Bishop Lamido ya koka kan rashin aikin yi a tsakanin matasa

Bishop din Wusasa da ke Zariya Rabaran Dokta Ali Buba Lamido ya koka kan karuwar rashin aikin yi a tsakanin matasa, inda ya ce bayanai sun nuna akwi matasa fiye da miliyan 48 da ba su da aikin yi a kasar nan.Rabaran Ali Buba Lamido ya bayyana haka ne a wajen taron da cocin Angalikan […]

Bishop Lamido ya koka kan rashin aikin yi a tsakanin matasa
Bishop Lamido ya koka kan rashin aikin yi a tsakanin matasa

Bishop din Wusasa da ke Zariya Rabaran Dokta Ali Buba Lamido ya koka kan karuwar rashin aikin yi a tsakanin matasa, inda ya ce bayanai sun nuna akwi matasa fiye da miliyan 48 da ba su da aikin yi a kasar nan.
Rabaran Ali Buba Lamido ya bayyana haka ne a wajen taron da cocin Angalikan ya gudanar na bana a Wusasa, inda ya ce abu ne mai karya gwiwa a ji cewa akwai matasa miliyan 48 ’yan Majeriya da ba su da aikin yi, “Muna sane da cewa gwamnati ba za ta iya samar wa mutum miliyan 48 aiki ba, to amma wadansu daga cikin matasan suna iya yin komai don su rayu, don haka akwai bukatar gwamnati ta samar da yanayi mafi dacewa domin hada hannu a kawar da matsalar ta rashin aikin yi a tsakanin matasa. Akwai bukatar mu kawo matasa da yawa cikin aikin gona da kasuwanci da gina gidaje da komfanoni da sauransu. Dole ne gwamnatin Najeriya ta samar da guraben da za su kawo hanyar kasuwanci da sauri, muddin ba so muke abin takaicin da ya fi na Boko Haram ya hallaka mu ba,” inji shi.
Bishop din ya ce lokacin dogaro da mai kadai ya wuce, musamman a wannan lokaci da Majalisar dinkin Duniya ta ce Najeriya ce take da mafi yawan yaran da ba su zuwa makaranta. “Wannan yana da matukar hadari ga kasarmu, ba matasa ilimi shi ne abin da kowace al’umma ta fi ba fifiko,” inji shi.
Sai dai ya yaba wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan kokarinta na yaki da cin hanci da rashawa, ya ce tunda aka rantsar da gwamnatin a bara ta nuna da gaske take a kan yaki da wannan mugun hali duk da cewa mun lura har yanzu ba a hukunta mutanen da aka kama ba.
Ya roki Shugaban kasa da majalisarsa su ci gaba da wannan aiki kada su yarda da masu shisshigi. “Muna ganin matsalolin Najeriya ba su da iyaka a lokacin da gwamnati take kokarin magance matsala a wani bangare, sai wata ta taso, don haka muna ba gwamnati shawara ta yaki masu fasa bututun mai da ke komar da tattalin arzikin kasarmu baya, kuma a dauke su a matsayin ’yan ta’adda, kuma a samar da hukumar tsaro ta musamman don ta kula da wannan bangare.