Birtaniya za ta sake bude ofishin jakadancinta a Iran

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya William Hague ya ce Birtaniya za ta kara bude ofishin jakadancinta da ke birnin Tehran, shekara biyu bayan ya kasance a  rufe.Wannan matakin yana zuwa ne a lokacin da kasashen Yamma suka fara tattaunawa da Iran kan ci gaba da gumurzun da ake yi a kasar Iraki mai makwabtaka da ita. […]

Birtaniya za ta sake bude ofishin jakadancinta a Iran
Birtaniya za ta sake bude ofishin jakadancinta a Iran

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya William Hague ya ce Birtaniya za ta kara bude ofishin jakadancinta da ke birnin Tehran, shekara biyu bayan ya kasance a  rufe.
Wannan matakin yana zuwa ne a lokacin da kasashen Yamma suka fara tattaunawa da Iran kan ci gaba da gumurzun da ake yi a kasar Iraki mai makwabtaka da ita. A fatan ganin yadda kasashen za su hada gwiwa a karon farko don yakar masu kishin Islama na kungiyar ISIS wadanda suke ci gaba da tada zaune tsaye a kasar ta Iraki, kuma suke barazana ga baki dayan yankin.
Sakataren ya shaida da wa zauren majalisar dokakin Birtaniya matakin ne cikin wata takarda da ya aika ma ta, wadda a cikinta ya ce: “A yanzu dalili da yanayin da ake ciki, ya dace mu sake bude ofishin jakadancinmu da ke birnin Tehran. Amma akwai wasu tattauna da za mu cimma kafin faruwar hakan.” Inji shi.
Sai dai a bayanan nasa bai ce komai ba game da halin da ake ciki a kasar Iraki, amma kuma akwai lokacin da ya bayyana cewa Iran din na da matukar mahimmamci wajen samar da tsaro a yankin.
Birtaniya ta rufe ofishin jakadancinta a Tehran  a shekarar 2011, bayan da wasu mutane suka ta da yamutsi a can. Wanda ya yi sanadiyyar dakatar da duk wata hulda ta jakadanci  tsakanin kasashen biyu.
Firaministan Irakin Nouri al-Maliki dan Shi’a ne wanda kuma ake wa kallon na kusa ne da gwamnatin Iran.
A wani mataki na shawo kan rikicin da kungiyar ISIS take jagoranta, a ranar Talatar da ta gabata, firaministan ya bayyana sallamar manyan hafsoshin sojin kasar hudu, ciki harda Kwamandan lardin Ninebeh. Ya kuma umarci gabatar da su a gaban kotun soji bisa laifin kaurace wa aiki.
Wannan na zuwa ne mako guda bayan birnin Mosul ya fada hannun mayakan ISIS.