Birtaniya ta girke na’urorin leken asiri a Jamus – Rahoto
Takardun bayanan sirri da tsohon jami’in Hukumar saron kasa ta Amurka, Edward Snowden ya baza wa duniya, sun nuna cewa Hukumar Leken Asirin Birtaniya ta girke na’urorin leken asiri a majilisar kasar Jamus,Bundestag da kuma kusa da ofishin Shugabar kasar Jamus, kamar yadda bincike mai zaman kansa ya bayyana. Bayanan sirrin, tare da wasu hotuna […]
Takardun bayanan sirri da tsohon jami’in Hukumar saron kasa ta Amurka, Edward Snowden ya baza wa duniya, sun nuna cewa Hukumar Leken Asirin Birtaniya ta girke na’urorin leken asiri a majilisar kasar Jamus,Bundestag da kuma kusa da ofishin Shugabar kasar Jamus, kamar yadda bincike mai zaman kansa ya bayyana.
Bayanan sirrin, tare da wasu hotuna da aka dauka ta sararin samaniya, sun yi nuni da yadda aka gudanar da ayyukan leken asiri, ta hanyar amfani da na’urori da aka girke a kusa da majalisar kasar Jamus da ofishin shugaba angela Merkel; an dana na’urorin ne a saman rufin kwanon ofisoshin, kamar yadda Jaridar Birtnaiya ta bayyana.
Sai dai rahoton mai zaman kansa da aka gudanar, ya bayyana cewa leken asiri a gine-ginen ofisoshin dimokuradiyya da ake gudanarwa a daukacin fadin duniya, ana aiwatar da shi ne tare da hadin kan Amurka da muhimman kawayenta.
Cibiyoyin leken asiri a daukacin fadin Turai suna aikin hadin gweiwa ne wajen bibiyar shafukan sadarwar intanet da wayoyin tarho, a karkashin kulawar Amurka, amma gwamnatocin Turai na adawa da al’amarin, kamar yadda jaridar Guardian ta Birtaniya ta ruwaito.