Birtaniya ta gana da Iran a karon farko cikin shekara 35
A jiya Alhamis ne Firaministan Birtaniya Dabid Cameron da Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani suka yi wata zantawa a birnin New York na kasar Amurka, wadda ita ce ta farko tun bayan juyin-juya halin Iran a shekarar 1979.Ganawar tana da muhimmanci saboda yadda masana suke ganin za ta yaukaka dagantaka tsakanin kasashen biyu bayan kwashe […]
A jiya Alhamis ne Firaministan Birtaniya Dabid Cameron da Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani suka yi wata zantawa a birnin New York na kasar Amurka, wadda ita ce ta farko tun bayan juyin-juya halin Iran a shekarar 1979.
Ganawar tana da muhimmanci saboda yadda masana suke ganin za ta yaukaka dagantaka tsakanin kasashen biyu bayan kwashe tsawon lokaci ana zaman doya da manja. Birtaniya ta ce tattaunawar ta duba hanyoyin da kasar Iran za ta taimaka wajen yakar mayakan kungiyar kasar Musulunci ta (IS) da ke kasashen Iraki da Siriya. Kodayake, ba a bar kasar Iran ta halarci tattaunar da aka gudanar a birnin Paris ba, kwanakin baya, wadda ta duba yadda kasashen duniya za su hada karfi da karfe don kasar kungiyar IS. Hakazalika, kasar ba ta halarci tarukan da aka gudanar a birnin Geneba ba har karo biyu, wadanda suka duba batun hanbarar da Shugaba Bashar al-Assad na kasar Siriya.
Shugaba Rouhani ya kasance wani mai sukar kungiyar IS da kaukausar murya. Sai dai kuma yana nuna dari-dari da hari ta sama da kasar Amurka ke jagoranta a halin yanzu, wanda a cewarsa bai yi wani tanadin da ya dace ba don aike wa da dakaru ta kasa.
A nasa bangaren, Mista Cameron ya bayyana cewa “kungiyar IS wata babbar barazana ce da za a iya shawo kanta a Iraki kuma dole ne Iran sai ta janye goyon bayan da take bai wa Shugaba Assad wanda shi ne ya samar da yanayin da ta’addancin ke ci gaba da bazuwa”
Shugabannin biyu sun kuma tattauna batun makamashin Nukiliyar Iran. Har ila yau, a ranar Talatar da ta gabata , Mista Cameron ya gana da Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi. Duka tattaunawar sun gudana ne lokacin Babban Taron Zauren Majalisar dinkin Duniya na bana, da aka fara shekaranjiya, a birnin New York. Wanda ya duba rikicin kungiyar IS da rikicin kasar Ukraine da annobar Ebola da kuma matsalar Sauyin Yanayi, inda shugabannin kasashen duniya fiye da 140 suke halarta.