Biri ya yi kama da mutum

A yanzu dai watan shan kunyar kungiyar Boko Haram ya tsaya, saura kadan a murkushe ta,  yayin da duniya gaba daya  ta sanya ta a gaba. An ce idan mutum na cin kasa, to ya kiyayi ta shuri, amma kungiyar Boko Haram ba ta san haka ba, domin kuwa tun tana aikata ta’asa ana kau […]

Biri ya yi kama da mutum
Biri ya yi kama da mutum

A yanzu dai watan shan kunyar kungiyar Boko Haram ya tsaya, saura kadan a murkushe ta,  yayin da duniya gaba daya  ta sanya ta a gaba. An ce idan mutum na cin kasa, to ya kiyayi ta shuri, amma kungiyar Boko Haram ba ta san haka ba, domin kuwa tun tana aikata ta’asa ana kau da kai don neman zaman lafiya, har sai da ta kai tana mari, ana kuma juya mata daya kuncin, tana dada kai marin. Amma  sa’ilin da tura ta kai bango sai ga shi nan an taru, an yunkura don tsira da mutunci ko don  ceton rai.
A yanzu dai aikace-aikacen ‘ya’yan wannan kungiyar sun wuce min-sharrin, sun kai ma-halaka, kuma an  kasa  tantance ko su wanene shugabanninta, ba kuma wanda zai iya cewa  ga iyayen gidansu,  masu daure masu gindi, daga cikin al’umman da suke mu’amala da su. Sun janyo wa lardinsu masifa, sun jefa jama’arsu cikin bakar wahala, sun kuma debo ruwan dafa kansu da kansu domin kuwa al’umman Musulmin Najeriya sun wanke musu hannu a kai, sun ce la’anarsu da kuma ta’addancinsu sun fitar da su daga jerin Musulmin duniya, kuma kowane Musulmi na jin takaicin yadda suke shafa wa Musulunci kashin kaji. Abin takaici game da haka shi ne farfagandar karya da ake yayatawa cewa kungiyar na son musuluntar da kowa da kowa a Najeriya.
Addu’ar bayin Allah don kawo karshen ta’adi da takadarancinsu ta kai su ga aika-aikar da ta sa kowa da kowa ya dukufa yakar su, musamman ma saboda yadda suka nemi zaluntar ‘yan mata sama da dari biyu da suke tozartawa a halin yanzu, kuma hakan ya sa an ja damara don faramakar su da kuma dakile dukkan hanyoyin aiwatar da ta’addancinsu.  Shi dai mara gaskiya ko a tsakiyar tafki yake sai ya yi jibi. Matsi, irin wanda ke sa gyada yin mai, ya sa wannan kungiyar fitar da hoton ‘yan matan da ta yi ikirarin sacewa. To bayan shugaban kungiyar Boko Haram da ake kira Abubakar Shekau ya ga haza, ya kuma fahimci cewa karyarsa ta kare, sai ya fitar da wani hoton bidiyo, kamar yadda ya saba yi loto-loto, wanda ke nuna wasu daga cikin ‘yan matan lullube da hijabai, cikin koshin lafiya da walwala, amma ba su da damar walawa, sai idan an cika wasu ka’idojin da ya gindaya. An ce wai daga cikin ‘yan matan da aka nuno cikin faifan bidiyon, sun takarkare suna ta tilawar Alkur’ani Mai Girma, biyu  sun musulunta, kuma za a maido sauran da ba su musulunta ba idan har za a saki  ‘yan kungiyar Boko Haram da yanzu haka ke hannun hukuma ba tare da wasu sharudda ba.
Ba za a iya cewa batan basira ce ta kai wadancan ‘yan Boko Haram din wafce wadancan ‘yan matan ba tun da farko, da saninsu ne suka aikata haka, domin su samu sukunin tsira daga harkallar da suka jefa kawunansu a ciki. Sun tsara yin amfani ne da ‘yan matan don su share hanyar tsira tare da ‘yan uwansu da aka rigaya aka danke, don kada a gane asirinsu; da ma can  hukumomin tsaro ba su bayyana wa jama’a ko su wanene wadancan mutanen da ‘yan Boko Haram din ke so a saki ba, da kuma wadanda aka ce an kashe a kwanakin baya a Abuja yayin da suka nemi su arce daga wakafin hukumar tsaro ta DSS.
Yanzu dai tusa ta kusa kare wa bodari, saura kiris a kawo karshen ta’addanci, hakan kuma zai bayar da damar fahimtar salsala da tsarin kungiyar ta’addancin da dalilan da suka sanya ta yi tasiri har ta gagari dukkan jami’an tsaron kasar nan. ‘Yan Najeriya za su daina mamakin yadda hukumomin tsaro ke kakkame wadanda suke da’awar cewa ‘yan ta’adda ne, amma kuma ba a gabatar da su a gaban kotuna, ba kuma wanda zai ce ga  kamannunsu da alakarsu da shugabannin kungiyar Boko Haram din da ake cewa suna fitar da bidiyo akai-akai. Baicin haka nan kuma ta yaya za a ce an samu irin wadannan faya-fayen bidiyon ba tare da bin diddigin tushen asalinsu ba? Idan har ta kafafen yanan gizo ake sadar da su ga jama’a, ta yaya ba a iya gane adireshin masu aiko da su, alhali kuwa ofisoshin tashoshin  sadarwa ta yanar gizo suna manyan biranen kasashen da a yanzu haka ke hakilon taimakon Najeriya gano wadancan ‘yan matan ne? Ai sun san masu shiryawa da  aikowa da su
A dukkan lokutan da aka aike da wasu hotuna ko bayanai ta yanar gizo game da ta’asar Boko Haram sai a taras cewa tushensa daga kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa ne, watau AFP. To, ta ina wannan kamfanin yake samun irin wadannan labaran idan ba yana da masaniya ne ba game da masu aikata ta’asar da kuma muhallan da suke boye? kasar Faransa dai ta yi kaurin suna a kasashen Afrika wajen tallaba da goyon bayan ayyukan ta’addanci, musamman na kwana-kwanannan  a kasashen Central Afrika da kuma Mali. Dangane da haka ne wasu ke cewa biri ya yi kama da mutum, domin kuwa ana zargin kasashen da Faransa ta raina, wadanda kuma ke makwabtaka da kusurwar Arewa-maso-Gabashin Najeriya, da assasan ta’asar da ta yi kama da ta wadancan kasashen.