Biyan haraji: Shugaban Yankin Raya Kasa ya ziyarci kasuwannin Ojo da Sasa

Sabon Shugaban Yankin Raya Kasa na Akinyele ta Kudu a Jihar Oyo, Alhaji Kazeem Adekunle Kagara ya yi kira ga ’yan Kasuwar Sasa da dukkan masu shaguna da gidaje a bakin babban titin Ojo Tudun Sunnah a Ibadan su rika biyan harajin wuraren da suke zaune cikin lokaci domin da irin wannan kudi ne gwamnati […]

Biyan haraji: Shugaban Yankin Raya Kasa ya ziyarci kasuwannin Ojo da Sasa

Sabon Shugaban Yankin Raya Kasa na Akinyele ta Kudu a Jihar Oyo, Alhaji Kazeem Adekunle Kagara ya yi kira ga ’yan Kasuwar Sasa da dukkan masu shaguna da gidaje a bakin babban titin Ojo Tudun Sunnah a Ibadan su rika biyan harajin wuraren da suke zaune cikin lokaci domin da irin wannan kudi ne gwamnati ke samar da abubuwan ci gaban al’umma.

Alhaji Kazeem ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a da ta gabata lokacin da ya jagoranci manyan jami’an yankin zuwa ziyarar aiki a kasuwannin Sasa da Ojo, inda ya ji dadin ganin ’yan Arewa ne mafi yawan ’yan kasuwar da suke gwamutse da Yarbawa da sauran kabilu suna gudanar da harkokinsu a wadannan wurare ba tare da takurawa daga bangaren mahukumta ba.

Ya ce, gwamnati ba za ta kori kowa daga wurin da yake a matsayin gida ko shago da rumfar saye da sayarwa ba. “Amma idan kuna bukatar gwamnati ta rika samar da abubuwan ci gaba a wuraren da kuke zaune to wajibi ne ku bayar da hadin kai da goyon bayan sabon shirin raya karkara da Gwamna Seyi Makinde ya bullo da shi a kananan hukumomi 33 da hukumomin raya kasa (LCDA) 35 da ake da su a fadin Jihar Oyo.

“Wani muhimmin abin da gwamnati ke bukata daga gare ku shi ne a kowane lokaci ku kasance masu girmama doka da oda domin zama lafiya da kwanciyar hankali. Kuma Gwamna Makinde ya ce mu shaida muku cewa babu ruwansa da  batun kabilanci da bangaranci ko bambancin addini, amma duk mutumin da ya tayar da hankalin jama’a to, shi ma ya san makomarsa,” inji shi.

Alhaji Kazeem Adekunle Kagara wanda ya yi wa jama’a jawabi cikin harshen Hausa ya shaida musu cewa ya gudanar da gaba dayan rayuwarsa ce a garin Kagara a Jihar Neja wanda hakan ne ya sa shi fahimtar al’adun kabilun Arewa da irin zamantakewarsu da sauran jama’a.

Tun farko a jawabin maraba da Sarkin Hausawan Ojo Tudun Sunnah Alhaji Ali Yaro ya yi, ya ce, “Yau fiye da shekara 40 ke nan da muke zaune a wannan wuri ba mu taba samun wata matsala a tsakaninmu da mahukunta a baya ba. Saboda haka matsalar biyan harajin shaguna da gidaje ba za su zama matsala a tsakaninmu da wannan gwamnati ba.”

Hakimai da manyan malaman addinin Musulunci da ’yan kasuwa da masu sana’o’in kanikanci da ’yan acaaba da sauran jama’a ne suka saurari bayanin da shugaban ya yi.