Biyafara: Ya kamata ’yan Arewa su farka – Ado Ɗansudu
Biyo bayan nasarar da rundunar sojin Nigeriya ta yi wajen kwantar da ƙurar da tsagerun ƙungiyar nan mai rajin kafa ƙasar Biyafara ta IPOB, al’umma da dama suna tofa albarkacin bakinsu. Inda Alhaji Ado Shu’aibu Ɗansudu Shugaban ƙungiyar tuntuɓar juna ta ’yan Arewa ya bayyana takaicinsa dangane da yunkurin ’yan ƙungiyar ta IPOB, ya ce […]
Biyo bayan nasarar da rundunar sojin Nigeriya ta yi wajen kwantar da ƙurar da tsagerun ƙungiyar nan mai rajin kafa ƙasar Biyafara ta IPOB, al’umma da dama suna tofa albarkacin bakinsu. Inda Alhaji Ado Shu’aibu Ɗansudu Shugaban ƙungiyar tuntuɓar juna ta ’yan Arewa ya bayyana takaicinsa dangane da yunkurin ’yan ƙungiyar ta IPOB, ya ce abin takaici ne yadda aka ƙyale ’yan tsagerun tun daga fari. “Domin idan ka lura za ka gane al’ummar Ibo da ke jihar Kano kaɗai sun fi ‘yan Arewacin Najeriya da ke zau ne a jihohin Kudu Maso Gabas kaf ɗinsu, kuma ita wannan Biyafarar mene ne manufarta a yanzu? Mene ne ma’anarta? Abin da Kalmar Bifara ke nufi a ma’anance shi ne, ‘zo ka tsir,’ to wacce tsira suke nema bayan sun mamaye ko’ina? Kuma tun a wanccan lokacin da aka kammala yaƙin Basasa ai waɗanda suka jagoranci wannan yunƙuri da farko sun saduda sun tuba sun yarda da tafiyar da ƙasar nan a matsayinta na ƙasa ɗaya, don haka waɗannan masu yunƙuri na baya-bayan nan wadansu mutane ne ke amfani da su domin kawo wa cigaban ƙasa cikas,” inji shi.
Alhaji Ado Ɗansudu ya ƙara da cewa, lokaci ya yi da mutanen Arewa ya kamata su daina cin junansu a kafafen yaɗa labarai, maimakon haka su yi amfani da kafafen wajen kare martabar Arewa, “za ka ga kafafan yaɗa labarai na kudu na yin maganganun ɓatanci a kan Arewa da jama’ar ta, amma abin mamaki sai a rasa wanda zai fito daga Arewa ya mayar da martani ko ya ƙaryata hakan, ko kuma ya kare martabar Arewa, sai dai ka ji su ’yan Arewan suna cin junansu a kafafan yaɗa labaranmu na gida.Misali akwai wadansu kafafan yaɗa labarai da suke yawan yaɗa labaran ƙarya wai yaƙin Basasa ya faru ne a tsakanin al’ummar Ibo tsiraru kiristoci da musulmi Hausawa ’yan Arewa, wanda hakan ba daidai ba ne, ƙarya ne ake jingina wa Arewa, domin a lokacin yaƙin Basasar shugaban ƙasan da ya jagoranci yaƙin Janar Yakubu Gawan ba bahaushe ba ne ba kuma musulmi ba ne, haka zalika mafi yawan manyan hafsosin sojin da suka jagoranci yaƙin irin su TY Ɗanjuma da Joe Garba da su Cif Olusegun Obasanjo da su Adekunle Fajuyi da Benjamin Adekunle da Dabid Ehjo dukkansu ba hausawa ba ne ba kuma musulmi ba ne, babban hafsan suji da za mu ce bahaushe ne kuma musulmi a wancan lokacin shi ne marigayi Janar Murtala Muhammad, to ai ka ga wannan yaƙi ne na gwamnatin Najeriya da ’yan tawaye, ba da hausawa musulmi da ƙabilar Ibo kiristoci ba, kamar yadda wadansu kafafen yaɗa labarai na kudu ke yayatawa ba, wannan shi ne ya sa lokacin da sojin Najeriya suka shiga Kudu maso gabashin ƙasar nan a baya-bayan nan domin yin aikinsu, sai wadansu ɓata-garin wannan yankin suka far wa ’yan Arewa suna kisansu, suna ƙone masu wuraren ibadar su, don haka akwai bukatar wayar wa jama’a kai a kan wannan,” inji shi.
Ya ce shugabannin Kudu Maso Gabas sun gaza jan kunnen matasansu masu ta da ƙayar baya ne domin tsoron kada wani abu ya same su, amma bayan da gwamnati ta dauki kwararan matakai gwamnoninsu sun fito sun barranta da su. “batan dabon da shi Nmadi Kanu Jagoran kungiyar IPOB ɗin ya yi ya tabbatar da cewa shi matsoraci ne kuma ƙaramin tsagera ne, daman abin da ya shirya yi ke nan, iyalansa na ƙasar waje idan ya tada ƙura ya tsere ya gudu kamar ya bar ’yayan talakawa da ba su san me suke ba ana kashe su, ai wannan gudu da ya yi ya ɓuya maimaita abin da jagoran Biyafarar na farko ya yi ne,” inji shi.
A ƙarshe, Alhaji Ado Ɗansudu ya yaba ƙwararan matakan tsaron da gwamnatin shugaba Buhari ta ɗauka, kana ya yaba wa al’ummar Arewa saboda yadda suka kai zuciya nesa.