Birtaniya za ta kara karfafa huldar kasuwanci da Najeriya
Firayi Ministan Birtaniya Mista Dabid Cameron ya tabbata da kasarsu za ta kara karfafa huldar kasuwanci da Najeriya. Ya bayyana hakan ne a yayin taron shekara-shekara na kasar Birtaniya kan huldar kasuwanci wanda aka gudanar a dakin taro na kueen Elizabeth Conference Centre da ke Landan a ranar Lahadi. Shugaban kungiyar ’yan Najeriya ’yan kasuwa […]
Firayi Ministan Birtaniya Mista Dabid Cameron ya tabbata da kasarsu za ta kara karfafa huldar kasuwanci da Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a yayin taron shekara-shekara na kasar Birtaniya kan huldar kasuwanci wanda aka gudanar a dakin taro na kueen Elizabeth Conference Centre da ke Landan a ranar Lahadi.
Shugaban kungiyar ’yan Najeriya ’yan kasuwa a Birtaniya (NBCC) Mista Adeyemi Adefulu cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce sun yaba da matakin da Cameron ya ce kasarsu za ta dauka dangane da batun kara karfafa huldar kasuwanci tsakaninsu da Najeriya.
Ya ce Cameron ya kara jaddada batun ne sakamakon wata yarjejeniya tsakanin Shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma Firayi Ministan Birtaniya a shekarar 2010 don kara huldar cinikayya tsakanin kasashen biyu. A cikin yarjejeniyar sun amince za a kara kudin cinikayya tsakanin kasashen daga Fam biliyan 4 zuwa 8 daga shekarar 2010 zuwa 2014.
Cameron ya ce saboda yadda abubuwa suka gudana ne ake sa ran ci gaba da huldar cinikayyar zuwa nan da shekara biyar mai zuwa.
“Bunkasa kasuwanci tsakanin kasashe biyu ba zai yiwu ba, ba tare da an mayar da hankali sosai ba, sannan dole sai an rika tunanin hanyoyin da za su bunkasa cinikayya tsakanin kasashen.” Inji Cameron.
kasashen biyu sun fara sanya hannu a yarjejeniyar huldar kasuwanci ne a shekarar 1977, inda suka gudanar abubuwa masu yawa ciki har da zuba hannayen jari da karfafa cinikayya da sauransu.
A yanzu kasashen sun mayar da hankali ne wajen kai kayayyaki wadanda ba su shafi mai ba zuwa kasuwannin Birtaniya.