Bishop din Katolika masu tsaurin ra’ayi sun yi fatali da sassauta wa ’yan luwadi
Kwana daya bayan da wasu Bishop-Bishop cocin Katolika suka mika bukatar cocin ya rungumi ’yan luwadi da madigo tare da yin sassauci kan sakin aure, limaman cocin masu tsattsauran ra’ayi sun fito a ranar Talata sun mayar da martani mai zafi tare da bayyana cewa hakan cin fuskar koyarawr cocin ne, kuma “Ba haka muka […]
Kwana daya bayan da wasu Bishop-Bishop cocin Katolika suka mika bukatar cocin ya rungumi ’yan luwadi da madigo tare da yin sassauci kan sakin aure, limaman cocin masu tsattsauran ra’ayi sun fito a ranar Talata sun mayar da martani mai zafi tare da bayyana cewa hakan cin fuskar koyarawr cocin ne, kuma “Ba haka muka ce ba kwata-kwata.”
Bayan saki takardar bukatar haka a ranar Litinin mai dauke da bayanan sassauci kamar cewa “maraba da masu luwadi,” Kadina na cocin a Amurka, Raymond Burke da takwaransa na Jamus, Gerhard Mueller sun yi korafin cewa kafafen watsa labarai sun nuna son kai kan muhawarar da Bishop-Bishop din suka.
“Ina jin an murguda labaran da aka bayar inda aka karkata ga ra’ayi daya kawai maimako ruwaito ra’ayoyin mabiya addini,” inji Burke a wata hira da ya yi da wata jaridar Italiya mai tsaurin ra’ayi da ke fitowa kullum mai suna II Foglio.
“Wannan ya bata min rai matuka, saboda mafi yawan Bishop-Bishop ba su yarda da wannan shawara ba, ’yan kalilan ne kawai suka san wannan.”
A wata tattauna a ranar Talata da jaridar Catholic World Report da ake bugawa a Amurka, Burke ya ce, Bishop-Bishop “Ba za su amince da” kowane canji ba, saboda ba su da wata madogara a Littafi Mai tsarki ko koyarwar coci.
A ranar Litinin ne wani daftari da Bishop-Bishop din cocin Katolika kusan 200 wadanda suka halarci wani taron sake nazarin darussan da cocin ke koyarwa domin iyalai, ya bukaci cocin ya sassauta matsayinsa na kyamar ’yan luwadi.
Takaitaccen bayanin da Kadinan cocin na kasar Hungary Peter Erdo ya gabatar wa kafafen watsa labarai ya jawo daga jijiyar wuya daga masu tsaurin ra’ayi kan yadda shi da abokansa suka fassara ra’ayoyin daaka gabatar a taron limaman cocin.
Kuma domin magance barakar da bayanin ka iya haifarwa Kakakin Fadar batikan, Rabaran Federico Lombardi ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa, “Wannan takardar shawara ce kawai, amma ba a cimma matsaya a kanta ba.”
Sakataren musamman na taron Bishop-Bishop din, Monsignor Bruno Forte, ya ce dole ne cocin ya mutunta ’yan luwadi da madigo. Sai dai ya ce har yanzu akwai cece-kuce da ake yi game da kalaman da aka yi amfani da su a daftarin.