Birtaniya ta damu da zartar wa mutum 81 hukuncin kisa a Saudiyya

Gwamnatin ta ce ta damu matuka kan yadda aka kashe mutanen da yawa

Birtaniya ta damu da zartar wa mutum 81 hukuncin kisa a Saudiyya
Birtaniya ta damu da zartar wa mutum 81 hukuncin kisa a Saudiyya

Gwamnatin Birtaniya ta ce ta damu matuka kan yadda Saudiyya ta zartar wa mutum 81 hukuncin kisa.

Mai magana da yawun Fira ministan Birtaniya, ya ce tattaunawar da Saudiyya za ta diba yadda za a magance matsalar a kasuwa.

A ranar Asabar ne dai Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan mutum 81 bayan ta same su da aikata laifuka daban-daban.

Lamarin dai ya tayar da kura a tsakanin wasu kasashen, inda ake ganin hukuncin ya yi tsauri.

Ofishin Ministan Harkokin Waje ya ce gwamnatin Birtaniya ta damu da kisan, tare da jadadda adawa da zartar da hukuncin kisa a ko wane yanayi.

Gwamnatin ta kuma ce za ta tattauna yadda za ta samar da wasu hanyoyi na samar da mai bayan matsalar da yakin Rasha da Ukraine ya haifar.

Farashin fetir da direbobin Birtaniya ke saye ya kai sama da fam 1.60 a kowace lita a baya-bayan nan.

Mamayar Rasha a Ukraine ne ya haifar da tsadar farashin danyen mai da kuma tsadar fetir a Birtaniya.

Tuni kasashen yammacin turai suka ci gaba da kakabawa Rasha da Atajiranra takunkumi.

Ko a satin da ya wuce sai da gwamnatin Birtaniya ta sanya wa attajirin Rasha mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Roman Abramovich takunkumi.