Binciken malaman Kimiyya kan tsibirin Bamuda (4)

Dalili na uku suka ce shi ne wani irin sinadarin kumfa da ke samuwa a saman manyan tekunan duniya, irin su tekun Atilantika da sauransu.  Wannan sinadari mai dauke da yanayin kumfa da a Turancin Kimiyya ake kira Methane Hydrates, kumfa ne da ke samuwa a saman teku, mai dauke da iska a cikinsa, wanda […]

Binciken malaman Kimiyya kan tsibirin Bamuda (4)
Binciken malaman Kimiyya kan tsibirin Bamuda (4)

Dalili na uku suka ce shi ne wani irin sinadarin kumfa da ke samuwa a saman manyan tekunan duniya, irin su tekun Atilantika da sauransu.  Wannan sinadari mai dauke da yanayin kumfa da a Turancin Kimiyya ake kira Methane Hydrates, kumfa ne da ke samuwa a saman teku, mai dauke da iska a cikinsa, wanda kuma samuwarsa a saman tekun ke yin tasiri wajen rage nauyin ruwan da ke tekun.  Wannan nauyi na ruwan teku da ake kira Water density, karfinsa ne ke iya daukar jirgin ruwa da abin da ke dauke a kansa, don yin shawagi daga gaba zuwa gaba.  Idan karfinsa ya ragu sanadiyyar samuwar wannan kumfa mai dauke da sinadaran Methane Hydrates, sai nauyin ruwan ya ragu, ta hanyar komawa kasa da yake yi, don baiwa kumfar damar mamaye ilahirin bigirensa.  Da zarar jirgin ruwa ya doso wuri irin wannan, inji wadannan malamai na kimiyya, sai ya fada cikin wannan kumfa, inda kuma babu iya mizanin nauyin ruwan da yake bukata don wuce wannan wuri.  Nan take sai kumfar yayi kasa, tare da jirgin, sauran ruwan tekun kuma ya maye saman jirgin, har a kasa samun buraguzansa.  Wannan hujja kan jiragen ruwa ke nan.  Amma ta yaya aka yi hakan ke shafar jiragen sama?  Nan ma suna da ta cewa.
Tasirin wannan sinadari na Methane Hydrates a kan jirgin sama kuma shi ne, idan ya taso a saman teku, ya mamaye iya bigiren da zai iya mamayewa, bayan nauyin ruwan tekun da yake ragewa, har wa yau, suka ce yana yin tasiri wajen rage nauyin iskar da ke sararin samaniyar tekun ma, watau Air Density kenan a Turancin kimiyya.  Idan kuma aka samu raguwar iskar da ke sararin samaniya, wacce ke tasiri wajen karfin dagawa da saukar da jirgi ke yi, to nan take jirgi na iya rasa daidaituwarsa a sama, har ya rikito kasa.  Kuma tunda a saman teku ne, da zarar ya fado cikin ruwan, nan take wannan kumfa ta Methane Hydrates na iya sulmuyar dashi karkashin tekun, ba tare da bata lokaci ba.  
Hujja ta hudu da ke haddasa faruwar hadarurruka a wannan kusurwa ta shedanu a cewar Malaman Kimiyya, ita ce mahaukaciyar guguwa mai dauke da iska da ruwan sama, irin wacce kasashen Amurka da Karibiyan ke fama da ita a duk shekara, watau Hurricane, a harshen Turanci.  Tasirin wannan mahaukaciyar guguwa yana samun jiragen ruwa ne kadai, ban da jiragen sama.  Suka ce mahaukaciyar guguwa na iya kife jirgin ruwa, tare da sulmuyar da shi nan take, a kasa ganin dukkan sassansa.  Da aka tambaye su hujja, sai suka ce akwai jirgin ruwan kasar Faransa tafkeke, mai suna Francisco de Bobadilla, wanda mahaukaciyar guguwa ce ta kifar tare da sulmuyar da shi nan take, ko gawarsa ba a gani ba!  Wannan lamari ya faru ne cikin shekarar 1502, kuma har zuwa yau ba a samu buraguzan jirgin ba.   Malaman Kimiyya suka ce in har haka zai kasance ga wannan babban jirgi, to hakan na iya kasancewa ga galibin kananan jiragen ruwan da suka ta bacewa a wannan Tsibiri da ke kusurwar shebanu.
Sai hujja ta karshe, wacce ke da dangantaka da abin da suke kira Magnetic Poles, a Turancin kimiyyar karkashin kasa.  Malaman Kimiyya suka ce bincike ya nuna cewa wannan duniya tamu, daga sararin samaniya zuwa can karkkshin kasa, akwai wasu sinadaran maganadisu (Magnetic Wabes), da ke manne da dirkokin duniya, watau Earth Poles a bangaren gabas da bangaren yamma.  Wannan sinadarin maganadisu yana yin tasiri ne wajen janyo duk wani abu mai nauyi da ke saman iska a wannan jihohi na duniya.  Wannan ya hada da jirgin sama da kuma na ruwa.  Da suka kaddamar da bincike, sai ya tabbata cewa wannan mahalli na kusurwar shedanu da ke tsakanin tsibirin Bamuda da sauran jihohi, yana zaune ne daidai inda wadannan dirkokin duniya a bangaren yamma suke.  Wannan, a cewar Malaman, ba zai rasa tasiri ba wajen haddasa hadarin jiragen sama da na ruwa.  Suka ce tunda wuri ne mai yawan zirga-zirgan abin hawa, haka na iya kasancewa.  Wadannan, a takaice, su ne ra’ayoyin Malaman Kimiyya kan dalilan da ke haddasa wadannan hadarurruka masu ban mamaki da ake gani amma aka kasa fahimta.  Sai nau’in ra’ayi na uku.
Ra’ayin ‘Yan Zahiri
Masu nau’in wannan ra’ayi na kira su  “’Yan Zahiri” ne domin sun sha bamban nesa ba kusa ba, da masu sauran ra’ayoyin da suka gabata.  Shugaban masu wannan ra’ayi shi ne Farfesa Lawrence Kusche da ke Jami’ar Arizona a kasar Amurka.  Malamin Jami’a ne mai sha’awar binciken kwakwaf.  Kuma kamar yadda bayanai suka gabata a baya, shi ya fara zuwa da sabon tsarin bincike kan dalilan da ke haddasa wadannan hadarurruka.  A cewar Kusche, duk abubuwan da ake ta fada shirme ne.  Babu wani abu sabo da ya raba irin hadarin da ake samu a wannan wuri da wanda ake samu a sauran wuraren da ke wasu nahiyoyin duniya.  Ya yi wannan tsokaci ne cikin littafinsa mai suna The Bermuda Triangle Mystery: Solbed, wanda ya rubuta cikin shekarar 1975.  
Farfesa Kusche ya ce dukkan cece-kucen da ake ta yi kan wannan kusurwa na shedanu shirme ne.  Babu wani abu sabo da ya cancanci a tsaya ana mamaki kansa.  Da farko ya ce idan aka kwatanta yawan jiragen sama da na ruwa da ake ikirarin sun bace a tsibirin Bamuda, da wadanda suka bace a wasu wuraren, musamman bakin gaban tekun kasar Jafan, sai a ga ma ba wani yawa ba ne da su.  Na biyu kuma ya ce, idan aka sake la’akari da irin yanayin zirga-zirgan da jiragen sama da na ruwa ke yi a yankin, har wa yau, za a ga ba wani abin mamaki don an samu yawan hadarurrukan da ake ta kukan suna faruwa lokaci-lokaci.  Abu na uku, Farfesa Kusche ya ce akwai karin gishiri cikin labaran da ake bayarwa ma.  A cewarsa, wasu hadarurrukan ba su faru ba kamar yadda ake ta ikirari; akwai karin gishiri don labarin ya yi dadi.  Na hudu, ya ce akwai karancin bincike yayin da wani hadari ya faru.  Ya ce sau tari idan wani jirgi ya yi hadari, aka rasa inda buraguzansa suke, nan take ‘yan jaridu da masu bincike za su yi ta ihun sanar da duniya cewa ga abin mamakin da ya sake faruwa.  Amma bayan tsawon lokaci, ko da an gano buraguzan, ba su sani balle su juya akalar labarin da suka bayar a farko.  Abu na biyar, Farfesa Kusche ya ce wasu labaran da ake bayarwa na hadarin wasu jirage musamman na sama, karya ne, ba su faru ba.  Misali, akwai labarin da ya yadu a littattafai da bakunan masu labarai kan wani jirgi da aka ce ya fadi a farfajiyar tsibirin Daytona, watau Daytona Beach, cikin shekarar 1937.  Ya ce bincike ya tabbatar da cewa wannan labari karya ne, hadarin bai faru ba.  A karshe dai ya ce duk labaran da ake ta bayarwa kan wannan tsibiri, ko dai karairayi ne, ko kuma an yi karin gishiri a kan labarun gaskiya, ko kuma rashin fahimta ce kawai da son kambama abin da bai cancanci kambamawa ba.  Dankari!  Wani zancen sai malaman jami’a.
A Ina Gaskiyar Take?
Bayan koro bayanai kan dukkan wadannan nau’ukan ra’ayoyi da marubuta suka tafi a kai na dalilan da ke haddasa wadannan hadarurruka a tsibirin Bamuda, mai karatu zai so sanin wanne ne gaskiya daga cikinsu?  To kafin mu yi nisa, kuma kamar yadda duk wani musulmi ya sani ne, sanin hakikanin abin da ke faruwa a wurin, da ma sauran wurare, sai Allah.  Abin da zai iya taimaka wa mai karatu fahimtar burbushi ko kanshin gaskiya dangane da wannan wuri, shi ne yin la’akari da yanayin labaran.  A iya bincike na, zan iya cewa dukkan ra’ayoyin da suka gabata na da kanshin gaskiya kan dalilin da ke haddasa hadarurrukan, komai kankantarsa kuwa.  A ra’ayin farko, wanda shi ne abin da ya fi shahara, ma iya cewa ba mamaki idan aka samu wasu halittu masu yin tasiri wajen faruwar haka.  Da ikon Allah komai na iya faruwa.  Kuma a bayyane yake cewa duk abin da ya faru, yana iya samun dalilan fili da na boye.  Don haka ma iya daukar ra’ayin farko a matsayin wasu daga cikin dalilan da suke na boye ne, da ke haddasa hakan, ba tare da yarda da cewa hakikanin wadannan halittu ne ke haddasa su ba, a hakikatan.  Domin sanin wannan kam sai Mai duka.
Idan muka koma kan ra’ayin malaman kimiyya, ba abin da hakan zai nuna mana illa dalilan bayyane.  Babu tantama cewa za a iya samun dukkan dalilan da malaman kimiyya suka kawo a matsayin hujja, amma na bayyane.  Domin su ba su yarda da duk abin da ba a ganinsa ba, ko jinsa, ko kuma taba shi.  Amma a ka’ida ta rayuwa kuwa, idan sun yi dogon nazari, za su samu da dama cikin abubuwan da ke haddasa faruwar abubuwa ba a ganinsu.  Misali idan muka dauki “hankali”, sai mu ga wani abu ne wanda ba a ganinshi, sai dai kuma yana cikin abin da ke tafiyar da dan adam gaba daya.  To a nan, ma iya daukar hujjojin malaman kimiyya a matsayin bayyanannun dalilan da ke haddasawa.
A bangaren karshe kuma, dole ne mu yarda cewa akwai karin gishiri cikin galibin labaran da ake bayarwa.  Ba wai Farfesa Kusche kadai ba, galibin marubutan su ma sun yarda akwai wannan.  Wasu labaran ma ba su faru ba, kamar dai yadda bayanai suka gabata.  To amma kuma ba za mu dauki bangaren ra’ayin Kusche ba da ke cewa: “Babu wani abu sabo da ke faruwa a wajen.”   Samuwar hakan ne ma ya haddasa shaharar wannan bigire na duniya a kan sauran bigirori inda makamantan hakan ke faruwa.  In ba haka ba, akwai wurare da dama da ire-iren wadannan abubuwa ke faruwa, amma ba su shahara ba a duniya.  Don haka, akwai abubuwan mamaki masu faruwa, sai dai sun sha bamban da yadda ake ruwaito su.  Wannan kuma dabi’ar dan adam ce wajen ruwaito labari; da wahala ya bayar da shi yadda yake a hakikaninsa, musamman idan abu ne mai yawan maimaituwa cikin yanayin da a zahiri ya sha karfin tunaninsa.  dan adam ya gaji kambama abu, idan ya burge shi, ko ya firgitar da shi fiye da duk wani mai firgitarwa.
Har wa yau kuma babu wani tabbataccen dalili – na boye ko na fili – da aka gano cewa shi ne ke haddasa wadannan hadarurruka.  Abu na karshe da ya kamata mu sani kuma shi ne, don an kasa samun wani dalili  daya ko sama da daya da ke haddasa hakan, ba shi ke nuna cewa babu ba.  A a, watakila yanayin binciken da ake gunadarwa ne ya kasa gano hakan.  Ko dai saboda wata hikima ta Ubangiji, boyayya, ko kuma lokaci ne bai yi ba.  A dai ci gaba da zuwa rafi…!