Birai sun kamu da cutar COVID-19 a gidan zoo

An gwada birran ne bayan masu kula da su sun ga suna tari.

Birai sun kamu da cutar COVID-19 a gidan zoo

Biran da suka kamu da COVID-19 Hoto: Aljazeera

An yi wa gwaggon biri (gorilla) da dama a gidan adana dabbobin daji (zoo) na Atlanta a Kudancin Jihar Georgia ta Amurka, inda aka gano suna dauke da cutar Kwarona.

An gwada birran ne a yammacin tekun kasar bayan masu kula da su, sun ga suna tari da sauran alamun kamuwa da cutar.

Gwaje-gwajen farko sun nuna cewa, suna dauke da kwayar cutar SARS-CoB-2 da ke haifar da cutar Kwarona, kuma mahukuntan gidan namun dajin sun fitar da wata sanarwa cewa, ana jiran sakamakon tabbatar da gwajegwajen daga Dakin Gwajin Kwayar cututtuka ta Kasar a Ames da ke Jihar Iowa.

Biran da ke cikin hadarin yaduwar cutar, ana kula da su tare yunkurin samar musu da maganin da zai taimaka wa garkuwar jikinsu, inda aka gwada kimanin birai 20 a gidan.

“Rukunin jami’an kiwon lafiya suna sa ido sosai a kan birran da abin ya shafa, kuma suna fatar za su murmure sosai. Suna samun mafi kyan kula,” inji, Babban Daraktan Kula da Lafiyar Dabbobi na Gidan Zoo na Atlanta.

“Mun damu matuka cewa, wannan cuta ta kama su, musamman ganin cewa, muna kokarin ba da kariya ga lafiya, lokacin da muke aiki tare da manyan birrai da sauran nau’o’in dabbobin da suke iya kamuwa da cutar a duk lokacin da ta kasance mai tsauri,” inji shi.

Mahukuntan gidan namun daji sun ce, sun yi imanin birran sun kamu da cutar ta dalilin wani mai kula da su ne, da ya nuna alamar kamuwa da cutar, duk da ma’aikacin ya samu cikakkiyar allurar rigakafin cutar kuma yana sanye da kayan kariya daga yada cutar.

“An gano mutane suna iya yada cutar ga dabbobi kamar birrai, kuma irin wadannan lamura sun faru a wasu gidajen namun daji, a halin yanzu babu bayanan da suke nuna ko dabbobin gidan namun daji za su iya yada cutar ga mutane,” inji mahukuntan gidan namun dajin.

Mahukuntan sun ce, masu ziyartar gidan ba su da wata barazana ta kamuwa da cutar, saboda tazarar da take tsakaninsu da dabbobin.

A bayyane yake cewa, kyanwa da karnukan cikin gidajen jama’a na iya kamuwa da cutar.