Bin sunnar Annabi (SAW) na tabbatar da sonsa a zukata

Kuma Ya wajabta wa bayi yi masa da’a da taimakonsa da girmama shi da sahibtarsa da tsare hakkokinsa.

Bin sunnar Annabi (SAW) na tabbatar da sonsa a zukata

Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Ya aiko AnnabinSa a matsayin rahama ga duniya, shugaban masu takawa kuma hujja a kan dukan talikai.

Ya aiko shi a lokacin da ake kamfar manzanni, sai Allah Ya shiryar da al’umma da shi zuwa ga tafarki mikakke kuma Ya haskaka hanya da shi.

Kuma Ya wajabta wa bayi yi masa da’a da taimakonsa da girmama shi da sahibtarsa da tsare hakkokinsa da wajibansa.

“Allah Ya kebe rahamarSa ga wanda Ya so, kuma Allah Ma’abucin falala ne Mai girma.”

Ina gode maSa Madaukaki Mai tsarki, kuma ina tuba gare Shi, ina neman gafararSa ina rokonSa Ya amfanar da mu da ambaton magabatanmu kuma Ya shiryar da mu zuwa ga hasken addininmu da na Annabinmu.

Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, ku saurara halitta da al’amarin juya ta naSa ne, tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

Shi ne Yake cewa a cikin abin saukarwarsa mai hikima: “Lallai ne hakika, Allah Ya yi babbar falala a kan muminai domin Ya aika a cikinsu da, Manzo daga ainihinsu yana karanta ayoyinSa a gare su, kuma yana tsarkake su kuma yana karantar da su Littafi da hikima, kuma lallai su sun kasance daga gabani, hakika suna cikin bata bayyananniya.” (Al-Imrana:164)

Kuma na shaida lallai shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad bawanSa ne kuma Manzonsa, wanda yake cewa cikin abin da ya tabbatar daga gare shi daga Hadisin Abu Ammar Shaddad, cewa lallai shi ya ji Wasila bin Al-Aska’u yana cewa: “Na ji Manzon (SAW) yana cewa: “Lallai ne Allah Ya zabi Kinanata daga cikin ’ya’yan Isma’il kuma Ya zabi Kuraishawa daga Kinana, kuma daga Kuraishawa Ya zabi Bani Hashim kuma Ya zabe ni daga Bani Hashim.” Muslim Kitabul Fada’il. Allah Ya kara tsira a gare ka ya ilimin shiriya da alayenka da sahabbanka da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.

Bayan haka, ya ku masoya Almustapha (SAW), Allah Madaukaki Yana cewa: “Kuma a lokacin da Allah Ya riki alkawarin annabawa: “Lallai ne ban ba ku wani abu daga Littafi da hikima, sa’an nan kuma wani manzo ya je muku, mai gaskatawa ga abin da yake tare da ku; (face cewa), lallai ne za ku gaskata shi, kuma lallai ne za ku taimake shi.”

Ya ce: “Shin, kun tabbatar, kuma kun riki alkawariNa a kan wannan a gare ku?” Suka ce: “Mun tabbatar.”

Ya ce: “To ku yi shaida, kuma Ni a tare da ku Ina daga masu shaida. To wadanda kuma suka juya baya a bayan wannan, to, wadannan su ne fasikai.” (Al-Imrana 81-82).

Daga wannan aya ya bayyana a gare mu cewa lallai Allah Mai tsarki da daukaka Ya sanar da annabawa dukansu game da haihuwar wanda za a aiko a matsayin rahama ga talikai.

“Ba Mu aiko ka ba face rahama ga talikai.” A cikin kowace marhala ta harkokinsu, domin talikai a duniya suna kama da ayari, yayin da annabawa suke jagorantar kowane ayari.

Kowane manzo aka aiko ba makawa ya san farko hanyarsa da karshenta.

Kuma ayyukan da aka ba ayarin ba makawa su zamo sanannu ga jagoran. Kowane jagora yana kai ayarinsa zuwa wuri mafi daukaka da daraja daga inda magabatansu suka tsaya gwargwadon abin da ya gani da kuma gwargwadon yadda Allah Ya yi masa baiwa.

Don haka a bisa hankali babu wani abu da zai hana Allah Ya nuna wa kowane jagora a kan ’yan uwansa jagorori ko a kan sunayensu da ayyukansu.

Abin da yake tabbatar da haka shi ne fadinsa Madaukaki game da AnnabinSa Isa (AS) a kan Annabinmu (SAW): “Kuma a lokacin da Isa dan Maryama ya ce, “Ya Bani Isra’ila! Lallai ni, Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bayar da bushara da wani Manzo da ke zuwa a bayana, sunansa Ahmad (Mashayabo).” (Q:61:6).

Hakika kafin haihuwar Annabi rahama (SAW), duniya ta hadu duffan zalunci da miyagun abubuwa wani a kan wani, sun rayu cikin tsoro da kashe-kashe da gallaza wa masu rauni, sun binne ’ya’yansu mata suna ta kwankwadar giya da ayyukan caca, mai rauni yana fama da bakin zalunci, ana dankwafe fakiri ana haramta wa mace hakkokinta, ana gwabza yaki kan ’yan kananan abubuwa, inda wutar yakin ke watsuwa ya cinye kore da busasshe ya jawo wa daukacin jama’a rugujewa da wargajewa.

Sai ya zamo gabashi da yammacin duniya a wancan lokaci suna ta neman wanda zai kubutar da duniya mai ceto dan Adam daga kaifin zalunci da darkakewar da take barazana ga duniya.

“Kuma ku tuna ni’imar Allah a kanku a lokacin da kuka kasance abokan gaban juna, sai (Allah) Ya daidaita zukatanku, kuma wayi gari da ni’imarSa ’yan uwan juna, kuma kun kasance a bakin ramin wuta sai Ya tserar da ku daga gare ta.”

Kuma Ya sake cewa: “Kuma ba Mu aiko ba face rahama ga dukkan duniya.”

Kuma “Abin da yake a cikin sammai da kasa suna tasbihi ga Allah, Mamallaki, Mai tsarki, Mabuwayi, Mai hikima.

“Shi ne Wanda Ya aika a cikin mabiya al’adu, wani Manzo daga gare su yana karanta ayoyinSa a kansu, kuma yana tsarkake su, kuma yana sanar da su Littafin da hikimarsa ko da yake sun kasance daga gabaninsa lallai suna a cikin bata bayyananna.”

Jimillar abin da ake cewa shi ne: Lallai karni na shida Miladiyya ya kasance daga cikin mafiya hadari a tarihin dan Adam.

Duniya ta kasance tana ninkaya a cikin matsaloli masu hadari ta yadda suke barazana ga daukacin mutanen duniya.

Hakika duniya ta kasance tana bukatar abin da zai kama hannunta zuwa ga tafarki madaidaici.

A shekarar da aka haifi Manzon ceto dan Adam (SAW) ne Abrahata Sarkin Yemen ya kai hari a kan Ka’aba Mai girma domin ya rushe ta.

Ya je da babbar runduna da manyan giwaye ke sahun gabanta wadanda suke daddage duk wani abu da ke kan hanyarsu ba ta barin komai, har mayakan suka isa Makka ya shige ta, sai Abrahata ya isa ga Larabawa mazauna kauye yana cewa: “Ba ni nufin komai face rushe Ka’aba, kuma da ku shiga sha’anina ba ba zan cutar da ku ba.”

Sai mutane suka gudu zuwa kan duwatsu, kuma a yayin shigar sojojinsa sai Abrahata ya samu wani rakumi, sai ya kama shi, rakumin ya kasance na Abdulmudallib ne, sai ya je ya same shi ya ce masa: “Lallai rakumin da ka kama, rakumina ne na zo ka ba ni.”

Sai Abrahata ya ce, cikin takama: “Hakika na dauka ka zo ne domin ka hana ni rushe Ka’aba wadda kuke da’awar cewa dakin Allah ne.”

Sai Abdulmudallib ya ce: “Ni rakumi ne nawa, shi kuwa daki na Allah ne, Ubangiji zai kare shi. Sai shi ma ya nufi kan dutse yana rokon Allah Ya mayar da kaidin ’yan ta’adda, azzalumai daga rusa Ka’aba. Sai Allah Ya karbi addu’ar Ya aiko a kansu da wasu tsuntsaye jama’ajama’a.

Rakumin Abdulmudallib ya tsira, kuma dakin Allah Mai girma Ka’aba ma ya tsira. Allah Mai girma Ya yi gaskiya inda Ya ce: “Ashe ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da mutanen giwa ba? Har zuwa karshen surar.

Sai Larabawa suka kara girmama Abdulmdallib suka sallama masa mabudan Ka’aba, kuma hidimar mahajjata dakin Allah Mai girma ba makawa wannan mutum mai girma ya yi tarayya a cikinsa, sai ya kasance Abdulmdallib ya sanya manyan Makka cikin wannan lamari.

Kuma Abdulmudallib ya kasance mutum mai gaskiya, ya taba cewa: “Idan Allah Ya azurta ni da ’ya’ya maza goma suna kiyaye bayana suna kare da kuma dakin Allah Mai alfarma, zan yanka daya daga cikinsu a matsayin neman kusanci ga Allah Madaukaki.”

Sai kuma ’ya’yansa maza suka kai goma, ya yi nufin ya cika alkawarinsa, ya yi kuri’a a kan ’ya’yan nasa, sai ta fada a kan shugabanmu Abdullahi, mahaifin Manzon Allah (SAW).

Abdullahi ya kasance mafi kyawun ’ya’yansa, sai ya kama hannunsa, daya hannunsa kuma rike da wuka. Sai ya tafi Ka’aba domin ya gabatar da shi a matsayin neman kusanci ga abubuwan bautarsu.

Abdullahi ya tafi tare da shi cike da mika wuya, amma sai Kuraishawa suka yi jayayya da shi, suka kalubalance shi suka ce: “Akwai wata boka masaniya da ke da kusanci da ababen bauta.

“Ka tafi zuwa gare ta, mai yiwuwa ta samar maka mafita. Suka tafi ka zuwa gare ta, ta tambaye su nawa kuke biyan diyya a wurinku? Suka ce rakuma goma.

“Sai ta ce, ku yi kuri’a a tsakanin rakuma goma da Abdullahi, idan ta fada a kan Abdullahi ku kara goma har sai kuri’ar ta fada a kan rakuma.”

Sai suka yi ta yin kuri’a tana fadawa a kan Abdullahi sai da suka kai rakuma dari kafin ta fada kansu, sai suka yanka su.

Daga Hudubar Imam Mustapha Yusuf Shu’aib Limamin Masallacin Wuse Zone 5, Abuja Fassarar Salihu Makera

Za a iya samun Imam Mustapha Yusuf Shu’aib ta tarho: 08025203756 da 07030439049

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda