Bishop Mamza ga Buhari: Kada ka nada ’yan PDP da suka nutsar da gwamnatin Jonathan a mukami
Bishop din cocin Katolika na Yola, Dokta Stephen Mamza, ya shawarci zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa kada ya nada duk wanda bai cikin Jam’iyyar APC kasa da shekara uku a gwamnatinsa, inda ya ce ’yan PDP da suka koma APC a baya-bayan nan na iya lalata gwamnatin. Limamin Kiristan ya bayyana haka ne a […]
Bishop din cocin Katolika na Yola, Dokta Stephen Mamza, ya shawarci zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa kada ya nada duk wanda bai cikin Jam’iyyar APC kasa da shekara uku a gwamnatinsa, inda ya ce ’yan PDP da suka koma APC a baya-bayan nan na iya lalata gwamnatin.
Limamin Kiristan ya bayyana haka ne a hudubar da ya gabatar a cocin St. Augustine’s Catholic Church da ke Bekaji, Yola, inda ya ce wadannan ’yan siyasa da ke barin PDP jama’a-jama’a zuwa APC sun nuna wa duniya abin da za su samu ne kawai damuwarsu ba abin da za su yi wa jama’a ba.
“Babbar shawarata ga zababben Shugaban kasa ita ce kada ya nada ko daya daga cikin wadanda ba su kasance a APC na tsawon shekara uku ba a kowane mukami. Wannan zai taimaka masa ya gina gwamnatin da za ta kafu kan manufar APC, amma idan ya yi kuskuren garwaya gwamnatinsa da ’yan PDP zai ba wadanda suka zabe shi kunya.”
Bishop Mamza ya kara da cewa: “Idan wadannan ’yan PDP da suke gudu zuwa APC masu gaskiya ne kuma suna son dimokuradiyya to su zauna a jam’iyyarsu su sake yi mata fasali don tunkarar zabe nag aba. Amma rige-rigen komawa APC ya tabbatar da cewa suna yin siyasa ne kawai don bukatunsu na son zuciya amma ba domin ci gaban kasar nan ba. Ina girmama ’yan PDP da suka ci gaba da zama a cikinta, su ne ’yan dimokuradiyya na hakika a kasar nan.”
Bishop Mamza ya ce wadanda suka bar PDP sun ci amanar tsohuwar jam’iyyar tasu a zaben da ya gabata inda jam’iyyar ta sha kasa a hannun APC.
Dokta Mamza, ya ce ’yan PDP da suke komawa APC babbar barazana ga gwamnatin Buhari domin ba suna komawa jam’iyyar ba ce don taimaka wa gwamnatin Buhari ba, sai don su nutsar da jam’iyyar irin yadda suka nutsar da gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan.