Bincike maganin cutuwa
Barka da warhaka Manyan Gobe Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘bincike maganin cutuwa’. Labarin na kunshe ne da yadda kyawun fuska ke iya yaudarar mutum. A sha karatu lafiya. Taku: Gwaggo Amina Abdullahi Bincike maganin cutuwa Akwai wani karen daji wanda yunwa ta dame shi sosai. Ya yi yawon […]
Barka da warhaka Manyan Gobe
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘bincike maganin cutuwa’. Labarin na kunshe ne da yadda kyawun fuska ke iya yaudarar mutum.
A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi
Bincike maganin cutuwa
Akwai wani karen daji wanda yunwa ta dame shi sosai. Ya yi yawon neman abinci amma bai samu ba. Musamman da namun daji suka sama wa kansu kariya daga yadda makiya ba za su iya zuwa su kashe su. Rannan sai wata dabara ta fado masa, sai ya sami buzuwar rago ya je ya shiga garken raguna. Akwai wata karamar tunkiya da ke neman mahaifiyarta. Da ta gan shi sai ta yi tsammanin mahaifiyarta ce. A hakan ya jawo ta zuwa wuri mai nisa da ko ta yi ihu ‘yan uwanta ba za su jita ba. Suna isa bakin rafi sai ya cire buzuwar jikinsa ya kashe tunkiya ya cinye.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi a kan wannan labarin. Kada a yi saurin yanke hukunci idan an ga kyakkyawan mutum a tsaya a yi nazari a kan halinsa. Da tunkiyar ta tsaya ta kare wa karen kallo da za ta gene cewa ba mahaifiyarta ba ce.