masa da’a a koyaushe kuma a cikin kowane hali. Babu wani dalili da ya fi shiryarwa a kan girmamawa da soyayya fiye daga yin wannan biyayya mai albarka da lizimtar Sunnar Annabi (SAW).

Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi da’a ga Allah da ManzonSa, kada ku juya baya daga gare shi alhali kuna ji. Allah Mai tsarki Yana cewa wannan shiriya hakikaninta kuma cikakkiyarta ba za ta samu ba, sai ta hanyar bin Al-Mustapha (SAW) da yi masa da’a. “Idan kuka yi masa da’a kun shiryu kuma ku bi shi akwai tsammanin za ku shiryu. Bin Sunnar Annabi (SAW) a cikin dukan halaye shi  ne hakikani kuma ginshikin girmamawa da karramawa da darajantawa ga Annabi (SAW), haka yin aiki da maganganunsa da ayyukansa.

Ya ku mutane! Ku guji wasa, kuma ku yi koyi da Annabi Muhammad (SAW), idan ba haka ba, sai soyayyarku ta zamo barrantacciya. Domin soyayya ta hakika ta gaskiya ba ta cika sai tare da bin umarce-umarcensa da guje wa hane-hanensa (Sallahu Alaihi Wasallam). Kuma lallai ne cewa asibitin Manzon Allah (SAW) cike yake da magunguna da aka jarraba su wajen magance cututtukanmu na jiki da ruhi. Domin haka a cikin dabbaka shiriyarsa akwai samun rabo a duniyarmu da Lahirarmu. To me zai hana mu yi aiki da magungunansa kamar yadda kwararren likitan ya siffanta mana?

Allah Madaukaki Ya ce: “Ka ce: “Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, sai Allah Ya so ku.” Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Dayanku bai zama mai imani, har sai son zuciyarsa ya kasance mai biyayya ce ga abin da na zo da shi.”

“Shin za ka saba wa Ubangiji ne kuma ka ce kana bayyana sonSa,

Wannan ba zai yiwu ba a kiyasi mai kyau.

Da soyayyarka ta kasance gaskiya ce da ka yi masa da’a,

Lallai masoyi ga wanda yake so, mai yi masa da’a ne.”

“Na rantse da Ubangijinka ba za su zamo masu imani ba, sai sun sanya ka mai yin hukunci a cikin abin da suka samu sabani a tsakaninsu. Kuma ya zamo ba su ji wani kunci a cikin zukatansu ba game da hukuncin da ka yi. Kuma su mika wuya mikawa.”

Ya ku bayin Allah! Allah da ManzonSa sun umarce mu da yawaita salati a kan shugabanmu mai cetonmu masoyinmu Annabi Muhammad (SAW)

“Lallai ne Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi tare da taslimi da sallamawa.” Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya yi min salati daya Allah zai yi masa salati goma, wanda ya yi min salati goma Allah zai yi masa salati dari….har zuwa karshen Hadisin”

Za a iya samun Imam Mustapha Yusuf Shu’aib ta tarho: 08025203756 da 07030439049