Bishop ya fadi matacce bayan ya yi ikirarin zina a cocinsa
Wani Bishop a birnin Connecticut na kasar Amurka, Bishop Boddy Dabis ya yi ikirarin zina da wata mace a gaban taron mabiya cocinsa, inda kuma ya yanke jiki ya fadi matacce, a wani abu da ake ganin bugawar zuciya ce a ranar Lahadin nan.Jaridar The Connecticut Post, wadda ta ruwaito labarin, ta ce ’yan sanda […]
Wani Bishop a birnin Connecticut na kasar Amurka, Bishop Boddy Dabis ya yi ikirarin zina da wata mace a gaban taron mabiya cocinsa, inda kuma ya yanke jiki ya fadi matacce, a wani abu da ake ganin bugawar zuciya ce a ranar Lahadin nan.
Jaridar The Connecticut Post, wadda ta ruwaito labarin, ta ce ’yan sanda suna binciken lamarin. Akwai bayanan da suke cewa Bishop din ya hadu da muguwar bugawar zuciya ce bayan ya hadu da mabambanta ra’ayi bayan ikirarin.
Shi ne ya kafa cocin Miracle Faith World Outreach Church a garin Bridgeport –wanda aka kafa a 1967.
“Muna ihun cewa mun yafe ka, muna sonka, -amma ina- zuciyarsa ta buga, inda ya mutu a gabanmu,” wata mai bauta a cocin mai suna Judy Stoball ta shaida wa jaridar. Ta kara da cewa, “Na rike kansa a lokacin da ya fadi a kasa…Cocinmu yanzu haka yana cike da bakin ciki.”
An tabbatar da mutuwar Bishop Dabis a asibitin Bridgeport. Sai dai ana ci gaba da bincike kan musabbabin mutuwar kamar yadda majiyar ’yan sanda ta shaida wa jaridar.
Sai dai wani mamban cocin da ba a bayyana sunansa ba, ya shaida wa jaridar Christian Post cewa, ba niyyar Dabis ce ya zo gaban jama’a don wanke kansa ba. Mamban ya ce da farko ya yi ikirari ga matarsa kuma ita ce ta matsa sai ya shaida wa daukacin mahalarta cocin. Kuma ikirarin ya tayar da hankalin ’ya’yan Bishop Dabis, wadanda “suka fara doke-doke,” inji jaridar.