Birgimar bagararwar Baffan-rawa
Birgimar burgar buguwa Bambamin bagararwa Bani-banin bilinbituwa Bakancen baubawa Basarwar Baffan-rawa Baffan-rawa An dai daki garwa An ji dadin kwankwadar gahawa Ana ta kada kararrawa Karajin karairayi ke ta kuwwa Basajar basarwa Babbar farautar farawa Bahaushen haushin furtawa Balullubar farar kawa Balbelar fuka-fukin filfilawa Salon sunkutar salwa Sharrin sha’awar shewa Sama-saman samamen […]
Birgimar burgar buguwa
Bambamin bagararwa
Bani-banin bilinbituwa
Bakancen baubawa
Basarwar Baffan-rawa
Baffan-rawa
An dai daki garwa
An ji dadin kwankwadar gahawa
Ana ta kada kararrawa
Karajin karairayi ke ta kuwwa
Basajar basarwa
Babbar farautar farawa
Bahaushen haushin furtawa
Balullubar farar kawa
Balbelar fuka-fukin filfilawa
Salon sunkutar salwa
Sharrin sha’awar shewa
Sama-saman samamen shamuwa
Sharbar sawarmar shirwa
Surar dan tsako shaho yai shakuwa
Danbotonku ya subuto
Ku hau kan garu a kusanto
A bar batun wato-wato
Dukiyar mabarnata aka kwato
Bera da gafiya ne suka sassato
Kura ce suka kwanto
Dole ai musu kwarmato
Miyagu an rasa koto
Da an take talaka da kofato
Sai mu fasko a fahimto
Lullumin lumana za mu zamto
Kyawawan ta’adu an hakaito
Muguntar mugga an ruwaito
Rayuka su zam ceto
Mu hada karfi a firfito
’Yan rawar yanyawa
Yatsinen yamutsawa
Yari-yarin yarawa
Yangar yakicewa
Yuyuyun yagalgalewa
Karakainar karawa
Karma-karmar kwakumewa
Kumbiya-kumbiyar kundumewa
Kurbe-kurben kurbewa
Kankambar kai-kawon katantanwa
Haramben hargitsewa
Hargagin hange-hangen hangamewa
Haka-hakan haukacewa
Hutsancin hautsinewa
Hayagagar hankoron hadidiyewa
Tallace-tallacen tattalin tallatawa
Turka-turkar takurawa
Togaciyar takarkarewa
Tulelen tulun tuttulewa
Talalar tunkudewa
Dauke-dauken daddakowa
Dokin dagawa
Damarar daurewa
Dundume kururun dumamewa
Dumamen dundumewa
Motsin mutsuttuke matsabbai
Make-maken kwasar kwabbai
Tudu da kwarin kwazazzabai
Ba na kwanaren karkatar da dalibai
Sai yawan zubo jawabai
Usainin-babajo
Ka fasko masu rawar banjo
Da suka tara kudin ajo
Suka gwabje su gwarjo
Suka cutar da su Hajo
Aminai
Kar a yaudareku da aninai
Kun dai ji haushin karnai
Burinsu tara taro da nai
Dode na-mujiyar gannai
Sun sulale da sulalla
Sun ga galala
Sun dinka galleliyar galila
Sun bar talakawa na lala-lala
Sun tsala wa al’umma bulala
Ba sauran kulunboto
Ballantana su wane su karkato
Wai dukiya za su wafto
Masar al’umma saura toto
A kiyaye dai kowane loto
Na ji batun teburin mai shayi
Kowa ya hau bisa layi
Mu daina layi
Mu sha maganin laulayi
Waskiya ta sha kayi
A kula kowa-da-kowa
Mu daina kokowa
Al’umma ta daina tsiwa
Miyagu nai muku kuwwa
Daddawar adawar dawan duhuwa
Mugun yai makuwa
Maganganu yai ta jefawa
Tsigarewar tsiwa
Baba dai yai musu tsawa
A bar su sui ta tsuwwa
Nai muku kalami
A kauce wa jimami
Da salallami
Kar magabta su daure dami
A zo ai ta bambami
Mui wa knmu masalaha
Kar ai mana dararraku hahaha
Wai an samu ahaha
In komai yai arha
Sai mu ji dadin raha
‘Juma’atu babbar rana, Laraba ta-bawa ranar samu, a cewar mai bara’
Ni dai na jiyo bambamin batutuwan Baffa-rawa, inda ya tallatatsiwar tsiya-tsiya ga jam’iyyar tsintsiya ta Baban-burin-huriyya, kamar yadda aka baje mana a fuskar Amintaciyar jaridar kasar Haurobiya ta Juma’ar da ta arce, wato ranar madambaci ga watan Dashen-Baba na shekarar dubu karamin lauje da sili da tukunyar dambu. Wannan dalilin ne ya sanya darasin wannan mako ya bi kadin RUGUGIN RAWAR BAFFAN-RAWAR MAI DANBOTO DA SANDA JIRGE, musamman ma bisa yunkurinsa na sake jirga gama-garin al’ummar Haurobiya.
Akwai yiwuwar wannan makaranta ta Dodorido ta jefa azargagiyar zargi kan Baffan-rawa wajen lalata tarairaya da biyayyar masu fuka-fukin tashi, har ta kai yau babu abin da ake ta tsuwurwurtawa a birnin Shehu Mujadaddi illa TAMBELEN TUMBIN WULLI. Domin ga dukan alamu su suka rudi Gwamna gwarangwam ya tsallaka dan boton jirga talakawan kasar nan, har ma ya yi hankoron taka-karan dannin danniyar jan ragamar al’ummar kasar nan.
Ko ma dai wace irin manufa ta sanya Baffan-rawa yake ta rangajin rungumar tsiyatakun tsuke jama’a a tsukuku, domin su dajin wawurar waftar waku, mun san dai BANZA BA TA KAI ZOMO KASUWA. Ko dai Iro Mugun Madambaci ya kai wa Baffan-rawa farmaki ne? To babu mamaki matukar hakan ta kasance, tunda na ji cewa shi ma ya kwashi rabonsa, daga lalitar kasa da Samun-bom-da-sauki ya dan jinka wa jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge. Kuma sanin kowa ne damin matsabban an ware su ne don sayen na’urorin artabun ayyukan BARADEN BINDIGA, don tukarar masu haramta Bobo-da-kwambon bokoko.
Haurobiyawa idan kun ga mutum shi ba dan jinjiri ba, shi ba a cikin tawagar masu raye-raye da kade-kade ba yana ta taka rawa,ku yi kuwwa a zo a duba kwanyarsa. Kai ’yan makaranta in kun gan ni ina rawa babu gaira, ba dalili, to ku yi mini tashen KAI MALAM KA YI RAWA, ni kuwa sai in ce muku BAN YI ba!