Birtaniya ta amince da kirkirar jarirai daga iyaye 3

A ranar Talatar da ta gabata ne ’yan Majalisar Dokokin kasar Birtaniya suka amince da gagarumin rinjaye da kirkirar jarirai kyankyasar inji daga kwayoyin halittan mutune uku. Masana kimiyya sun ce amfani da kwayoyin halittan gado na wata mace daban da kuma na wasu iyaye biyu na iya kare yaduwar wasu cututtukan da ke bazuwa […]

Birtaniya ta amince da kirkirar jarirai daga iyaye 3
Birtaniya ta amince da kirkirar jarirai daga iyaye 3

A ranar Talatar da ta gabata ne ’yan Majalisar Dokokin kasar Birtaniya suka amince da gagarumin rinjaye da kirkirar jarirai kyankyasar inji daga kwayoyin halittan mutune uku.

Masana kimiyya sun ce amfani da kwayoyin halittan gado na wata mace daban da kuma na wasu iyaye biyu na iya kare yaduwar wasu cututtukan da ke bazuwa daga uwa zuwa da.
Wannan matakin ya sanya kasar ta zama kasa ta farko a duniya da ta halarta kimiyyar. Kuma ana sa ran cewa za a iya samun jaririn farko daga wannan hanyar zuwa badi.
Shugaban wata kungiya mai goyon bayan gwajin Mista Robert Medicrot, ya ce “babbar bukatar mu ita ce kawar da cututtukan da ake gada daga wurin uwa. Ba wai muna son kirkiran jariran musamman ba ne. Ko kuma kirkiransu domin wata manufa ta daban ba. Abin da muke buri shi ne samar da jariran da ba za su dinga samun matsala daga cututtukan gado ba,” inji shi.
kungiyon addinai a kasar sun nuna adawa da matakin saboda a cewarsu bai dace da dabi’un mutane da kuma kariya ga lafiyar dan Adam ba.
Wata mata mai suna Sharon Bernadi wacce ta rasa ’ya’yanta bakwai daga cututtukan da ke da dangantaka da na gado. Ta ce: “Lokacin da na samu labarin daukar wannan mataki, farin ciki ya lullube ni. Wannan babbar nasara ce da ta kamata kowa ya yi alfari da ita.”