Filayen Masarauta: Binciken Sanusi II zai ci gaba —Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Karbar Rashawa ta jihar za ta ci gaba da binciken tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II. Hukumar na binciken tsohon sarkin ne bisa zargin badakalar filaye na kimanin Naira biliya biyu da miliyan 200 mallakar Masarautar Kano. Tsohon sarkin ya kalubalanci […]
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Karbar Rashawa ta jihar za ta ci gaba da binciken tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Hukumar na binciken tsohon sarkin ne bisa zargin badakalar filaye na kimanin Naira biliya biyu da miliyan 200 mallakar Masarautar Kano.
Tsohon sarkin ya kalubalanci binciken hukumar a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kanon, kafin daga bisani kotun ta kori karar tasa.
“A baya mun fuskanci tsaiko sakamakon tarnakin da muka samu na shari’a kan halascin kirkiro sabbin masarautun, amma tun lokacin da muka cire tsohon sarki lamarin ya zo karshe”, in ji Ganduje.
- Sanusi ya sha kaye a kotu
- Kotu ta soke dakatar da ‘yan majalisar da ke adawa da tube Sarki Sanusi
- Gwamnatin Kano ta kara yawan ranakun fita
Kazalika ya ce gwamnatin ta fuskanci tirjiya daga wasu masu kiran kansu ‘Dattawan Kano’ kafin su ma kotu ta kori kararsu kan kirkiro masarautun, yana mai cewa yanzu ba su da wata dama ta kara kawo wa lamarin tsaiko.
Ganduje ya ce sakamakon kawo karshen dukkan wadannan shari’un, yanzu gwamnatinsa ta yi nasara ke nan a kan batun.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin amsa tambaya kan dalilin gwamnatinsa na kirkiro sabbin masarautu hudu a jihar, a zantawarsa da ‘yan jarida a fadar gwamnatin jihar ranar Litinin.
A baya dai gwaman ya sha cewa gwamnatinsa ta yanke shawarar kirkiro sabbin masarautun ne don ta fadada ci gaba zuwa dukkan sassan jihar.