Birtaniya ta cire Najeriya a jerin kasashe masu yada COVID-19

Gwamantin Birtaniya za ta janye takunkumin shiga kasarta da ta sanya wa baki daga kasashe 11.

Birtaniya ta cire Najeriya a jerin kasashe masu yada COVID-19

Gwamnatin Biritaniya ta cire sunan Najeriya daga jerin kasashen da ke barazanar yada cutar COVID-19, musamman nau’in Omicron.

Sakataren Lafiya na Birtaniya, Sajid Javid, ya bayyana cewa bullar kwayar cutar Omicron alama ce da ke nuna cewa hana tafiye-tafiye ba zai hana yaduwar sabon nau’in kwayar cutar na COVID-19 ba.

A sakamakon haka, gwamnatin Birtaniya za ta cire Najeriya da sauran kasashen da ta sanya wa bakin daga cikinsu takunkumi daga karfe 4 na yammacin ranar Laraba.

A makon jiya ne gwamantin Birtaniya da sanar da matakin da ta dauka na hana baki daga Najeriya shiga kasarta bayan an samu bullar kwayar cutar Omicron a Najeriya.