Binance zai daina hada-hada da Naira
Idan ba mu fatattaki Binance ba, Binance zai durƙusar da tattalin arzikin wannan ƙasa.
Babban Kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance ya ce zai daina musayar kuɗin Nijeriya na Naira daga ranar takwas ga wannan watan na Maris.
A cikin wata sanarwa da kamfanin na Binance ya wallafa a shafinsa na intanet, ya ce duk waɗanda kuɗinsu na Naira ya rage a cikin asusunsu, zai a mayar da shi kuɗin kirifito na stablecoin idan wa’adin ya cika.
Matakin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da gwamnatin Najeriya ta tsare wasu manyan jami’an kamfanin Binance a birnin Abuja.
- Jeff Bezos ya karɓe ragamar mai kuɗin duniya daga hannun Elon Musk
- Daurawa ya shiga ofis bayan dawowarsa Hisbah
Hukumomi na zargin Kamfanin Binance ne da laifin “ƙayyade farashin kuɗin ƙasashen waje a ƙasar.”
A makonnin da suka gabata ne Gwamnatin Nijeriya ta zargi Binance da taka muhimmiyar rawa wajen tashin farashin dala a ƙasar da kuma lalacewar darajar naira abin da ya jefa tattalin arzikin ƙasar cikin mawuyacin hali.
Darajar takardar kuɗin Najeriya – Naira dai ta yi faɗuwar da ba a taɓa gani ba a tarihi tun bayan da Shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ƙyale kasuwa ta tantance darajarta.
Lamarin ya ƙara jefa tattalin arzikin Nijeriya da kuma al”umma ƙasar cikin garari, abun da ake ganin ya samo asali daga cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.
A bayan nan ne Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso ya bayyana cewa “kusan dala biliyan ashirin da shida na bi ta Binance ta hanyoyi da masu amfani da manhajar da ba za mu iya tantancewa ba”.
Haka kuma, a wata hira da gidan Talabijin na Channels, Bayo Onanuga, kakakin fadar shugaban Nijeriya, ya zargi manhajar kirifto da sa farashin kuɗin waje a ƙasar tare da karɓar matsayin babban bankin.
“Idan ba mu fatattaki Binance ba, Binance zai durƙusar da tattalin arzikin wannan ƙasa. Kawai suna ƙayyade farashin,” kamar yadda ya bayyana.
Wata majiya daga Fadar Shugaban Nijeriya ta shaida wa TRT Hausa cewa, kamfanin Binance bai yi rajista da hukumomin ƙasar ba, sannan gwamnati ba ta samun haraji daga ɗimbin ribar da Binance ke samu daga hada-hadar da yake yi a ƙasar, matakin da ke yin illa ga tattalin arzikinta.
Haka kuma, majiyar ta ce babu gamsassun bayanai kan adadin ’yan Nijeriya da ke hulɗa da Binance da kuma yawan kuɗin da ake hada-hadar su.
Kazalika, majiyar ta ƙara da cewa, gwamnatin Nijeriya na zargin cewa masu aikata laifukan da suka shafi harkokin kuɗi da masu neman kuɗin fansa suna amfani da manhajar wajen musayar kuɗaɗe ba tare da wata kafa ta iya bibiyarsu don gano abubuwan da suke yi ba.