‘Biyafara bankaura ce’ (1)

Minista mai kula da samar da ayyukan yi.”Sanarwar ta kara da cewa: “Tarihi ya nuna cewa zai fi alfanu a zauna a tattauna maimakon daukar makami. Tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa, kuma muna kokarin yin haka a sassan kasar nan.”Ya ce, wajibi ne ’yan kabilar Ibo su zamo masu lura a gwagwarmayarsu, domin akwai […]

‘Biyafara bankaura ce’ (1)

Minista mai kula da samar da ayyukan yi.”
Sanarwar ta kara da cewa: “Tarihi ya nuna cewa zai fi alfanu a zauna a tattauna maimakon daukar makami. Tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa, kuma muna kokarin yin haka a sassan kasar nan.”
Ya ce, wajibi ne ’yan kabilar Ibo su zamo masu lura a gwagwarmayarsu, domin akwai hujjojin da suka nuna suna daga cikin wadanda za su fi cin gajiyar manufar rayawa da cin gaban kasa na Shugaba Buhari.
“Bai kamata mu rika manta tarihi ba, mu yi tawaye a daidai lokacin da za a ’yantar da mu. Mu yi tunani wannan lokaci  bai dace a tado batun ’yancin Biyafara ba, saboda Shugaba Buhari ya yi alkawarin gyara hanyoyin Gwamnatin Tarayya da suka lalace a yankin Kudu maso Gabas tare da farfado da hakar kwal a Enugu da aikin gadar Neja ta Biyu da sauran gine-gine. Kuma Shugaban kasa mutum ne mai fada da cikawa. Kuma idan aka lura bayan ya gama zangonsa na biyu yankin Kudu maso Gabas na kabilar Ibo ne za su samar da Shugaban kasa.”
Jam’iyyar ta ce me ya sa wannan gwagwarmaya ta masu neman kasar Biyafara ba ta kankama sosai a shekara 16 na mulkin Jam’iyyar PDP da ’yan kabilar Ibo suka ba ta cikakken goyon baya ba tare da ta yi musu sakayya ba? Shin hakan ba ya nufin masu azalzala wannan zanga-zanga ba su ga laifin danmu Shugaba Goodluck Jonathan da ya bari hanyoyin tarayya suka yi matukar lalacewa a Kudu maso Gabas, kuma ya kasa bayar da kwangilar aikin gadar Neja ta Biyu kamar gadar Owete kuma ya gaza inganta hakar kwal na Enugu?”
Jam’iyyar APC ta shiyyar ta kara da cewa: “Shaidu sun nuna  cewa masu azalzala tawayen mutane ne da ake zargi da aikata laifuffuka, kuma ba su nemi ra’ayin galibin ’yan kabilar Ibo a yankin ba ko a Dutse da ke Jihar Jigawa ko Akure a Ondo ko Oron a Akwa Ibom ko Ibon da suke Legas da Kano da Abuja ba.”
‘Ba ruwanmu da ku’
kabilun da suka fito daga yankin Kudu maso Kudu sun ce ba ruwansu da bukatar da ’yan kabilar Ibo ke yi na neman kafa kasar Biyafara, inda suka nemi masu gwagwarmayar su fice daga yankunansu.
Wannan mataki yana zuwa a daidai lokacin da gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas suka kira taron gaggawa na shugabannin Ibo don tattauna ci gaba da zanga-zangar da MASSOB da IPOB ke gudanarwa a yankin.
Mutanen Kudu maso Kudun sun fadi a takardar bayan taron da suka gudanar a Uyo fadar Jihar Akwa Ibom a karkashin Sarkin Ibibio Obong Dokta EU Ekidem, Ntisong Ibibio III, cewa ba ruwan yankin Kudu maso Kudu daga neman ‘kasar ta Biyafara.’
Wakilan kabilun Ibibio da Efik da Anang da Ijaw da Itsekiri da Urhobo da Ikwerre da Oro da Isoko da sauransu da suka halarci taron, ciki har da shugaban riko, Ekidem da wanda ya shirya taron kuma Sakataren Shugabannin kabilar Itsekiri a Jihar Delta, Barista Edward Ekpoko da Albert Akpomudje, SAN (na Urhobo) da Shugaban Ogbakor- Ikwerre a Jihar Ribas, Farfesa A.M Onyeozu da sauransu, sun ce ba za su bar ko da taki daya na kasarsu ya kasance a kasar ta Biyafara da ake mafarki ba.
Sun bukaci gwamnoni da shugabannin siyasa da sarakunan yankin Kudu maso Gabas su fito su yi magana, domin yin shirunsu na jawo matsala. “Mun kadu da yadda Ibo wadanda suka dawo Najeriya bayan faduwar Biyafara a ranar 15 ga Janairun 1970 cike da damuwa da bakin ciki, yanzu za su dawo suna batun Biyafara… mun yi imani da kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya kuma za mu  yi   amfani da dukkan karfinmu wajen kare hadin kan Najeriya.
A taron gwamnonin yankin Gabas sun yi kira da a zauna lafiya, kamar yadda yake kunshe a takardar bayan taron da Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha ya karanta a gidan gwamnatin Enugu a ranar Talatar da ta gabata.
Gwamnonin sun yanke shawarar tuntubar shugabannin Ibo da sarakunan yankin da kungiyoyin ci gaba da shugabannin addini da sauransu, don nemo hanyar tabbatar da zaman lafiya a yankin, inda za su sake gudanar da wani taro a jibi Lahadi a Enugu tare da’yan Majalisar Tarayya da ministocin da suka fito daga yankin da sauransu.
Sun shawarci MASSOB da IPOB su bi hanyar lumana, domin ita kadai ce za ta kawo ci gaba ga yankin.

Yan Arewa da dama sun tsorata – Liman
A birnin Aba na Jihar Abiya, Aminiya ta tuntubi limamin masallacin Jumma’a na garin, Alhaji Idris Bashir, inda ya ce, da farko ’yan Arewa da dama mazauna birnin sun tsorata da batun zanga-zangar ta magoya bayan Biyafara, har ma wasu sun koma gida Arewa, amma daga baya da suka ga ba wata matsala, sai suka koma.  Kuma yanzu haka ba sa zaman dar-dar.
“Ya zuwa yanzu dai babu labarin an kai hari ga wani dan Arewa a nan Aba, tun da matasan suka fara zanga-zangar tasu,” a cewar Imam Idris Bashir.
Malamin Musuluncin ya ce ci gaba da  cewa,tsare daraktan haramtaccen gidan rediyon Biyafara, Nnamdi Kanu, wata babbar barazana ce, ba wai ga ’yan Arewa mazauna yankin Kudu maso Gabas kadai ba, har ma ga ita kanta Gwamnatin Tarayya. Saboda yadda matasan Ibo za su iya harzuka, su tayar da kayar baya. “A yanzu ma haka, ’yan kasuwa da yawa da suka saba zuwa daga Arewa, su sari kaya a kasuwannin Aba sun ragu matuka, saboda tsoron mai yiwuwa zanga-zangar ta haifar da wata matsala,” inji shi.
A Anaca Jihar Anambra, kusan haka abin yake. Domin kuwa Alhaji Tanimu Ibrahim Lakwaja, daya daga cikin shugabnnin ’yan Arewa mazauna birnin ya shaida wa Aminiya, cewa yanzu haka suna nan zaune lami lafiya a birnin. “Ba mu ga wata barazana ba, kuma jama’armu ba su yi kaura ba, domin ba wanda ya tayar mana da hankali,” inji shi.
Hasali ma dai, inji dan kasuwan, Gwamnan Jihar Anambra, Cif Willy Obiano ya tanadi matakan tsaro, don magance barkewar duk wata tashin-tashina a sanadiyyar zanga-zangar ta magoya bayan Biyafara. “Gwamnan ya kwantar mana da hankali, cewa kada kowa ya ji tsoro. An ma baza jami’an tsaro cikin shirin ko-ta-kwana, suna ta gudanar da sintiri a sasan birnin,” inji shi.
Shi kuwa Basaraken garin Ibagwa Nike a karamar Hukumar Enugu ta Gabas, Igwe Emannuel Ugwu, tabbaci ya bayar cewa, su ma sarakunan gargajiya da sauran shugabannin al’umma, suna kokarin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyoyi daban-daban. Domin kada jerin zanga-zangar da matasan na Ibo suke gudanarwa su kawo wata baraka a tsakanin jama’a.
Sai dai basaraken ya ce, akwai bukatar a kara wa sarakunan gargajiya iko a hukumance, ta yadda za su fi bayar da gudunmawa ta fuskar sha’anin tsaro. Domin sun fi kusa da jama’a, kuma sun san mutanen da ke masarautunsu.  

‘Mu Ibon Kano ba mu goyon bayan yunkurin’
Sarkin ’yan kabilar Ibo na Jihar Kano Igwe Boniface Ibekwe (Ide I), ya ce masarautarsa ba ta goyon bayan kirayen-kirayen da wasu kungiyoyin MASSOB da IPOB ke yi a yankn Kudu maso Gabas na neman ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biyafara.
Dokta Boniface Ibekwe, ya shaida wa Aminiya cewa jama’arsa suna zaune lafiya a Jihar Kano tare da gudanar da harkokin kasuwancinsu ba tare da samun matsala ba. “Ba ma goyon bayan wannan fafutika da mutanenmu ke yi a can Gabas. kabilar Ibo mutane ne masu son zaman lafiya da a kullum suke kokarin ganin kasar nan ta ci gaba da kasancewa kasa daya. Mun dauki kanmu uwa daya uba daya mu da mutanen Arewa. Muna samun goyon baya da taimako daga Sarkin Kano da gwamnatin Jihar Kano. A yanzu haka idan aka duba za a ga mutanenmu suna ta gine-gine a jihar, kasancewar sun yi amanna da cewa dukkanmu ’yan kasa daya ne,” inji shi.
Sarkin na kabilar Ibo ya yi kira ga shugabannin da ke yankin Gabas su riki Hausawan da ke can a matsayin ’yan uwa ta yadda za su ji cewa tamkar suna zaune a Arewa ne.
Sai dai Sarkin na Ibo ya ce: “Ina kira ga Gwamnatin Tarayya ta kira masu zanga-zangar ta zauna da su don ta san hakikanin abin da suke nema, kuma hakan ya ba ta damar sanin hanyar da za ta bi ta magance matsalar. Kowa a cikinmu shaida ne game da yadda aka fara Boko Haram a kasar nan. Da a ce tun farko gwamnati ta saurari wadancan mutane, to da abin da ya faru bai kai ga haka ba. Ta dalilin Boko Haram mun yi asarar mutane da dukiyoyin da ba za mu iya lissafawa ba. Shi ya sa nake yaba wa marigayi Shugaban kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa kan abin da ya yi wa ’yan ta’addan Neja-Delta. Babu shakka ya nuna cewa shi shugaba ne.”
Sarkin ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tsayin daka wajen ganin shugabannin yankin Gabas suna yin amfani da kason da ake ware musu don gudanar da ayyukan raya kasa a yankunansu, saboda yawancin shugabannin sukan karkatar da kudin ne ga amfanin kansu.  “Idan aka je Kudu maso Gabas babu wasu ayyukan ci gaba da za a iya nunawa. Duk tituna sun lalace, mutane ba su samun kyakkyawar kulawa ga lafiyarsu ga uwa-uba rashin aikin yi da sauransu,” inji shi.
Sarkin na Ibo ya ce mafi yawan wadanda ke kiraye-kirayen kafa kasar Biyafara a yanzu ba su san zafin yaki ba. “Mafi yawan matasan ba su san lokacin da aka yi Yakin Basasa ba, shi ya sa suke wannan abu. Yaki babu kyau. A lokacin Yakin Basasa an kashe mana mutane, mun yi asarar dukiyoyinmu. Don haka ba mu son duk wani abu da zai sake jefa kasar nan a cikin yaki. Burinmu shi ne mu ci gaba da zama a matsayin kasa daya tare da fatan ganin mun cicciba kasarmu ta yadda za ta samu ci gaba ta yi gogayya da takwarorinta a duniya,” inji shi.
Sai ya yi kira ga matasan su bi hanyar da ta dace wajen sanar da gwamnati matsalolinsu da kuma abin da suke nema ta yi musu, amma ba ta hanyar rigima ba, don guje wa abin da hakan ka iya haifarwa.  “Ina kira ga wadannan jama’a su san cewa ba a samun biyan bukata ta hanyar tashin hankali. Don haka ku bi a hankali,” inji Sarkin Ibon.
Kame daraktan haramtaccen gidan rediyon Biyafara, Nwannekaenyi Kenny Okwu-Kanu wanda ake wa lakabi da Nnamdi Kanu ya sa aka gano wata kwantaina shake da kayan aiki a kauyensu da ke Umuahiya ta Arewa da ke Jihar Abiya a watan jiya.
Rahotannin sirri sun ce gidan rediyon ya kaddamar da gidauniyar neman kudi shekara biyu da suka gabata, inda aka tara Dala dubu 100 (kimanin Naira miliyan 20) don sayowa da shigo da wadannan na’urori daga Turai don yada farfaganda a sassan kasar nan.
An zargi gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, wadda ita ma aka yi zargin  ta kashe kusan Dala biliyan daya wajen yakar Arewa da nuna mata kiyayya da kamfe din kabilanci, da cewa ita ta daure wa gidan rediyon gindi tare da karfafa masa gwiwa wajen yada kamfe din kiyayya. An zargin gwamnatin Jonathan da kyale Nnamdi Kanu ya shigo da kayan watsa labaran ciki har da watta babbar na’urar watsa labarai da Hukumar SSS ta gano bayan kama Nnamdi Kanu ranar 14 ga Oktoban bana.
Ana ci gaba da tsare Nnamdi Kanu kan zarginsa da cin amanar kasa da tawaye da barazana ga zaman lafiyar kasa. Kuma an zarge shi da shigo da bindigogi da harsasai don kashe ’yan Najeriya a wani faifan bidiyo da ya fitar, kuma ‘’yan sandan Imo suka ayyana nemansa  ruwa a jallo a watan Maris kan alakarsa da wasu fastoci da suke safarar bindigogi kirar AK 47 da sauran miyagun makamai.