Binne gawa na neman zama alkakai ga ’yan Arewa mazauna Fatakwal

Fiye da shekara 80 ’yan asalin Arewa suka mike kafa a Jihar Ribas musamman a garuruwan Ahoada da Alele da kuma Fatakwal, inda suke gudanar da addini da harkokin kasuwanci, wasu lokuta ma da auratayya a tsakaninsu da ’yan asalin jihar.Haka abin yake ci gaba da gudana a tsawon shekarun nan kwatsam sai ga shi […]

Binne gawa na neman zama alkakai ga ’yan Arewa mazauna Fatakwal

Gwamna Rotimi Amaechi na Jihar RibaFiye da shekara 80 ’yan asalin Arewa suka mike kafa a Jihar Ribas musamman a garuruwan Ahoada da Alele da kuma Fatakwal, inda suke gudanar da addini da harkokin kasuwanci, wasu lokuta ma da auratayya a tsakaninsu da ’yan asalin jihar.
Haka abin yake ci gaba da gudana a tsawon shekarun nan kwatsam sai ga shi cikin shekara 12 na mulkin dimokuradiyya ba tare da sun fuskanci wata tsangwama ko matsala ba, sai a wannan lokaci na gwamnatin Chubuike Rotimi Amaechi aka samu ribas a harkokin zamantakewa da kuma mu’amala, abin da ya haifar da shakku da yi wa juna kallo-kallo na kyama ko kyarar juna.
Babbar matsalar da ta kunno kai tsakanin ’yan Arewa mazauna Fatakwal fadar jihar wadanda akasarinsu Musulmi ne da kuma ’yan asalin jihar ita ce ta batun makabarta.  A baya Musulmi da Kirista na binne gawa ce a wuri daya, kowa da nasa bangare a babbar makabartar da ke Layin Aggerry, kwatsam sai aka wayi gari an bullo wa Musulmi da wata doka kafin su binne gawar dan uwansu a makabartar, cewa sai sun ajiye Naira dubu 10 zuwa sama, al’amarin da ’yan Arewa mazauna garin ke kokawa a kai.
Sun ce sam ba za su yarda da haka ba dama can ba a biya, amma sai aka ce musu tunda Kirista ’yan asalin jihar da baki suna biyan kudi kafin su binne gawarsu, dole su ma Musulmi su biya. Lamarin ya kai har ana tono gawar da Musulmin suka binne ana konawa alhali su Musulmin suna da tasu a Unguwar Tela Park da ke hanyar Onne.
Alhaji Musa Sa’idu mazaunin Fatakwal shi ne Shugaban kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) a shiyyar Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, ya shaida wa Aminiya ta waya yadda rikicin ya samo asali da kuma inda aka kwana. Ya ce “Hawan Gwamna Amaechi ba ma biyan kudin binne gawa, sai Shugaban karamar Hukumar Birnin Fatakwal Cif biko ya ce sai mun biya Naira dubu 15 kafin mu binne gawa. Muka je muka roke shi ya mayar da shi Naira dubu shida daga baya kuma ba a yi wata daya ba ya dawo ya ce sai mun biya Naira dubu 35. Wata rana mutanenmu sun je da gawar wata karamar yarinya za su binne sai aka turo wasu ’yan iska suka doki mutane aka jefar da gawar aka gudu.”
Shugaban na ACF ya ci gaba da cewa, “Daga baya aka je aka dauki gawar aka tafi Tirela Park aka binne, daga nan sai suka tafi makabartar suka karya kofar shiga suka tone duk wata gawar Musulmi suka kone suka sauya kofar shiga makabartar don kada wani Musulmi ya kara kawo gawa. Sai suka zuba su cikin wani kwalbati saura suka kai dakin ajiye gawarwaki.”
Wakilinmu ya tambaye shi adadin gawarwaki da suka tone suka aona sai ya ce “sun fi hamsin.”
Har ila yau ya ce wannan matsala sun koka wa Kwamishinan ’Yan sandan jihar na wancan lokaci Alhaji Mohammed Indabawa kafin aka kammala warware takaddamar aka sauya masa wurin aiki. “Kwamishina na yanzu kuma Mista Mbu ya ce in rubuto takarda a sanya hannu mu rika binne gawa da rakiyar ’yan sanda, ka ga idan a kai haka tashin hankali za a yi,”inji shi.
Ya ce ganin irin yadda ba su jituwa da Gwamna sai a ga tamkar yana daure wa ’yan Arewa gindi ne, kuma a siyasance idan ya dauki wani mataki hakan zai iya kawo tashin hankali, saboda za a yi zargin yana kuntata wa Gwamna Amaechi ne.
Game da cewa tunda ’yan Arewa suna da tasu makabartar a Tirela Park me ya sa ba za su rika tafiya can suna binne gawarsu ba, sai ya ce “Nisa da kuma kafin a kai yawan jinkiri gawa a mota matsala ce, ya sa haka.” Wakilinmu ya yi bakin kokari jin daga karamar Hukumar Birnin Fatakwal domin ta kare kanta daga zargin amma ya ci tura.