Binciken malaman Kimiyya kan tsiribin Bamuda (3)

Ra’ayoyin Malamai Kan Tsibirin Bamuda Bayan nazari kan rubuce-rubucen da maruba ko masana suka yi kan wannan kusurwa na shedan da a Turance ake kira The Debil’s Triangle, ra’ayoyi nau’uka uku ne suka fito fili kan haka. Wadannan ra’ayoyi, idan mai karatu ya yi nazari kan su, zai ga cewa kusan kowanne daga cikinsu ya […]

Binciken malaman Kimiyya kan tsiribin Bamuda (3)
Binciken malaman Kimiyya kan tsiribin Bamuda (3)

Ra’ayoyin Malamai Kan Tsibirin Bamuda

Bayan nazari kan rubuce-rubucen da maruba ko masana suka yi kan wannan kusurwa na shedan da a Turance ake kira The Debil’s Triangle, ra’ayoyi nau’uka uku ne suka fito fili kan haka. Wadannan ra’ayoyi, idan mai karatu ya yi nazari kan su, zai ga cewa kusan kowanne daga cikinsu ya danganci abin da ke faruwa a wajen.  To amma, ganin cewa kowannensu ya rike ra’ayinsa ne a matsayin shi ne daidai, wannan ta sa muka fitar da ra’ayi gamamme da ya kumshi dukkan sauran ra’ayoyin nan guda uku, don bai wa mai karatu wata sabuwar mahanga kan wannan lamari.  A halin yanzu ga wadannan ra’ayoyi nan da muka taco, kan musabbaban da ke haddasa wadannan al’amura masu ban mamaki a Kusurwar Bamuda, ko The Bermuda Triangle.

‘Yan Al’ada da Gargajiya
Sanannen ra’ayi wanda a kanshi ne aka fara rubuce-rubuce kan wannan Tsibiri, shi ne wanda ya ke ta’allaka dalilan da ke sa jirage na bacewa ga wasu ra’ayoyi na gargajiya da al’adu.  Masu wannan ra’ayi suka ce babban abin da ke haddasa bacewar jirage bayan sulmuyarsu a cikin ruwa, ko ma a rasa inda suka shiga daga sararin samaniya ba tare da samun wata alama da ke nuna abin da ya kawo hakan ba, shi ne dayan abubuwa hudu.  Abu na farko suka ce akwai wasu halittu da ke shigowa wannan duniya daga wasu duniyoyin da ke makwabtaka da wannan duniyar da muke ciki.  Wadannan halittu da a Turance ake kira Aliens, inji masu wannan ra’ayi, su ne ke yin tasiri wajen haddasa wadannan hadarurruka masu ban al’ajabi.  Suka ce su ne masu sace jiragen suna kai su duniyarsu.  Su ne ke sulmuyar da jiragen ruwa can cikin karkashin teku, su hana masu bincike ganin buraguzansu.  Wadannan halittu, inji masu wannan ra’ayi, tabbatattu ne ba tatsuniya ba.  Domin akwai labarai da ke nuna samuwarsu a wasu sasannin Amurka, shekaru masu yawa da suka wuce.
Abu na biyu da ke haddasa hakan, a cewar masu wannan ra’ayin, su ne jinsin aljanu, ko kuma rauhanai, kamar yadda aka fi saninsu a kasar Hausa.  Suka ce bayan wadannan halittu na Aliens, su ma jinsin aljanu na da hannu wajen haddasa ire-iren hadarurrukan da labarinsu ya sha kan duniya. Sai abu na uku, wanda ya kunshi wasu halittu ko abubuwa masu ban mamaki da dan Adam ba ya iya hankalta balle ya fahimci yadda tasirinsu yake.  Suka ce wasu irin halittu ne ko abubuwa da ke yawo a sararin samaniya, lokaci-lokaci, kuma akwai tabbacin suna yin tasiri wajen haddasa hadarurrukan jiragen sama a lokuta da dama.  Wadannan halittu ko abubuwa, wadanda a Turance ake kira Unidentified Flying Objects (UFO), su ne dalilai na uku da a cewar masu wannan ra’ayi, ke haddasa wadannan hadarurruka masu ban al’ajabi.  Sai abu na hudu, wanda shi ne na karshe.
 Wannan abu kuwa, shi ake kira Paranormal.  A ka’idar ilimin kimiyya, malamai sukan kira shi: Suspension of the Laws of Physics.  Wannan yanayi wani irin tsari ne da ke nuna faruwar abubuwa, a fili, amma kuma babu wata alama ta kusa ko ta nesa da ke iya zama musabbabi kan faruwar abin.  Idan aka samu wannan yanayi, a kan kira shi Paranormal  –  ma’ana duk wani yanayin da ke haddasa abubuwa su faru, a fili ana gani, amma a kasa gane dalilin faruwarsu bayan kaddamar da binciken kimiyya a kansu, haka suke kiran yanayin.  A takaice dai sun sallama wa “dabi’a” kenan, kamar yadda sauran malaman kimiyya ke cewa.  Wannan ke nuna lamarin ya sha karfinsu.  To amma tunda ba yarda galibinsu suka yi da Allah ba, sai su kauce, su ba shi wannan suna.  To, wannan dalili na hudu, a cewar masu wannan ra’ayi, yana cikin dalilan da ke haddasa hadarurruka a wannan kusurwa ta shedanu.  Kuma ma, su suka bai wa wannan mahalli wannan suna, kamar yadda bayanai suka gabata a baya.  
Wadannan su ne kashi na farko cikin ra’ayoyi hudu da marubuta suke ganin suna da hannu wajen faruwar abubuwa a kusurwar shedanu.  Sai nau’in ra’ayi na gaba.

Malaman Kimiyya
Kafin mu yi nisa, yana da kyau mu san cewa a ka’idar bincike na kimiyya, musamman ma na zamani, ba a yarda da duk wani abin da ke haddasa faruwar abubuwa, wanda kuma ba a jinshi ko ganinshi ko iya taba shi ba.  Kuma ba a yarda da cewa ga wani abu na faruwa amma an rasa dalilin faruwarsa ba.  Wannan, a cewarsu, ba zai taba yiwuwa ba.  Da wannan, masu binciken Kimiyya kan ire-iren hadarurrukan da ke faruwa a wannan bigire na kusurwar shedan, suka ki yarda da ra’ayin malaman farko, masu ta’allaka dalilin faruwar ga jinsin aljanu ko wasu halittu masu shigowa wannan duniya tamu daga wasu duniyoyin, ko kuma wadansu halittu da ke shawagi a sararin samaniya (Unidentified Flying Objects – UFO)  ko ka’idar Paranormal ba.  Wannan, a cewarsu, duk hauragiya ce da rashin kan gado.
A nasu mahangar, malaman kimiyyar zamani suka ce akwai akalla dalilai guda biyar masu haddasa wadannan matsaloli.  Dalilan farko da na biyu su ne: yawan jiragen sama da na ruwa masu zirga-zirga tsakanin dirkokin wannan kusurwa.  Da kuma mummunar yanayin hazo ko iska ko ruwan sama, watau Terrible Weather Condition da ke samuwa a wannan wuri.   Wadannan na cikin abin da ke haddasa samuwar hadarurruka da yawan maimaituwansu lokaci-lokaci.  Da aka tambayesu kan abin da ke haddasa bacewar jiragen kuma fa?  Mun yarda yawan zirga-zirga da kuma samuwar mummunar yanayi na haddasa hadari, amma me ya sa idan aka yi hadarin, sai kuma a rasa buraguzan jirgi?  Sai suka ce dalilai na uku da na hudu da kuma na biyar ne ke haddasa bacewar wadannan jirage ko buraguzansu, har a wayi gari ba a ganinsu idan hakan ta faru.  Ga bayani kan haka filla-filla, dalla-dalla, sanka-sanka.

Za mu cigaba