Binne gawa ta jawo takaddama a Kalaba

Binne wata gawa ya jawo cece-ku-ce a tsakanin iyalan marigayi  Okon Effiom Ekpe-Owo da Masarautar Ikot Uduak da ke Karamar Hukumar Birnin Kalaba a Jihar Kuros Riba, bayan ’ya’yan marigayin sun yi watsi da gawarsa kuma da aka haka kabari za a sanya shi ciki suka ki yarda . Hakan ya jawo surutai daga jama’ar […]

Binne gawa ta jawo takaddama a Kalaba

Binne wata gawa ya jawo cece-ku-ce a tsakanin iyalan marigayi  Okon Effiom Ekpe-Owo da Masarautar Ikot Uduak da ke Karamar Hukumar Birnin Kalaba a Jihar Kuros Riba, bayan ’ya’yan marigayin sun yi watsi da gawarsa kuma da aka haka kabari za a sanya shi ciki suka ki yarda .

Hakan ya jawo surutai daga jama’ar unguwar da sauran mutanen yankin, kan yin watsi da gawar mamacin wadda komai na iya faruwa da ita. Al’amarin ya faru ne a makon jiya.

Wakilin Aminiya wanda ya je wurin don gane wa idonsa a ranar Asabar ta makon jiya, ya ce bayan da aka dauko gawar mamacin da nufin binnewa gardama ta barke a tsakanin iyalan mamacin da masarautar kan inda ya kamata a binne shi a makabartar unguwar. Haka mahaka kabari suka koma ba tare da sun gama aikinsu ba.

Aminiya ta tuntubi Sarauniyar yankin, Madam Efio-Awan Asukuo Asibong  a fadarta ta kuma fadi hujjar da ta sanya ba za a binne Okon Ekpe-Owo ba, inda ta ce “Mutumin nan bako ne, ba dan asalin wannan yanki ba ne zuwa ya yi don haka muka ki amincewa a binne shi.”

Ta ce, shi ya sanya ma “Iyalan mamacin yau kwana bakwai ke nan suka bar min gawarsa a fadata hakan na iya zama babbar barazana ga lafiyata da ta al’ummar wannan unguwa. Mutumin nan ni na sauke shi lokacin da ya zo nan kuma babu wata shaidar da yake da ita lokacin yana raye da za ta nuna ya mallaki wuri ko fili da za a binne shi idan ya mutu. Na san dai daya daga cikin ’ya’yan mamacin ya zo ya same ni ya ce, yana son a ba shi wurin da zai binne babansa.” Ta kara da cewa, “Ni kuma na nuna musu wani fili a cikin gidan da suke na ce su haka rami su binne shi a ciki. Ya amince ya tafi ashe ban sani ba wadansu daga cikin iyalansa sun bijire wa wurin sun nuna bai yi musu ba, ba su so ba alhali ba su dawo sun ce, mini wurin da na ba su ba su so ba, kwatsam sai na samu labarin sun kawo wadansu masu hakar rami suna haka musu kabari daga bisani wani mai suna Ene ya zo, ya ce lallai su a inda bai kamata ba suke so su binne babansu,” inji ta.

Ta ce bai kamata su tubure ba balle su sake dawowa za su binne gawar a inda bai kamata ba.

Wazirin Sarauniiyar mai suna Uduak Edem  Oyoyo Etim Oyo Ita,  ya shaida wa wakilinmu cewa sakamakon watsi da gawar da suka yi har ta fara rubewa suka sanar wa Hukumar Tsabtace Birnin Kalaba da Kewaye abin da ke faruwa wadda ta gurfanar da iyalan mamacin a gaban kotu.

Ya ce babban dan mamacin an yanke masa hukuncin dauri na shekara daya ko ya biya tarar Naira dubu 40, inda ya ce yanzu haka yana tsare a gidan kurkukun  Afokang da ke Kalaba.