Bishiya mai shekara 100 ta yi ajalin mutum 4 a Oyo
Bishiyar ta fado musu sakamakon mamakon ruwan sama da tsawa da aka tafka.
Akalla mutum hudu ne ake fargabar sun rasu bayan wata tsohuwar bishiya da wata bishiya mai kimani shekara 100 ta fado musu sakamakon tsawa a Jihar Oyo a ranar Litinin.
Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewar tsohuwar bishiyar da ta shafe tsawon shekaru a kusa da kasuwar Sabo a garin Ibadan, ta fadi ne sakamakon mamakon ruwan sama da tsawa da aka yi.
-
- NAFDAC ta gargadi ’yan Najeriya kan cin kajin da aka yi fasa-kwaurinsu
-
Domin sauke shirin latsa <a
Alhaji Akeebu Alarape, shugaban kasuwar Sabo ya tabbatarwa da NAN faruwar lamarin, inda ya ce bishiyar ta kai kimanin shekara 100 a duniya.
Alarape, ya shaida cewar an kira masu saran bishiya da dama don su sare ta tare da ceto mutanen da ta danne.
Wata ’yar kasuwa a yankin, Misis Kareemot Ejide, ta ce tun da ta taso ta san bishiyar a wannan yankin.
Shugaban jami’an tsaro na Amotekun na Karamar Hukumar Atiba, Mista Akeem Ojo, ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 6:00 na yammancin ranar Litinin.
“Wata dalibar Kwalejin Oyo, sai wata mata da ’yarta tare da wani yaro aka ciro a karkashin bishiyar.
“Mutum daya ya samu mummanan rauni, kuma tuni aka garzaya da shi wani asibiti don ba shi agajin gaggawa,” cewar Ojo.
Kazalika, ya ce zuwan jami’an Amotekun wurin ya taimaka wajen hana mutane yashe kayan ’yan kasuwar da ke wajen bayan faruwar lamarin.
Shi ma Mista Seun Oguntona, Shugaban Karamar Hukumar Saaro ya tabbatarwa da NAN faruwar lamarin.