Birtaniya ta kara kudin bizar dalibai da masu yawon bude ido

Hakan zai taimaka mana wajen samun karin kudin shiga.

Birtaniya ta kara kudin bizar dalibai da masu yawon bude ido

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana karin kudin bizar dalibai da ta masu yawon bude ido.

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar cikin gida ta kasar ta fitar ta ce kudin bizar ziyarar – kasa da wata shida – ya karu zuwa fan 115, yayin da na karatu zai karu zuwa fan 490.

Sanarwar ta ce karin kudin bizar zai taiamka wa gwamnati wajen samun kudin shiga.

”Karin kudin zai taimaka wa ma’aikatar cikin gida wajen samun damar aiwatar da tsare-tsaren da suka shafi batun shige da fice”, in ji sanarwar.

Matakin na zuwa ne kasa da wata shida bayan da Birtaniyar ta sanar da karin kudin bizar jinya ga marasa lafiya.