Birtaniya ta yi gwajin mota mai tuka kanta

Gwamnatin kasar Birtaniya ta gwada yiwuwar a fara amfani da mota mai sarfa kanta, bayan da aka gudanar da gwajin farko a kan tituanan kasar. Kuma ana sa ran nakasassu da tsofaffi da kananan yara za su fi cin gajiyar motar, wadda aka yi wa lakabi da “robocar,” wadda za a iya amfani da wajen […]

Birtaniya ta yi gwajin mota mai tuka kanta
Birtaniya ta yi gwajin mota mai tuka kanta

Gwamnatin kasar Birtaniya ta gwada yiwuwar a fara amfani da mota mai sarfa kanta, bayan da aka gudanar da gwajin farko a kan tituanan kasar. Kuma ana sa ran nakasassu da tsofaffi da kananan yara za su fi cin gajiyar motar, wadda aka yi wa lakabi da “robocar,” wadda za a iya amfani da wajen tura yara makaranta ba tare da dan rakiya ba.
Ministan Sufurin kasar, Claire Perry cewa ya yi, “Ina hangen wannan motar mai sarrafa kanta za a iya sanya yara a ciki, a daga musu hannu sai sun dawo daga makaranta bayan karfe uku da minti 30.”
Mutane da daman a ganin wannan motar tamkar shirin fim ne. sai dai kuma mafi yawancin dabarun kere-kere na zamani duk an cusa su a cikin wannan mota, ta yadda maganadisu da kwamfuta ke tuki da taka burki, har kuma a zabi irin yanayin gudun da ya dace a yi, bisa la’akari da yawan ababen hawa a kan titi.
Wannan mota dai an tabbbatar da cewa za ta iya sarrafa kanta cikin tsari da natsuwa, ta hanyar amfani da na’urar zuko hotuna a lokacin da take kan hanya, ta yadda za ta cusa kanta inda ya dace a tsakanin sauran ababen hawa da masu tafiya kasa da ke kewaye da ita.