Biri ya yi kisa, ya jikkata mutum 250 saboda ya rasa giya

Wani biri da ya saba yin tatul da giya ya hallaka mutum daya ya kuma jikkata 250 bayan ya nemi giya ya rasa. An yi wa akasarin mutane 250 din da birin ya ji wa rauni tiyata, wadanda yawancinsu mata ne da yara da birin dan shekara shida ya yi ta kai wa farmaki. Majiyarmu […]

Biri ya yi kisa, ya jikkata mutum 250 saboda ya rasa giya

Wani biri da ya saba yin tatul da giya ya hallaka mutum daya ya kuma jikkata 250 bayan ya nemi giya ya rasa.

An yi wa akasarin mutane 250 din da birin ya ji wa rauni tiyata, wadanda yawancinsu mata ne da yara da birin dan shekara shida ya yi ta kai wa farmaki.

Majiyarmu ta shaida cewa birin mai suna Kuala wanda kuma ba ya cin ‘ya’yan itatuwa sai nama, mallakar wani matsafi ne wanda ya kware wajen ba wa dabbobinsa barasa a yankin Uttar Pradesh na kasar Indiya.

Bayan mutuwar mai shi ne birin ya rasa giyar da zai rika sha, wanda hakan ta sa shiga gari yana kai wa mata da yara farmaki yana yakushinsu.

Da yake tabbatar da dabi’un birin da kuma abin da ya faru, wani jami’i kuma likitan dabbobi a kasar ta Indiya, Dokta Mohammed Bashir ya tabbatar da an kame birin za kuma a ci gaba da tsare shi har zuwa tsawon rayuwarsa.

“Yau kimanin shekaru uku ke nan da aka kawo mana shi mu yi ajiyarsa a gidan zoo, amma har yanzu bai sauya halayya ba, don haka za mu ci gaba tsare shi a nan har tsawon rayuwarsa”, inji shi.